Chapter 2
Chapter 2
ba. Domin kuwa duk dillalin da yazo ya duba gidan ba ya yi masa 'kima ta mutunci. duba da yanayin unguwar ta gargajiya ce. bayan haka kuma gidan irin ginin taka haye ne irin ginin 'yan kanci! duk fulastar ta zaizaye! ramuka ciki da wajan gidan, sannan kuma duka d'akuna uku ne sai tsakar gida madaidaici da kicin da band'aki. Wannan dalilin yasa gidan bai yi wani daraja ba. wanda yazo daga k'arshe ne ma yayi wa gidan 'kima ta mutunci ya saya miliyan daya da dubu dari biyu, amma duka na bayan sun taya ne a wula'kance! Ganin ba yanda zai yi ne ya sanya ya sallama a hakan, idan ya so sai ya biya bashin miliyan d'aya tare da alkawarin cika sauran a cikin 'yan kwanaki kad'an domin akwai wasu kudi da yake sanya rai a kansu duba da cewa malaminsa ya tabbatar masa da samuwar su. Alhaji Sammani ya nuna rashin amincewar sa akan hakan. A cewarsa ya za ayi yai masa wasa da dukiya duba da cewa shi a dunkule ya bashi, amma zai tsinka masa kud'i a cikin miliyan biyu da rabi an bashi miliyan d'aya mai zai yi da ita a wannan lokacin da yake bukatar kud'in masu kauri da zai yi order amma za a zo masa da wasa! ba tare da 'bata lokaci ya nufi police station. domin shigar da 'kara mutukar akan kudi ne baya saurarawa kowa ciki kuwa har da 'yan uwansa. "Alhaji Sammani ban yi tunanin za kayi min haka ba wallahi, yanzu ni ka kawo police station? na d'auka ai kai mai rufa min asiri ne a kowane hali. Alhaji Sammani me akayi akai miliyan biyu da rabi da har zaka tozarta ni." Murmushi yayi ya ce" Alhaji Jamilu ni kaina ban so hakan ba amma duk kaine ka janyo duba da ganin yanda kake min yawo da hankali alhalin na sheda maka cewa ga bukatar da zanyi da kudin nan. shin wai ko so ka ke ka talautani ne kamar yanda ka talauta kanka." Murmushin takaici yayi ya ce." Kana da damar da zaka fad'i duk abinda kake so, amma ka sani sai kayi nadamar abinda kayi min.'' Ya zakud'a kafad'arsa da nuna alamun bai damu ba ya ce." Kud'i na kawai nake bu'kata a yanzu gani a zaune ga kuma Yalla'bai shi zai zama shaida zan kar'bi miliyan d'aya ba don raina ya so hakan ba sai don samun maslaha a tsakaninmu, sabida haka ka fadi lokacin da zaka cikan kud'i na." Shuru yayi gumi sai karyo masa yake. D.P.O Ya ce." Alhaji Jamilu kai muke saurare." Kansa ya d'ago ido jawur! ya ce." karshen watan nan insha Allah zan biya Alhaji Sammani Kud'insa." D.P.O yayi rubutu cikin wata takarda ya bashi ya sanya hannu. Ya kalle shi da fadin." Wannan shine 'karshen magana Alhaji Jamilu, iyakar adalci anyi maka kada lokaci ya cika ka zo da wata magana, hukuma ba zata saurare ka ba idan baka cika al'kawari ba to zamu d'auki mataki na gaba." Ya ce." Babu damuwa Allah zai rufa asiri." Daga haka bai saurari jin wani abu daga gare su ba ya tashi fuuuuu! ya fita daga ofis din. Duk suka bi shi da kallon mamaki! **** A shirye ya fito ya same ta zaune a falo tana kallo. kafin ma yayi magana ta riga shi da fadin." Ranka ya dade ina son magana da kai." Tunda ya ji haka sai yayi murmushi ya nufe ta ya samu guri ya zauna tare da fuskantar ta. cikin zuciyarsa yake raya cewa maganar dai d'aya ce amma ba zai yi saurin yanke hukunci ba tukkuna. Ta gyara zaman ta da fadin." Hajiya Fatima ta kawo k'arar ka akan Shukura wai ta samo mata aiki amma ka hana shine nake so na ji dalili." 