Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Majanuni Book 3 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gidan da yake tutiya dashi ya sarayar dashi kuma bukatarsa ba ta biya ba, dama karshen kwad'ayi jin kunya! Mutumin da ya sayi gidan ya bada notice saura 'yan kwanaki, kana kuma ga wani can a gefe yana jiran miliyan daya da rabi wannan wane irin tashin hankali ne? Ido jawur! ta fito tsakar gidan da hijab a hannunta, Jamila na biye da bayanta itama kallo d'aya za kayi mata ka hango damuwa a tare da ita. Baba dake tsige alayyahu ya kalle su tana girgiza kanta, babu shakka ruwa baya tsami banza duba da yanayin fuskokinsu, bayan haka kuma ta zargi wani abu ne yake faruwa da mahaifin nasu duba yanda ta ji suna magana 'kasa-'kasa kamar ba sa so wani ya ji abinda suke tattaunawa. Cikin dushewar murya! da yanayin harshenta ta ce." Baba zan je na duba babanmu bashi da lafiya shine Jamila ta zo ta fad'a min." Cikin alhini ta ce." Allah sarki to ai ba kuka za kuyi ba addu'a za kuyi masa Allah ya tashi kafad'arsa ai cuta ba mutuwa ba ce; shin wai me yake damunsa ?" ta karasa maganar tana kallon jamilan dake kokarin mayar da k'wallar idonta. A sanyaye ta ce." Ciwon kai ne mai tsanani! amma da likita ya duba shi ya tabbatar mana da cewa jininsa ne ya hau?" "Allah sarki! ai abinda ake ta fama dashi kenan. Allah ya bashi lafiya." Gabad'aya suka amsa da "Ameen." 'Dari biyar ta mi'ka wa Shahidan da fadin." Kuyi kudin mota amma ki dawo da wuri kar ki bari dare yayi miki kin ji ko ." A sanyaye ta ce." Insha Allahu." Hanyar fita suka nufa ta ce." Jamila ki gaishe min da mai jikin kinji ko." Ta ce." Insha Allahu zan fad'a masa." Girgiza kanta tayi bayan fitar su, tausaya musu take na rashin samun nagartaccen uba! idan Jamilu bai yi hankali ba yanzu yaushe ne zai yi ? gashi Allah ya bashi zuria duk mata wannan shine abin dubawa. Lokacin da suka isa gidan yana bacci shi kadai a dakinsa, ita kuwa Talatu sai sabgoginta take, Hadiza bata nan ta je bikin 'kawarta, gidan a bushe 'kamas! yanzu ne Talatun take kujuba kujubar d'ora girki bayan ta je tayi fafutukar ciyo bashi a mak'ota! Babu arziki ta kalle su da fadin." Au! ita ki kaje kika jajibo me za tayi? ko kuma za ta iya biya masa bashin dake a bin sa ne." Ta ce." Haba Talatu wannan ba magana bace dani da Anty Shahida duk d'aya muke kuma itama tana da hakki na je na fada mata ne domin ta zo ta duba shi saboda yana matsayin mahaifinta. Tsaki! ta ja ta shige dakin girki ta bar su a tsaye a gurin da takaicin ta. To sai gefin magriba ya tashi daga baccin babu laifi da dama-dama jikin nasa. fitowa yayi domin daura alwala nan ya gansu a zaune a tsakar gidan sunyi jugum jugum! jikinsa ya k'ara yin sanyi! kunyar had'a ido yake dasu, da sauri ya dauki buta ya kama hanyar band'aki. Sai suka dinga rige rigen yi masa sannu! kansa kawai ya iya daga musu yayi saurin shiga band'akin Talatu ta bishi da zabgegiyar harara! "Baba ya jikin naka.''