Chapter 6
Chapter 6
hanyar warware matsalarta. **** "Baba yau fa zai zo da daddare ku gaisa sannan kuma mu je da shi can gidanmu su gaisa da Babanmu domin gobe yake so ya koma gurin aikinsa." Ta ce." Waye zai zo?" domin ita har ga Allah ta manta da maganar da sukayi da safe. Ta d'an 'bata fuska da fadin." Har kin manta ko?" Girgiza kanta tayi ta ce." Ke shahida magana mai muhimmanci ita nake ajiyewa a cikin raina domin abubuwan da suka dame ni suna da yawa." Ta 'karasa maganar tana kokarin kwance lalitar dake d'aure a k'ugunta. Sunkuyar da kanta tayi idonta yayi ja! alamun ranta ya 'baci! Ita kuwa Saliha dariya kawai take mata tana 'yan 'kananun maganganu wanda ta san ba za ta ji ba. Wutar nepa a ka kawo Saliha da sauri ta kunna musu fanka domin zafi ake a garin. Ita kuma Shahida ta je ta dauko hijaban ta domin ta goge. Ta kalle ta da fadin." Kin san dutsen gugar nan yana da jan wuta Shahida da ki bari na gama kallon labarai idan an gama sai kiyi gugar ki." Ta ce."Baba idan su ka dauke wutar fa.''? Ta ce." A'a ba zasu dauke ba insha Allahu, ke Saliha kunna min talabijin din NTA KANO zaki kai." Ta ce." To." da sauri ta janyo 'yar yawo (cover socket) ta jona kayan kallon tana kokarin gyara Area domin hoton ya fito. Shahida d'aki ta shiga ta kwanta ta shiga tunanin masoyinta. An gama labaran, 'karshen kawai suka riska. A in da mai gabatarwa yake fad'in kanun labaran 'karshe, cewa wannan Attajirin d'an kasuwar Alhaji Saddiku wanda aka fi sani da *'Dan gaske* zai yi rabon shinkafa a babban company sa dake sharad'a, za a fara rabon abincin da karfe hudu har zuwa karfe goma na dare. Baba Asabe ta ce." Wannan karon ma sai na je ko Allah zai sa na da ce." Saliha ta ce." Da rabon kiyi asarar kudin motarki, har kin manta 'bakar wuyar da ki kasha a wancan lokacin" Ta ce." Wuya ai mai shigewa ce 'yar nan a wannan zamanin shinkafa 'yar gwamanti babban buhu ai ko kwana zanyi a gurin ba zan damu ba mutukar zan samu, saboda haka yanzu ma zan tashi na shirya sai ki kula da masu shige da fice. Girgiza kanta tayi a zuciyarta ta ce." Wanda ya 'ki sharar massalaci ai yayi ta kasuwa! samun shinkafar nan ai sai mai tsananin rabo. "Baba ina za ki je kuma?" ta fada tana kokarin tashi zaune. Tana gyara hijab din dake wuyanta ta ce." Unguwa zani amma ba zan dade ba insha Allah." Ta ce." To don Allah kiyi sauri ki dawo kada kuma ya zo ba kya nan." "To." kawai ta ce ta kama hanya ta fita da sauri tana mamakin wautar yarinyar. **** Gurun cike yake da mata da maza dattijai da matasa matan aure kai harda 'yan mata, dama irin wannan na faruwa mutane babu uzuri sai su tarkato 'ya'ya da jikoki a zo a bi layi kowa kansa ya sani idan kai ka samu ba zaka bari d'an uwanka ya samu ba, wannan shine abinda yake cutar damu wato son kai. Gurin yayi cikar kwari! hayaniya ce kawai take tashi wasu ma fad'a suke yi akan bin layi mussaman mata wasu babu kamun kai! don ma da akwai masu tsaro (securities) da abinda za ayi a gurin sai yafi haka. Duk yana kallon abinda yake faruwa ta cctv camera ya umarci yaransa cewa su je su raba number kowanne ya san matsayinsa lokaci yana cika afara rabo." Abinda ya faru kenan mutum goma ke raba