Chapter 18
Chapter 18
sanye da singileti da wando iya gwiwa, cigaba yayi da motsa jikinsa ba tare da ya kalle ta ba. Tsugunawa tayi a gefansa da fadin." Ina kwana?" shuru yayi be amsa ba ya cigaba da abinda yake gabansa. "Don Allah kayi hakuri." Tafada cikin yanayin maganarta, gabadaya duk tayi sanyi ta fara nadamar wannan auran. Ya cire 'karamin towel din dake rataye a wuyansa. fuskarsa ya goge! kawai ya jefa mata towel din a jiki. Sai ta bi towel din da kallo tana mamakin abinda yayi. kallonsa tayi. suka had'a ido sai tayi saurin kawar da fuskarta. Ya tashi daga kan keken ya nufi gurin cin abinci ba tare da ya ce mata komai ba. Ganin haka sai ta ajiye masa towel din ta kama hanyar fita tana neman tsari dashi. Sunanta ya kira tana daf da fita. Ta juyo tana kallonsa fuskarta sam! babu fara'a. "Zo ki zuba min abinci" hankalinsa na kan wayarsa yayi maganar. Girgiza kanta tayi ta koma da baya domin bin umarinsa. Ta had'a masa komai ta ajiye a gabansa kafin ta ce." Zan iya tafiya?" Kansa ya girgiza alamun A'a. sai ta tsaya tana kallonsa da jiran umarni na gaba. Sai da ya mula tukkuna ya ajiye wayar hannunsa kafin ya kalle ta a sakarce ya ce." Kinyi kyau cikin hijabi." Tayi shuru dai ba tace uffan ba. Gabadaya girmansa ya zube a idonta. Ya ce'' Na ga kina ta wani rufe-rufe me ki ke b'oyewa ne?" Ta ce." Babu komai." Girgiza kansa yayi ya ce."Ban yarda ba gaskiya, ba zaki fita ba sai kin cire wannan hijabin na duba ki." Taji wani irin fad'uwar gaba! ta kalle shi idonsa k'ur! a kanta kamar tsohon maye! Ta ce" Shigowata ban kai minti goma ba kuma iyakata nan falon me kake tunanin zan d'auka?" Ya daga kafad'a da fad'in." Ni dai ban yarda ba saboda haka ki cire idan kuma kinyi gardama to zan cire miki da kaina. Cikin rawar murya ta ce." Kai fa uba ne, ka haifa kasan mai kyau da mara kyau, yanzu idan akayi wa 'yarka abinda kake min za ka ji dad'i?" "Ba zan ji dadi ba gaskiya" Serious ya fadi maganar. Ta ce." To mai yasa ka keyi min haka?" Shuru yayi be ce komai ba illah kofin shayi da ya d'auka yana kur'ba! Ta ce" Zan iya tafiya?" Ya ta'be baki "A'a nifa har yanzu ban yarda dake ba, mutukar zaki shigo nan to ki dinga sa mayafi wannan hijabin akwai munafurci a ciki. Cike da takaici da mugun haushinsa ta ce." Ba hali na bane sata, kuma ba zan fara anan ba, don haka ka daina d'aukar alhakina. Bagarar da maganar yayi ya cigaba da kur'bar shayinsa. Yanda ya ke wulakantata hakan yana yi mata ciwo mutu'ka! sai kawai ta kama hanyar fita a karo na biyu ya dakatar da ita da fadin." Har yanzu ban baki izinin fita ba don haka dawo ki tsaya." Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke ta koma da baya ta tsaya tana facing d'in shi, ya 'kura mata mayunwatan idanuwansa masu je fata cikin tashin hankali. Sai da ya gama karyawa tsaf! sannan ya tashi ya fito daga tsakanin kujerun ya nufi gurin da take tsaye. Ta ji fad'uwar gaba sosai! amma ba ta karaya ba, domin kuwa tasan duk shaid'ancin mutum bai fi karfin addu'a ba, tana da tabbacin cewa sai ta samu rinjaye a kansa. Daf da ita ya tsaya yana lumshe mata shu'uman idanuwansa. Ta kawar da fuskarta tana cigaba da nanata addu'ar neman rinjaye a bakinta. Ya sanya hannu da nufin cire hijabin jikinta. Ba tare da jin