Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

Majanuni Book 3 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

d'ago kanta ilai kuwa sai ta ritsa shi ya zuba mata ido wanda har ya fara sanja kala, ya 'kan'kance ya kuma yi ja! ta sake shiga rud'ani mara misaltuwa! cikin yanayin maganarta ta ce." Yallabai ko kana bukatar wani abu ne?" Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya nuna mata tarin abincin dake shirye a teburin alama yayi mata wai ta had'a masa abin kari. Cikin rashin kuzari ta fara abinda ya umarce ta, gurin tsiyaya shayi (tea) ya zubo mata a hannu saboda gabad'aya ta kasa nutsuwa sakamakon kallon kurillan da yake mata. Yarfe hannun tayi, tana d'an ya mutse fuska! babu zato babu tsammami ta ji ya kama hannun yana dubawa! da saurin gaske ta k'wace hannunta tana d'an harararsa, gefe guda kuma kafafunta sai rawa suke domin ba 'karamin tsorata tayi da abinda yayi ba. "Sannu.'' a hankali ya furta duk da ya san ba lallai ne ta ji ba. Ba tare da tace masa komai ba, ta juya da sauri ta bar gurin. kallo ya bita dashi yana ayyana abubuwa da yawa a tare da ita. Cikin mutuwar jiki da faduwar gaba ta isa sashenta, ta zube kan kujera tare da dafe goshinta. Sam 'kunar dake hannunta bata dameta ba akan abinda ya faru a tsakaninsu, shin wai mai yake shirin faruwa ne? gabad'aya mutumin bai kwanta mata a rai ba, duba da irin mugun kallon 'kurrila da yake mata, bayan haka kuma menene hujjarsa na ri'ke mata hannu a matsayinsa na babba mai hankali ai ya san hakan ba daidai bane, tunda yafi kowa sanin matsayinta a gidan, matar aure ce kuma matar yaronsa. Gaskiya al'amarin ya sanya ta cikin rud'ani haka ta yini tana tunane-tunane! Wajajen tara na dare text ya shigo wayarta, da yake tana samun chaji a can cikin gidan, tunda gurinta babu wuta haka take zama cikin duhu sai hasken wannan fitilar da ya kawo mata ranar da suka zo gidan. Farin ciki ya cika mata zuciya ganin mijin nata ne ya turo mata sa'kon, cikin rawar hannu ta bud'e domin karantawa! Hawaye ne suke 'kwace mata ganin abinda yake rubuce. _"Ba zan dawo jibi ba, saboda maigidana ya umarce ni na zauna tsayin sati uku na kula masa da wasu harkokinsa ."_ Tana kuka ta rubuta masa amsa kamar haka. _Don Allah ka dawo wallahi ina cikin matsala da kewarka akwai abubuwan da suke shirin faruwa."_ Ya dawo mata da amsa kamar haka. _"Maigida na ya wuce komai a guri na, ba zan iya yin jayayya dashi ba saboda haka kiyi hakuri kawai"_ Kasa bashi amsa tayi sai uban kukan da take shirga! wai shin ita ya za tayi ne? wannan lamari da faru ya fara sanya ta cikin shakku da fargabar zama a gidan. Kwana tayi cikin zullumi da tunani da kuma rashin madafa, amma tasa a ranta cewa Allah shine madogara a gare ta. Washe gari ta shirya tsaf cikin doguwar riga ja mai adon duwatsu tayi kyau sosai sai dai rigar ta d'an matseta daga 'kasa kasancewarta mai cikakken 'kugu, koda ta ga haka sai tayi tunanin cire rigar ta sanja wata sai dai duk kayanta sunyi daud'a wanki suke bukata gashi har yanzu ba ta ga Sulen ba ballanantana ta tambayeshi sabulu. hakanan ta yafa mayafin rigar ta nufi cikin gidan domin gaishe da Hajiya kamar ko da yaushe. Sai dai yau ma shuru babu Hajiyan babu Shukura! cikin zuciyarta take tunanin ina suka tafi, can taji motsi a hanyar kicin ta juya da sauri, sai tayi ido hud'u da Sule ya fito daga kicin din da wani abu a wuyansa, hannunsa rike da babban tire ya shiryo abincin akai. Gaisawa sukayi take tambayarsa masu gidan, nan yake sheda mata cewa sun je biki za suyi kwana uku ko hud'u kafin su dawo." "Eh hakane fa, ta manta shaf ta ji suna maganar biki wanda za suyi a cikin gari. 