Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Majanuni Book 3 Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kyau ya zo ya gaishe ka, kuma akwai alherin da yake tafe dashi." Bud'ar bakinsa sai ya ce." Ni da kai na nace ki fito da mijin aure, amma kin san dai a yanzu ba ni da kud'in da zanyi miki wata hidima ko? don haka maganar aure a tattara a ajiye a gefe guda. idan kuma zai aure ki babu kayan daki falillahil-hamdu." Ya ce."Babu komai Baba Shahida nakeso ita kanta ba wani k'yale-k'yale ba, buri na kawai ka bani ita. Wani irin kallo yake masa yana raya abubuwa da yawa a ransa! wannan mutumin da yake gabansa da ka gani talaka ne duba da yanayinsa, amma kuma ya yaba da nagartarsa kuma ba 'karamin yaro bane, Shahida 'yarsa ce mai rangwamin ga ta, shiyasa bai wani ci buri a kanta ba, amma zai so nagari ya aure ta ko dan ya kula da ita saboda lalurarta. Ya ce." Na baka yarinyar nan amana. sai abu na gaba wane alheri ne yake yafe da kai bayan wannan." Fuskarsa cike da annuri ya ce."Alhamdulillhi na gode sosai insha Allah zan kula da amanarka. bayan haka kuma Shahida ta shaida min irin halin da ka ke ciki na rayuwa, zanyi iyakar bakin kokari na akan lamarin. Ya ce." Wane irin taimako za kayi min? da ka ganinka dai talaka ne, wanda baka ajiye ba, baka bawa wani ajiya ba, shin ko akwai wata hanyar da ka ke samun kudi a b'oye kake yawo a tsiyace! kana da hanyar miliyan biyu da rabi ne?" Ya girgiza kai cikin rashin jin dadin maganganunsa ya ce." Eh insha Allahu, ina da alfarma a gurin maigidana, mutum ne shi mai tausayi da taimako insha Allahu zai duba uzuri na." Nan da nan fuskarsa ta washe ya ce." mutukar kuwa hakan ya tabbata baka da matar aure sai wannan yarinya na baka ita halak malak." Bai yi mamakin jin haka daga gare shi ba, ya ce."Shikkenan Baba na gode sosai, yanzu abinda za ayi shine ka bani number wayar mutumin da yake bin ka bashin kud'in koda maigidana zai bukaci magana dashi idan na koma can abujan." Ya ce." Don ta lamabar waya ai babu matsala sai na baka yanzu. Ya shiga fad'a masa lambar shi kuma yana d'auka a 'kwara'babbiyar wayar dake hannunsa da aka d'aure ta da kyaure. Sai bayan ya gama fada masa lambar wayar ne ya kalle shi da fadin." Da gani kai ba yaro bane ga alamun shekaru nan a tare da kai. shin kana da aure ko kuma yarinyar nan ita ce matarka ta farko?" Ya ce." Nayi aure shekarun baya har 'yata ta girma ta zama budurwa amma tana can garinmu." Ya ce." Ina kenan?" "Katsina a cikin karamar hukumar jibia, nan ne mahaifata. Ya ce." Ma sha Allah. kayi kokarin ganin ka fitar dani a wannan masifar ni kuma nayi maka alkawari sati guda yayi yawa gurin daurin auranka da yarinyar nan. Ya ce." Insha Allahu zanyi kokari." Gidan ya shige zuciyarsa fes! yau haihuwa za tayi masa rana. A tsakar gida ya same ta a tsaye. kamar wacce take jiran shigowarsa babu sannu da zuwa ta ce." Maganar da Jamila ta zo fad'a min gaskiya ne?" A lalace ya kalle ta kafin ya ce." 