Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 15

Chapter 15

Zainaba Yar Gata Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Nawaye wa, Matashin nam ne Yazo dakanshi Ya samu k'abiru cikin ma gar k'ama yace gobema ka sake Yiwa wani Rashin kunya nawa ma kake dashi da harzakayi Sa Insa dani Akan Wannam Kuchakar yarinyar Shiru kabiru yayi bai ko tanka mishiba Abun ya k'ara cimai rai sosai Budar bakin Gayen Yak'ira wani police yace Kasashi ya bani Hakuri Idan kuma har ya k'i bani to A cika musu An kamasu Ne Suna lalata. Dajin wannam Kalaman Nashi, Kabiru yace Wai kai wana irin Mutum ne Kam Bakada imanine Ko shin bakasan Darajar Mace Bane So kake Ka bata mana suna Idan kayi Hakan ribar me zaka samu?. Kafin Yagama Rufe Bakin shi, Yasmin ta ce, A'a yaya kabiru Kabashi Hak'uri Nine mai laifi Yayi shiru Ta ce Kayi Hak'uri Nasan ka da hak'uri Budar bakin Kabiru Yace Kayi Hak'uri Ya fada har sau uku Ranshi Abace Saurayinnam Yace Naji Taba jikina fa dakayi Kananufin Kadaki Banza kenam?. Kabiru Yace A'a ba haka bane kayi Hak'uri shiru yayi yai dariya yace Shikenam Amma Koda gabane Kada kasa ke yunk'urin ja da wanda yafika kudi Wahala zakasha. Bawa kabiru wayar sa akayi, Ya k'ira baffanshi cikin gaggawa yazo saida sukayi ta naira dubu hamsin kudin beli, Matashin nam yana gefe yanata famar dariya da aka karanto abunda ya faru Ran mahaifin yasmin yabaci, Yace Bazai yi hak'uriba a tafi kotu kawai Anam ne Yasmin ta durk'usa ta ce A'a baba Muhak'ura kawai Kabiruma yace Su hak'ura Amma mahaifin Su sam yak'i Yadda Haka Akayita shari'a Harna tsahon Sati biyu Kullum Basa cin Nasara Daga k'arshe suka hak'ura, Cinzon dasauro ya musu saida sukayi Gajeruwar Jinya. Bayan Kabiru yasamu sauk'i Ya k'ira number zainaba yaji A kashe, Ya k'ira number Mahaifin ta yana dagawa suka gaisa yace Kabiru kenam Kabani Mama ki amma ba komai Da nayi niyyar niyyar mallakamaka Zainaba Amma najika Shiru Yanzuhaka Na riga na bada I ta Kawai ya katse wayar shi. To masu sauraro, Muhadu A fejin gaba dan jin yadda zata kasance?. ♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥ *ZAINABA Y'AR GATA* ♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥ *(RICH AND POOR..)* _________________________________ ® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_ _________________________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/ BY *KAMAL NO LOVE (DAN GOMBAWA)* *BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM* *36=40* 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 Bayan “Kabiru yasamu sauk'i Ya k'ira number zainaba yaji A kashe, Ya k'ira number Mahaifin ta yana dagawa suka gaisa yace Kabiru kenam Kabani Mama ki amma ba komai Da nayi niyyar niyyar mallakamaka Zainaba Amma najika Shiru Yanzuhaka Na riga na bada I ta Kawai ya katse wayar shi". “Shiru kabiru yayi wasu zafafan hawaye ne suke gangarowa daga idanun sa, yace Zainaba ina matuk'ar sonki Amma mahaifinki yagaza fahimta na gashi zaibaki wanda ba kya so Yacigaba ta hawaye awannam lokacin ne Nafahimci Girma so Jiyayi “Yasmin, Tana kwan-kwasa mashi K'ofa maza-maza yashare hawayen Fuskar shi dan karta gane, shigowarta kedawuya kenam tace lafiya naga jikin ka yayi sanyi kodai jikinne haryanzu?. Gyad'a kai yayi Yace A'a kallonsshi tayi Taga hawaye na biyo kumatunshi zama gefen sa tayi tace Maiya faru yaya kabiru?. Na ke Ganin Yau kaine da kuka gaskiya babban Abune Tayi Tayi Amma yak'ifada mata komai Tashi tayi Tafita jim kadan Saiga “Mahaifiyar shi tare da mahaifiyar Yasmin, zama sukayi Gafen shi mahaifiyar salma Antinshi kenam Ta ce Kabiru Maiyake damun ka ne Mukam bekamata ka Boye mana Ba Shiru kabiru yayi nad'an wasu mintoci Yaja Dogon numfashi yayi murmushi Ya