Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

Zainaba Yar Gata Book 1 Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya sako aka kwana Ana ruwa, Washe gari DA safe, *"KABIRU"* ya Dan wanke kayan da zaije zance da yam ma, Yatafi gun aikin sa, Misalin k'arfe uku na yammad yadawo gida yaci ado ya fesa Dan turaren Sa, be tsaya ko inaba sai k'ofar gidan su *ZAINABA"*, yana zuwa ya tarar da ita ta na hira ya zauna gefe d'aya akan keken sa, bayan sungama hira ta k'ariso gunda yake ta ce Baku hadu DA abokin naka bane har yau yace A hakane, ta kalleshi tayi murmushi, Ta Ciro wayar ta ta k'irawo number kawai waya ta Fara ringin, A aljihun sa ya cirota ta kalleshi ta ce Ina amfanin k'arya da girmanka Samarin yanzu yawancin Ku bakuda ga ski ya, *"KABIRU"* Be ce Mata komai Ba ta juya tayi tafiyar ta ta bar shi A tsaye. Yayi zugum..! Tafara tafiya ta juyo tayi murmushi ta ce Yaya na Idan har Dagake kake miye Amfanin k'arya?. "KABIRU, yayi Zugum Tayi Shigewar ta cikin Gida tabarshi Waje Cikin Tinani, Haye keken Sa yayi yayi Tafiyar sa Shiru_Shiru, tsahon Sati *"ZAINABA, bataga Mutumin ta Ba, Ita Dakanta Ta k'irashi Awaya tayi (Ringin), Har sau uku Bed'aga Ba tayi murmushi "Kabiru Ya na zuwa ya tarar da, K'ira har Sau uku. "Bin k'iran yayi dayaga zainaba ce yaudakan ta take k'iran shi, K'irjin Sa na bugawa duf_duf, Ta na amsa k'iran Ta ce Dan nafada maka gaskiya shine kake fushi Dani, Saura k'iris kayi nasara Amma naga kamar Bada gaske Kazo yauda yamma idan Har da gaske kake, 'Yar gata tana Nam tana jiranka ta kashe wayar ta. Yammana yi Awannam ranar *"KABIRU"*, zazzabi Mai tsanani ya kamashi Am ma saboda tsananin son da Yakewa 'Yar gata Haka ya ta shi ya yunk'ura zai tafi yahau keken sa, Am ma Sam yagagara tukawa. Tajira_Tajira harta gaji Bataganshiba Shiru tayi tace Lafiya kuwa banga Mutuminnam ba, balafiya ba dai kam Kwanciya *"Kabiru, yayi yana famar murk'ususu Zazzabi ya galabaitar dashi k'irar wayar tayi Shibesan ma ana k'iraba saboda zafin zazzabi Mahaifiyar sa ce, ta d'aga suka gaisa take tambayar ta shin me Qatar bay a Ku sane, murmushi tayi tace Ai gashinam yana kwance ba lafiya, Ta ke Zainaba ta ce subahanallahi Kihada ni dashi Girgiza kai tayi ta ce, Yata Baya hayyacin sa Kibari zuwa anjima ki k'ira kinji zainaba tace To Mama takashe wayar karfe 7:17 dai_dai na dare k'irar wayar tayi har Sau uku Ba'a dauka ba washe gari dasafe tasake k'ira *kabiru Yanafarkawa ya daga wayar yayi Sallama suka gaisa Yayi mamaki Dayaji zainaba tace masa yaya jiki. Sunacikin tadin su tace Insha allah zanzo na dubaka koda yamma, kabiru yace A'a nama warke basai kinzoba murmushi tayi tace Bakaso naga gidan naku ne, kabiru yace A'a bahaka bane Nima zanzo Anjima karkidamu Murmushi tayi Tace Kaida bakada lafiya Kabari jikin ka yawar_ware kaji. Sati d'aya yayi Amma jiki yaki ci yak'i cinyewa Dalilin haka yasa zainaba ta taho har *WURO HAUSA", Aunguwar su tana zuwa Sukagaisa da mahaifiyar sa Ta je tadauko likita har gida yabashi magani yamasa wasu Allurai Bewuce kwana ukuba jikin sa ya warware kamar Bashiba Yayi kwalliya ya kama hanya sai Unguwar su zainaba. Yanazuwa ya tarar da ita Zaune Ak'ofar gida tana hiradawani tanaganin Sa, Tataso tazo wajen sa Wanda suke hirara ransa yayi matuk'ar naci Abusace Yataho ya ce Haba Zainaba Wannam talakan kike saurara mai zai tsinana miki dubeshima wari yake, murmushi yayi yace A'a bekama kafadi hakaba danasam zakazo nidana bari sai gobe, Cikin fushi yace Kai Aibaka isa mu hada budurwa tare Dakai ba talakan Banza Kaduba Akeke kake zuwa wanda kudin keken ko zoben hanuna