'kwarai kuwa yau haihuwa za tayi min rana dake da yaranki kun zama yuyuyu! sakarkaru kawai." Yana 'kare maganarsa ya bude dakinsa ya shiga ya bar ta a tsaye a gurin cike da d'umbun mamaki! A hanyar su ta komawa gida take tambayarsa ashe ya ta'ba aure har da haihuwa, ya tabbatar mata da gaskiyar magana ya ce." Amma yarinyar ta na can garinsu kamar yanda ya shedawa mahaifinta. Cike da 'kauna da begen juna su kayi sallama da juna tare da alkawarin cewa gobe da wuri zai zo ya gaisa da Baba Asabe kafin ya tafi. Lokacin da ta shiga gidan, muryoyinsu ta ji a can cikin daki harda Kawu Musa. gabanta ya fad'i! jin kawu Musa a gidan ba alheri ba ne. Saliha ta fito tsakar gidan ta sameta a tsaye ta kasa shiga dakin. Ta dan d'aga muryarta da fadin." Matar mahaukaci kin dawo kenan?" Kallonta kawai tayi amma ba tace mata komai ba, ba don ba taji haushin kalaminta ba. Suka fito daga dakin a tare, Baba Asabe na sake jadadda masa matakin da zata dauka akan al'amarin, ya yin da shi kuma yake nuna mata cewar tabi a hankali domin ba ta da k'arfi akan yarinyar kamar ubanta. Ya kalle ta suka had'a ido! sai tayi saurin sunkuyar da kanta kasa. Ya d'an bud'e muryarsa da fad'in." Shahida wannan rayuwar ki ka za'bawa kanki ko?" Shuru tayi hawaye na 'kok'arin kufce mata. Ya cigaba da cewa." Shin me ki ka hango a tare da wannan mutumin wanda shi ba mai hankali ba kuma ba mahaukaci ba, a matsayin ki na mara lafiya zaki za'bi wannan rayuwar da mara galihu. wanda ba a san asalinsa ba." Baba Asabe ta d'ora da fadin" Yo idan ba rashin hankali ba ina ke ina auran mahaukaci mutumin da ba a san daga ina ya ke b......gurin ta bari tana wani irin kuka! duk suka bita da kallon mamaki! lallai al'amarin yarinyar ya fi karfin tunaninsu. [12/8, 12:47 PM] Bintu: 47&48 To a daran ranar Talatu dai da kyar ta iya rintsawa, domin ta jima tana tunani akan al'amarin, ka da fa tana zaune baki a sake yarinyar da ta tsana! tayi mata zarra! tunda gashi tun kafin aje ko'ina Hujaj ya fara yi mata habaici ita da 'ya'yanta, dole ta je ta bincika domin sanin ainihin mutumin da ya ke neman auran yarinyar. Shahida da 'kunci! da 'bacin rai ta tashi. tsakanin Baba da Saliha jira take wani ya ce mata kule tace cas! domin gabad'ayansu a ciki take dasu, saboda suna kiran masoyinta da mahaukaci. Ta shiga d'akin ta same ta a kudindine a cikin bargo amma ba bacci take ba. kawai ta tsirawa rufin dakin ido! Ta d'an bud'e muryarta ta ce." Shahida ki tashi ki karya kummalo mana kina kwance kina tunane tunane mara amfani ko?" Ta mike zaune tana kallonta ta ce." Baba ina neman alfarma a gurinki." Kallonta tayi tana ayyana wani abu, labarin gizo dai baya wuce na koki, amma sai ta ce." To Allah ya sa zan iya. Ta ce." Don girman Allah da darajarsa ki kar'bi wannan al'amari da zuciya d'aya! wallahi nayi imani da Allah cewa alheri ni, nayi istahara akan al'amarin, Baban Baba ba zai cutar dani ba, mutumin kirki ne kuma ba mahaukaci bane kamar yanda ku ke zato, yau ce kawai ta mayar dashi haka, amma tunda ya samu ubangida ya koma mutum kamar kowa, arziki da rashi duk daga Allah suke, kiyi min addua kawai Allah ya sa hakan alheri ne. Gabadaya ta gama kashe mata jiki da kalamanta, a yanda ta shirya ta kuma kudire a ranta cewa sai bayan ranta wannan al'amari zai tabbata, amma wannan maganganun da tayi gabadaya gwiwarta tayi sanyi, babu shakka akwai wani abu da Allah ya rufe, kuma sha'anin aure irin wannan ba'a tsawwala wa domin idan ka tsananta sai ayi babu kai. Ta ce." Shikkenan Shahida na rabu dake da abinda ki ke so Allah ya sa hakan alheri ne dake

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});