Chapter 9
Chapter 9
damu baki daya. Cike da tsantsar farin ciki ta ce." Na gode sosai Baba insha Allahu za muyi farin ciki gabadayan mu, amma ki shirya an jima kadan yana tafe zai zo ku gaisa kafin ya tafi Abuja gurin sana'arsa. Ta na kokarin fita daga dakin ta ce." Shikkenan Allah ya kawo shi lafiya. Zama tayi kan kujera 'yar tsuguno jikinta duk a mace! Saliha ta ce." Baba Lafiya dai?" A sanyaye ta ce." Lafiya lou Saliha al'amarin Shahida da wannan mutumin ne yake ban tsoro. Ta ce." Tuntuni na ce miki ki daina damuwa amma kina kokarin janyowa kanki matsala! duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka." Ta ce." Na yi fatan alheri ai Allah ya ba su zaman lafiya." Shuru tayi ba ta amsa da ameen ba, kawai ta cigaba da feraye kabewar dake gabanta. ** To kamar yanda Talatu ta kudire a ranta cewa za ta je tayi tambaya a kan lamarin, da asubah zakara ya bata sa'a ta fita can wani 'karamin k'auye ta nufa gurin wani malami, wanda ya duba mata al'amarin ya kuma tabbatar mata da cewa shi bai ga komai ba face alheri domin kuwa babu da na sani ko bak'in ciki a cikin al'amarin, sai farin ciki. Jikinta a sa'bule ta dawo gida da tunanin yanda za tayi ta wargatsa auran. *** Cikin nutsuwa ta fito ta same shi a tsaye a soran gidan, sosai tayi farin cikin ganinsa tsaf dashi cikin shadda bulu mai duhu tazarce har k'asa da hula da takalmi ya dora rigar sanyi a sama saboda yanayin garin sanyi ya fara busawa, ta tsuguna har kasa tana gaishe shi, ya amsa a nutse yana mata wani irin kallo wanda ya sa ta jin kunyarsa ta kasa tashi tsaye. Ya ce." Kin yi min kyau fiye da tunaninki. Murmushi tayi ta ce." Ni ma haka idan na gan ka cikin suttura cike da kamala sai na yi ta mamaki kamar ba kai ba, wanda da yawa mutane suke maka kallon mahaukaci! lallai babu shakka wannan ubangida naka dole a jinjina masa domin ya taka muhimiyyar rawa a rayuwarka, ya sanya ni cikin farin ciki mara mislatuwa domin ni yayi wa tagomashi yayi wa bajinta ba zan gushe ba face na cigaba dayi masa addu'a har karshen rayuwata." Ya dinga jin wani irin farin ciki na kwarara a zuciyarsa, ya ce." Za ki gaisa da maigidana insha Allahu sai kiyi masa godiyar alherin da yayi miki, duk da cewa yana da labarinki amma lokaci kad'an ya rage ku gaisa da juna da ikon Allah." Ta mi'ke tsaye tana gyara mayafinta da ya sauka a kafadarta ta ce." Ina fatan zuwan wannan rana. Kawu Musa ne ya shigo da shirin zuwa kasuwa a tare dashi. Ya tsaya suna gaisawa babu yabo babu fallasa yake kallon mutumin, shima mamakin sauyawarsa yake, kamar bashi ne wannan mahaukacin ba mai yagaggun kaya da kwanciya cikin 'kazanta. Ya ce." Ai babu damuwa mu je ciki sai ku gaisa sosai tsayuwa a soron bashi da amfani." Cike da jin dadi ya ce." Na gode sosai Kawu." Ita kuwa Shahida babu wanda ya kai ta jin dadin ganin yanda Kawu Musa ya saki fuskarsa su gaisa da Masoyinta cikin farin ciki. Babu yabo babu fallasa ta shimfida masa tabarma ya cire takalminsa ya zauna a nutse ya ke gaisata, ta amsa babu walwala a tare da ita domin dai har yanzu zuciyarta ba tayi na'am dashi ba kawai dai ta hakura ne saboda samun farin cikin yarinyar. Ita kuwa Saliha a fakaice take kallonsa tana k'unshe dariya, hular kansa da takalminsa soso