bazai sayaba. Shiruyayi *"Kabiru yace Da ace kafahaimceni daduk hakan bazata faruba, sannam Alziki da Wannam kuma nima Allah zai bani Saboda haka Kadaina cimun fuska Yanda kakeji da zainaba taka ce to nima tawace Kuma tawace nikadai Juyawa yayi yashiga motar sa ya fizgeta yayi tafiyar sa. Kallon shi zainaba tayi Tace nibataka bace, Banason mutum mai son Tada husuma tatashi tayi tafiyar ta tindaga wannam lokacin koda yak'irata Awaya bama ta d'agawa Daga k'arshe Da abun ya dameshi cire sim card dinnashi yayi ya Aje shi na tsahon sati kuku ko sakashi ba'a yi Awaya....! Washe Gari Yayi wanka, ya tattaro 'yan kayayyakin shi masu tsafta yataho ya durk'usa yagaida Mahaifiyar sa yace Mama Tafiyar nam tatashi Zanjeni Wajen *"BAFFANA*, murmushi tayi tace Aibazan hanakaba Kabiru Amma zakasha tafiya shiga d'aki tayi ta dauko ragowar 'yan kudaden ta dabazasu wuce naira dubu d'aya ba ta mika masa ya maida mata da kanyata ya ce, haba Mama na Kibar kudaden ki Idan naje chan zanna yiyo miki Aike tafashe dakuka ya rarrashe ta sukayi bankwana. Tafiyar Awa Shida sukayi Kafin Isar Su *Garin kebbe*, Yana isa suna sauka atashar mota Ya daga wayar Baffan sa Daniyyar zai k'irashi jiyayi An wanke shi da kwatami Besan lokacin daya katse wayar ba Motar data watsa masa Ruwan kwata, Tana fakawa Yataho Ya tsaya daga gefe Wata zankadidiyar budurwa ce tafito daga motar Fiskar ta sanye da Tabarau,(Gilashi) Magana yamata yace Ke Bakida tarbiyya ne kinwatsa wa mutum Ruwan kwatami amma bakisan kibashi hak'uri ba ko?. Juyowa tayi taimasa wani irin kallo Nagadara Tace Ayya..! To kayi hak'uri kaji Bude jaka tayi Taciro 10k ta zo tace Gashi kaje Ka sauya wasu kayan, besan lokacin daya ja Hanun ta ya wanka mata mari tasssss...! Ba gabakidaya Kowa dayake wajen saida ya zaro Ido rik'e kumatun ta tayi idon ta na hawaye tace Mari Na kayi Ko To yau zanga waye Gatanka A kaf Cikin Garin (KEBBI), murmushi yayi yace mezaki iya daga wayar ta tayi Cikin shagwaba Tace Dady kana Ina Yace Lafiya kam Fashewa tayi Dakuka Tace Inason Mota d'aya na yan sanda wani ne ya marini Haka kawai. Wasa gaske Kabiru Jiyayi Hukuma sun nadeshi basutsaya dashi ko ina ba sai ofishin 'yan sanda Kabiru Yana zaune bece komai ba tamaida stetment, Tafadi k'arya da gaskiya. Wani Contabul ne yataho ya kalli kabiru yace Kai dan saurayi meyakaika Marin Wannam yarinyar Gaskiya na tausaya maka Gashi har Cinhanci dabayar maitsoka wai A ajemata kai har zuwa lokacin da ka shirya bata hak'uri Kadurk'usa har k'asa murmushi yasakeyi yace nibak'one Kubani wayata Zan k'irawo baffana ya zo yayi belina Anam fa sukace ina ai bazancen beli hakadai kabiru yacigaba dazama A cikin magar k'ama harna tsahon Kwana hudu. Rannabiyar ne, babban D.P.O daya ziyar ci Ofishin ya tarar da Kabiru, yasa akafito dashi Ya tambayeshi Shin wajen waye kazo garin kebbe Sannam kana bak'o maiyakai ka rigima. Kabiru ya zayyana masa Abunda ya faru, dayaji Haka yabashi Hak'uri akadauko wayar sa Aka bashi, Acikin chaji ofishin 'yan sanda ya k'irawo Baffan sa wato *"ALHAJI BADAMASI*, yana isowa ta ke D.P.O yatashi suka gaisa yace wa Alhaji badamasi wannam d'in dankane Yace A danane Dan yata ce, Nayi nayi Yadawo wajena tare da mahaifiyar sa amma sai Kwanaki yak'irani yace yana zuwa ya kalli kabiru yace tashi muje Kaji Kabiru tashi Yayi suna tafiya yanata sak'e sake ina zaosamu budurwar nam Ya rama abunda ta masa, Tafiya suke Amota Amma komagana bayayi Suna shigowa Cikin Gida wata k'aramar yarinya ya hango tanaganin sa tataho dagudu

Table of Contents

Chapters

16 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});