kalli yasmin yace wata sharri ma zakimin ko?. Maidawa yayi kamar Babu Abunda ya faru, Murmushi “Yasmin tayi Tace Yaya kabiru Naji duk abunda kakyi ta zayyanah musu abunda yafaru shiru sukayi Nadan wasu Lokuta mahaifiyar sa Ta kalleshi tace kabiru nasan ka da juriya Lallai “mahaifin Zainaba yagaza fahimtar ta ta ce yace yabada Ita yanzu babu yanda zamuyi saidai hak'uri kawai. Dajin wannam Batun Yasmin Cikin zuciyarta tace Alhamdulillah Burina yacika Ta kalleshi Ta ce Babu Inda zaka Munanam Tare Insha Allah nice matar Ka tace Ya Allah kacika Min burina Amin Acikin zuciyar ta. Kallon Antinshi yayi yace Yanzu sai hukuncin da Abba yace washe gari suka zauna da Abban shi Yace, Kabiru Dole Hak'uri zakayi Kanemi Wata Amma Abun babu dad'i Karbar number Mahaifin zainaba Yayi Ya k'irashi suka Gaisa Yace Wanene?. Shiko yace Neman Alfar ma Nakewa Dana Kabiru Dajin Haka Yayi Shiru Baice Komai Ba Can Yace Bawai Dagani Bane Daga zainaba Ne Yanzuhaka Gobe Za'a Daura Mata Aure Kuyi Hak'uri Baffan kabiru yayi Shiru Yace Ba Komai Yakashe wayar Yace Kabiru Kayi Hak'uri Gobe Za'a Daura Mata Aure Shiru Yayi Yace Shikenam. Washe Gari Akadaura Auren Zainaba Da Wani Mata shi Dan Masu kud'i. “Kabiru, ne Zaune ya had'e fuska yayi shiru Kanshi na k'asa “Yasmeen, Tazo wuce wa ta kalleshi taga yanayin Dayake ciki Acikin zuciyar ta Ta ce, Allah Sarki Na tausaya maka bros Kabiru Tahowa, Tayi Ta zauna Gefen shi Ta ce Yaya Kabiru Kayi Hak'uri Juyowa yayi ya kalleta yayi Murmushi yace Ninasam Har Gobe “Zainaba Tana sona Zatayi Auren Nam ne Bisaga Gudun Bacin Ran Mahaifin Ta Amma duk Da haka Ina mai mata Fatan Zaman Lafiya Mai Dorewa. Dajin Wa 'yan nam Kalamun Nashi Yasmeen Yayi Murmushi, A cikin zuciyar Ta Tace Wannam Fa yasaduda, Tayi Shiru Haka dai sukayi Hira Sama-Sama. Bayan Wata Uku da Auren, “Zainaba Watarana Kabiru Sunfita Tare Da Yasmin Yakaita Wajen Walimar Daurin Auren Wata k'awar ta, Bayan ya Ajiyeta ya juya da mota zai fita Wata mata Yagani Ta rufe fuskar ta Da nik'abi, tasha Gaban Motar Sa Kauce mata yayi Amma ta sake Tare Hanya. Dakatawa yayi ya kashe motar yafito, Yace “Baiwar Allah Lafiya kuwa kike k'ok'arin Tare ni duk kuace-kaucen da nake k'ok'arin miki?. Bude fuskarta tayi, Suka had'a idanu Ta ce Kabiru Meyasa Zakamin Haka ta fashe Da kuka!!. Gabas da yamma yaduba ruk'e kai yayi Yace A'a bawai daga nibane kifahim ce ni, Share hawayen ta Tayi Ta ce Mahaifina Ya baka dama Ina murna Haka mukaji shiru Nayi koko kamar raina zai fita, Daga k'arshe Mahaifina ya yanke shawara yabayar da ni. Kabiru Kallon ta yayi Yace Daga mahaifin kine nayi k'ok'arin fahimtar dashi Amma yak'i sauraro na, Nayi-nayi Amma daga k'arshe Haka inaji Inagani Ya baki wanda ba kya so. Kallonsa tayi Tai murmushi wasu zafafan gawaye ne suke kwarayonwa daga idanunta, Juyawar Da kabiru zaiyi Kawai ya hango “Yasmin, Ta taho Afusace Da Leda A hanunta lemon k'walbar da yake d'aya hanun nata ta watso amma kabiru Ya tare Ta bata mishi Jamfar sa, ya kai hanu zai mare ta sai ya fasa yace. “Haba yasmin, Baikamata Kimata Haka ba Karki manta Fa matar Aure ce Ba kya tinanin Mijin ta bazai Bar muba, Shiru ta yi Ta ce To munafuka bayan Ki k'ishi kuma name zaki zo kina kulashi?. “Murmushi Zainaba tayi Ta ce Dakata K'awata Ba laifinshi bane Laifinane kallon Kabiru Tayi Ta ce Wannam k'ishinta yayi yawa k'antar da hankalinki Kabiru nakine A yanzu kam Amma ada chan baya Nawane Kinyi Sa'ar miji Maida nik'abin ta tayi Ta juya zata tafi Tasake juyowa ta kalli kabiru taci kuka fuskarta a rufe Ta juya ta shiga cikin 'yan walima. *lokaci d'aya zainaba* ta juyawa mijin ta baya tadinga gallaza masa

Table of Contents

Chapters

16 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});