da ya cire a gefanta su takewa dariya. wanda duk abinda take yana kallonta kuma yana mamakinta a zuciyarsa. Kawu Musa shi yake masa tambayoyi, cikin nutsuwa yake bashi amsa daidai da tambayar da yayi masa. Kawu Musa ya ce." To Allah ya tabbatar da alheri a cikin al'amarin. tunda ka riga kayi magana da mahaifin yarinyar ai shikkenan, dama shike iko da 'yarsa, tunda ya baka mu kuma za mu zama masu addua da fatan alheri, amma mun baka amana ka rike ta da kyau, marainiya ce bayan haka kuma ka duba lalurarta. Ya ce." Nayi alkawarin haka insha Allahu. Baba Asabe ta ce." Da zai yiwu sai ka kama haya a cikin unguwa ka ajiye ta a kusa, idan yaso ka dinga zuwa daga can abujan. Ya ce" Hakan ba zai yiwu ba Baba, ni dai buri na ku yarda dani, ku amince cewa zan rik'e amanarku, ni kuma nayi alkawari insha Allahu idan ban rik'e ba Allah ya hukunta ni". Ta ce." To ai shikkenan Allah ya sa mu dace amin." Gabadaya suka amsa da "Ameen ameen." Da zai tafi ya ajiye mata dari biyar, ta ce."A'a zo ka dauki kudinka bawan Allah ka 'kara guziri, kai da za kayi tafiya" Yayi sauri yasa takalmansa ya kama hanyar fita Shahidan ta bi bayansa da sauri. 'Yar 'karamar waya tacno ya bata ya ce ta ri'ke zai dinga turo mata sak'on gaisuwa, saboda ya san lalurarta, ta kar'ba ta na godiya sai murmushi take ganin yanda aka samu daidaito ta kowane b'angare! a yanzu burinta bai wuce ace sun mallaki juna ba. **** "Eh ni ne Alhaji Sammani mai leshi kasuwar wambai.'' Ya fad'a yana gyara wayar a kunnansa. Daga daya 'bangar ya ce." Ma sha Allah. dama na kira ne akan maganarka da Abokinka Jamilu Hujaj." Ya ce." Eh hakane to ina sauraranka, Allah yasa alheri ne. Murmushi yayi a nutse ya ce." Alheri ne insha Allahu." Yayi shuru na second daya kafin ya ce." Nawa ne sauran kud'in naka ne?" Cike da karsashi da kwarin gwiwa ya ce." Ba saura bane ai domin a miliyan biyu da rabi an bada miliyan daya ka ga kuwa ya wuce saura." Ya ce." 'Kwarai kuwa, yanzu idan na fahimta cewa kudinka da suka rage a hannun abokinka Miliyan daya da rabi kenan?" Ya ce." 'Kwarai kuwa." ya fada yana gyara tsayuwarsa a cikin shagon. Ya ce" Babu matsala ka tura min account number zan sa maka insha Allahu." Mamaki ya rufe shi! ya bud'e baki kenan zai yi magana sai ya ji wayar ta tsinke! ya dinga kallon fuskarsa wayar yana mamakin in da Alhaji Jamilu ya samu wannan hanyar, shin waye wannan mutumin? amma bari ya tura account din ya gani, domin bai gama amincewa da maganar mutumin ba, ya na so ya tabbatar ne kawai. Ko minti biyar bai yi da tura account d'in ba ya ji alert kudi sun shigo, yana dubawa ya ga kud'insa cif miliyan biyu da rabi! Cikin tsantsar mamaki! ya nemi guri ya zauna jikinsa sai kyarma yake dama Jamilu ya sha sheda masa cewa shi ba 'karamin mutum bane. Text ne ya shigo wayarsa ya bude yana dubawa. Sai jikinsa ya 'kara mutuwa karanta abinda yake k'unshe. _"Ga kud'inka nan Alhaji, ka mayar masa da miliyan dayan da ya baka Allah ya kiyaye faruwar hakan anan gaba."_ Hannu na rawa ya fara kokarin kiran wayar sai dai sai kash a kashe take, ya kira ya kai sau bakwai bata shiga ba, sai ya hakura ya fara laluben lambar abokin nasa domin fada masa halin da ake ciki. " Na san da hakan, domin
Table of Contents