'Bacin ransa ya danne ya ce." Hajiya ki cire kan ki a cikin wannan maganar don Allah. domin ba ni da wannan ra'ayin, babban buri na shine Shukura ta samu miji nayi mata aure amma ni ba zan yarda da wannan tsarin ba." Ta ce." Sabode me? kenan karatun da tayi ya tashi a banza?" Ya ce." Bai tashi a banza ba mutukar za tayi amfani dashi ta hanyar da ta dace. nufi na anan shine ta tarbiyan tar da yaran ta sannan tayi biyayyar aure." Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Hakane kai ma kana da hujja amma ai har yanzu ba ta samu tsayayye ba, mai zai hana ka bar ta domin ta ci gajiyar karatun da tayi." Girgiza kansa yayi, alamun bai amince ba. ya dan kalli agogon dake daure a hannunsa ya ce." Wannan maganar mu bar ta kawai Hajiya kawai ki cigaba dayi mata addua'a." Ta ce." To shikkenan Allah ya za'ba mata miji nagari." Ya amsa da "ameen." Kallonsa tayi lokacin da yake kokarin tashi ta ce." Yanzu kuma ina ka nufa? kwana biyu dai na ga ka zauna a gida ka huta sosai na ji dadin hakan." Ya ce." Kano zan tafi amma iyakaci na kwana biyu zuwa uku zan dawo saboda akwai tafiyar da zanyi zuwa Swaziland insha Allah." Ta ce." To Allah yayi jagora ya tsare ka a duk in da zaka shiga. Sai dai ba zan fasa yi maka maganar aure ba, Alhaji Habu mutukar ka naso ka cika cikakken mutum to dole kayi aure idan ba haka ba to jama'a ba za su daina zargin ka ba." Murmushi yayi ya ce." Na kusa aure Hajiya insha Allahu kiyi min addua." Fuskarta cike da annuri ta ce." Alhamdulillahi haka nake so na ji to ubangiji Allah ya baka tagari.'' Ya amsa da "Ameen ya rabbil-alamina." ******** Tsabar fargaba da tashin hankali ya haddasa masa matsanancin ciwon kai! wanda duk dauriyarsa sai da ya kwanta! hankalin Talatu ya tashi domin ko banza idan ya fita ya samo wani abu yana rage mata wata wahalar! ta shiga nan, ta fita can. yawon cin bashi domin samun abinda za su ci da yara. Ganin saura 'yan kwanaki wa'adin ya cika ya sanya ya yanke shawarar sanar da ita halin da ake ciki ko da taimakon da za tayi akan lamarin. Tashin hankali kenan! maimakon ta tausaya masa halin da yake ciki sai ta shiga surfa masa rashin mutunci da tsiya iri-iri da tozarci! a cewarta shi ya siyi hakan da kud'insa saboda haka ita babu wani taimako da za tayi masa domin shi kadai yake cin kud'insa hakkinta da na yara baya saukewa! saboda haka matsalarsa ce! a halin da ake ciki 'ya'yansa ne kawai suke tausaya masa domin sune suke jinyarsa! Talatu ba ta bi ta kansa harkokin gabanta kawai take. Jamila ce ta yanke shawarar zuwa ta fad'a mata halin da mahaifin nasu yake ciki na rashin lafiya, da kuma irin tashin hankalin da suke ciki. Kasa hakuri tayi hawayen takaici suka k'wace mata! ko shakka ba tayi fargaba da tashin hankali ne suka janyo masa ciwo! me za ayi da wannan hali irin na mahaifinsu, duniya ta sani suma 'ya'yansa sun sheda cewa abinda yake aikatawa haramun ne, anyi anyi dashi ya bari ya'ki! kullum sake tsunduma kansa yake a masifa! yau shine cin bashin wancan. gobe shine cin bashin wannan. kuma kudi ba kad'an ba! to yanzu dai yayi kankat!
Table of Contents