nauyi ba ta buge hannunsa da karfin gaske! bahaushe ya ce ." Idan babba ya zubar da girmansa yaro zai iya hawa kai ya tattaka. Ya dube ta da fad'in" Ba ki ji nauyin abinda ki kayi ba?" Zum'bura bakinta tayi tana d'an ture shi da 'kokarin so ta fita daga tsakaninsa domin ya babbake gurin yayi mata rumfa. Ya sake kama 'kasan hijab din a karo na biyu, sai ta sake wancakalar da hannunsa, ta tsinci kanta da nuna shi da yatsa da fadin" Wallahi zan baka mamaki yanzu nan!" cikin zafin zuciya ta fad'i maganar jikinta na wani irin karkarwa! Bai wani tsorata ba, sai ma sake matse ta da yayi jikin bango (garu) ya tallafo fuskarta da hannunsa d'aya, aikuwa karan hancinsa dake daf da bakinta ta gartsawa cizo! tana nema ta gutsire masa saman hanci! babu shiri ya matsa gefe yana shafa gurin da ta cije shi wanda yayi sheda tare da rurucewa! Zazzafar harara! ta buga masa kafin ta ja masa dogon tsaki! tana 'kun'kuni! ta wuce ta bar shi a tsaye a gurin yana bin ta da kallo har ta bud'e 'kofa ta fita. [12/16, 7:25 PM] Bintu: _'Karshen littafi na d'aya kenan, sai mu tara a cikin littafi na biyu, wanda ya kasance na kud'i #500 vip 1k za a tura kudin ta wannan account din...0542382124...Binta umar gtbank, idan kati za a turo sai ayi min magana ta WhatsApp da wannan numbers.. 07084653262.or 08089965176. BINTA UMAR ABBALE_ 59&60 Ya jima yana jinyyar karan hancinsa kafin ya daina masa ciwo, sai dai sa'i da lokaci idan ya tuna abinda ya faru tsakaninsa da yarinyar sai yayi murmushi! cikin zuciyarsa yake addua'a akan Allah yasa ta cinye jarrabawarsa, domin d'an zaman da su kayi tare sonta da k'aunarta ya gama mamaye jini da gangar jikinsa. A na ta 'bangaran kuwa daina walwala tayi a gidan, motsi kadan za ta tsorata, domin tana fargabar kada ya kawo mata farmaki har gurinta. Bata sake saki jikinta ba sai da su Hajiya suka dawo sannan. ta warware amma duk da haka Hajiyan sai da ta lura da wani abu, sai take tambayarta ko akwai abunda ke damunta ta daina sakewa, da sauri ta ce "babu komai wallahi kaina ne kawai yake ciwo." Hajiya ta ce'' Ai fa na ga alama saboda ba haka muka tafi muka bar ki ba, to amma kin shedawa mijinki domin naga kina da k'wauron baki'' Murmushi tayi ta ce." Eh na fada masa har ya siyo min magani na sha." Ta ce."To Allah ya raba lafiya." domin ita Hajiyan a tunaninta ko ciki ne da ita. Ta ce." Ki je ki kwanta ki huta ai sai da lafiya ake komai." Sosai tayi farin cikin hakan, sakamakon ganin saukowarsa tasan tabbas idan yana gurin ba zata iya sakewa ba. Ya zauna kujerar dake fuskantarta. sai ta sunkuyar da kanta a hankali ta ce." Ina kwana?" ya d'aga mata hannu ba tare da ya amsa ba. Hajiya ta kalle shi da fadin." Yarinyar nan bata da lafiya har nake zargin ko ciki ne da ita?" Gabansa ya fad'i ya kalle ta da fadin." Wane irin ciki kuma Hajiya duka-duka yaushe su kayi auran?" Murmushi tayi da fad'in." Yo tsakanin mace da miji ai sai Allah, ai yanzu kamar tuntu'be akeyi dashi a hanya, shine nake tambayarta mijinta ya sani, ta ce" Eh har magani ya siyo mata." Ya kalle ta tare da bud'e muryarsa yanda za ta ji sosai ya ce" Ke da gaske ciki ne dake?" Kunya duk ta rufe ta, sunkuyar da kanta tayi tana jin nauyi don gani take kamar maganar tayi
Table of Contents