number 'bangaran maza mutum biyar 'bangaran mata mutum biyar. Baba Asabe dai ita ce ta dari hud'u da talatin da shida😂 ta tambayi cewa ita ce ta nawa ? ya fada mata cewa sai an bawa mutum dari hudu da talatin da biyar kana za a zo kanta, amma bata sare ba! ta gyara tsayuwarta a gurin tana adduar Allah yasa tana da rabo. Wasu na fita wasu na shigowa haka ake ta turmutsutsu! a gurin, duk wanda rabo ya zo kansa ana bashi yake jan buhun ya fita daga gurin da yake kan titi ne abun hawa baya wuya. Gefin magriba ya sauko 'kasa yana sanye da farin yadi dinkin tazarce, yadin mai taushi ne wanda kallo d'aya zaka san mai tsada ne, kansa sanye da hulu zannar bukar mai adon bakin zare da ja! kafarsa sanye da bakin takalmin mai gidan yatsa. bai yarda ya fito haka ba sai da ya sakaye idonsa da farin gilashi. Da sauri Sule ya je ya bud'e masa mota! tunda ya ga ya fito ya san fita za su yi. Duk saurin Sule sai da wasu daga cikin mutanan dake gurin suka ganshi. Kafin ki ce kwabo sun yanyame! motar! wani za'kwa'kuri a cikinsu ya 'bude murya sosai dan da alama maro'ki ne ya fara yi masa kirari. "Damuna uwar albarka." Alhaji Saddiku mai dubun nasara! kai ne 'ki gudu sa gudu mazan fama! Allah yayi maka arziki muna amfana dashi! Allah ya 'kara suturtaka *'DAN GASKE!* 'Dan da aka haifa da kyakykyawar Aniya." Da murmushi a fuskarsa yake d'aga musu hannu cikin nuna alamun jin dad'in addu'onin da suke masa! Sule da Labaran suna ta k'ok'arin ganin sun kori mutanan da sukeyi dafifi a jikin motar, da 'kyar suka matsa sannan ya samu ya shiga motar ya zauna amma duk da haka hannu yake daga musu cike da jin dadin adduarsu. Motar tana daf da fita ya hangi dattijuwar matar da ba zai ta'ba mance fuskarta ba. tana tsaye ita ce a kusan 'karshen layi. Baba Asabe ganin yana kallon gurin da suke da sauri ta daga masa hannu tana fadin." Alhaji Allah yayi maka albarka hakika kana aikata alheri muna rokon Allah ya kai mizani, Allah ya yi wa dukiyarka Albarka." Ya amsa da "Ameen ya rabbi." Ya kalli Laraban da fadin." Ka fita ka samu daya daga cikin yaran dake wannan aikin, cewa su ware Dattijawa maza da mata a sallame su duba da raunin da suke da shi." "An gama ranka ya d'ad'e." Da sauri ya fita daga motar ya je ya cika umarni ya dawo ya zauna a mazauninsa, Sule ya ja motar suka fita. Sai da suka hau titi sosai sannan ya ce." Ranka ya dad'e "Gadon 'kaya za mu nufa ne?" Ya ce." A'a Adakawa za mu je." Gabad'aya sukayi shuru babu wanda ya sake magana, sai dai Labaran da Sule cikin tunani suke! a duk lokacin da suka shigo garin KANO maigidan nasu sai ya je unguwar Adakawa kuma baya yarda su shiga dashi cikin unguwar a bakin titi yake sauka ya ce su tafi zai dawo gida da kansa. Wannan abu na nasu mamaki mutu'ka! [12/7, 8:06 PM] Bintu: 45&46 "Wai ana sallama da Shahida." Yaron ya fad'a yana wasa da garegaran dake hannunsa. Saliha dake zaune a tsakar gidan tana kula da masu shige da fice domin sayan abinci ta hararin yaron tana shirin magana sai ga Shahidan ta fito daga daki. Sai tayi shuru tana yi mata wani mugun kallo. Yaron ya ce." Yawwa Shahida ki zo ana kiran ki a waje." Da dan 'karfi yayi maganar. saboda ya
Table of Contents