? Ba tare da ya kalle ta ba ya ce." Da sauki alhamdulillhi wanene ya fada miki bani da lafiya?" Ta goge hawayen da ya zubo a fuskarta ta ce." Jamila ce ta je ta fada min shine na ce bari na zo na duba ka, Baba Asabe ma ta ce ayi maka sannu.'' "Ina amsawa ai na ji sauki ki tashi ki tafi kada dare yayi." Ya fada yana dan kallonta ganin yanda take kuka sai abin ya bashi tsoro lallai baya shakka ta samu labarin abinda yake faruwa; sai kawai ya sunkuyar da kansa 'kasa ya san takaicin abin ke damun zuciyarta. Aikuwa ya tsinkayi maganarta. "Baba wace irin rayuwa ka jefa kanka a ciki? wace irin rayuwa kake so ka jefe mu a ciki shin wai baka tausaya mana ne?" Shuru yayi bai ce komai ba. Ta ja majina! tare da cigaba da cewa ." Gabadaya ka zubar da kima da mutumcinka a gari, babu wanda bai san irin harkar da kake ba, shifa arziki na Allah ne, wallahi ubangiji ba zai ta'ba azurtaka da haram ba! ko ya azurtaka din 'karshen nadama da jin kunya! shin meye ribar abinda kake? gashi ka jefa kanta cikin masifa da bala'i ka jefe mu a ciki, a yanzu ina muka ga miliyan daya da rabi? babban tashin hankalinmu wannan gidan da ya rage maka shima ka sarayar dashi yanzu da mu da kai ina zamu kama?" [11/17, 8:09 PM] Bintu: _••MAJNUN!••_ *'BOYAYYAN ATTAJIR!*🛩️ ~~~~~ *NA* *BINTA UMAR ABBALE🍒* *MANAZARTA WRTS ASS* ~~~~~ Tukwici ne gare ku mutana ne💕 _*1-AUTAR MANYA*_ _*2-ZEEY KUMURYA*_ _*3-AYSHA BARNO*_ Pege 41&42 Cike da fuffuka! irin wacce ya saba ya nuna ta da yatsa da fadin." Kada ki yi min maganar banza da wofi mana; don uwaki ni za ki zauna kina tsarawa magana, ke din guda nawa kike? me ki ka sani a rayuwa da har zaki zo kina kawo min 'kabli da ba'adi, to wannan shine gargadi na dake na karshe! kada wani abu ya sake faruwa ki zo kina min wasu zantuka ranki sai yayi mummunan 'baci! wallahi." A sanyaye ta ce." Kayi hakuri Baba." tsawa! ya daka mata ya nuna mata hanyar fita da fadin." Fita ki bani guri shashasha kawai." Da sauri ta fito tana share hawaye! Talatu ta ja tsaki da fadin." Aikin banza yarinya kina wahalar da hawayenki a wofi wannan mahaifin naku ai ya riga yayi nisa domin ba zai ta'ba gane hanya ba, don haka kowacce ta nemi madafa don duk wanda ya dogara da Jamilu 'bacin rai ne zai kashe shi." Hadiza ta ce." Talatu duk lalacewarsa ubanmu ne babu yanda za mu yi dole mu shiga damuwa." Ta ce." To ai sai ku yi karo karo ku biya masa bashin da ake bin sa shashashai kawai ana nusar da su suna baud'ewa." To in ban da rigima irin ta Talatu ya za suyi ? za su je su rufe shi da duka ne? ai ya riga ya gama yi musu illah! a rayuwarsu dole kuma suyi hakuri su cigaba da yi masa addu'a domin ba a canzawa towo suna. A na kiran sallar isha'i mai adaidaita sahu ya sauke ta a bakin titi. Kud'insa ta bashi ta fara kokarin tsallaka titin da nufin shiga layinsu, dan gabadaya Hankalinta yayi gida ganin garin yayi duhu, gashi babu wani cikkaken haske akan titin. tana kokarin tsallakawa kawai ta ji ana jan gefen hijab d'in ta. A razane! ta juyo sai tayi saurin ja da baya tana kallonsa gabanta na wani irin fad'uwa! Yana nan yanda yake sai dai an samu sauyin tufafi a jikinsa, amma fuskarsa tana nan cike da 'kasumba sumar kansa ka a cukurkud'e! Yana sanye da tazarce na shadda bulu sai dai ta kod'e sosai tayi haske sai wani takalmi sosa a kafarsa shima ya sud'e! amma babu datti a tare dashi. Murmushi kawai yake mata yayin da yake mata wani irin kallo. Ita kuwa gabanta sai bugawa! yake tana kallonsa tana so ta tabbatar da cewa shine ko kuma aljani

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});