'Dan tsayawa tayi har ya gama shirya teburin cin abincin, sannan ta kalleshi tare da sheda masa bukatarta. Ya ce." Babu damuwa insha Allah zan kawo miki idan anjima. Tana shirin magana suka hangi sakkowarsa daga sama. yau ma yana cikin kayan bacci masu taushi masu kama dana sanyi domin har da hula. waya ce a kunnansa da alama da wani yake magana. Koda ya sauko kai tsaye gurin cin abincin ya nufa. Sule ya bishi gurin da saurin gaske. Da har tayi niyyar fita sai kuma wata zuciyar ta hana ta domin tana gudun 'bacin ran mijinta tana kuma so ta zauna lafiya dashi, wannan dalilin ne ya sa ta tsaya amma har yanzu tana jin haushin abinda yayi mata jiya. Sule ya risina tare da mi'ka gaisuwarsa, ya amsa hankalinsa na kan wayar dake hannunsa. Sule ya fara 'kokarin zuba masa abinci, sai ya dakatar dashi tare da bashi umarnin tafiya. Ya bi umarni cikin sauri ya kama hanya ya fita. Ta kai minti biyar a tsaye tana dawurwura! kafin ta yanke shawarar zuwa ta gaishe shi. Duk abinda take yana kallonta ta gefen idonsa. A nutse ta tsuguna da fadin." Yallabai ina kwana ka tashi lafiya?" Ya d'an saci kallonta da gefen ido kafin ya amsa a ciki, wanda yake da tabbacin ba lallai ne ta ji ba. Itama ganin bakinsa ya motsa yasa ta mi'ke tsaye zata tafi. Kawai ta ji sunanta rad'au! a bakinsa. Ta ja ta tsaya tana kallonsa gabanta na bugawa. Da hannu ya nuna mata gurin zama. ma'ana ta zauna cikin d'aya daga cikin kujerun dake gurin. Kasa zama tayi, domin tana ganin kamar hakan bai dace ba. Ya bud'e muryarsa yanda za ta ji sosai ya ce." Ki zauna nace ko bana son gardama." Ganin yayi maganar da yanayi na bacin rai! yasa taji wani iri kwata-kwata ba taso ta 'bata masa rai! Ido cike da ruwan hawaye ta ce" Kamar hakan bai dace ba. "Ni na baki umarni." yafad'a yana tsatstsare ta ido! A sanyaye ta ja kujera ta zauna amma ta gagara kallonsa, bayan kwarjinsa sai mugun 'kamshin turaransa da duk ya cika gurin. sai jikinta ya sake mutuwa ta dinga wasa da hannayenta. Muryarsa ya bud'e sosai tare da kiran sunanta. Ta amsa tana d'an kallonsa, kafin ta sunkuyar da kanta kasa tana sauraran abinda zai biyo ba. Ya ce." Ya hannun naki?" "Da sauki." tafada a ta'kaice! Gurin yayi shuru na minti uku. d'ago kanta tayi ta ritsa shi ya 'kura mata ido wannan karon ma idonsa ya sauya kala yayi ja! tare da 'kan'kancewa! sosai ta shiga rud'ani! sam bata 'kaunar wannan kallon da yake mata. Ta tsinkayi maganarsa yana cewa; 'Kin san kina da kyau kuwa ?" Shuru tayi ba ta iya magana ba, sai mugun mamaki! da yake kasheta. Ya sauke ajiyar zuciya mai zafi! kafin ya sake bude muryarsa yanda za ta ji ya ce." Zuba min abinci." A hankali ta fara zuba masa abincin tana Allah wadai da wannan hali nasa. shi kuma sai kallon hannunta yake, wannan dalilin yasa duk ta daburce amma dai yau ba ta zubar da komai ba. Bayan ta had'a masa sai ta kalleshi, as'usul ita d'in dai yake kallo! 'bata fuskarta tayi kafin ta ce." Zan tafi Yallabai. Kai tsaye ya ce." Zauna ki ta ya ni ci." Ta kalleshi da

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});