Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Majanuni Book 3 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tsantsar mamaki a tare da ita lallai ma wannan mutumin da alama bashi da kamun kai Fita tayi daga tsakanin kujerun. Ya kira sunanta, ta kalle shi ba tare data amsa ba. Babu walwala a tattare dashi ya ce." Hau sama ki gyara min gado na. Taji wani irin miyau! ya tsinke a bakinta tsabar tashin hankali. Baki na rawa ta ce." Yallabai kamar hakan bai dace ba, kana yin wasu abubuwan da basu cancanta da kai ba. Ya ce" Na san ke matar aure ce, kuma matar yaro na, to ina so ki sani; shi mijin naki a 'karkashi na yake, dake dashi duk abin iko na ne, saboda haka kada ki sake yi min jayyaya akan umarni na. Jikinta yayi sanyi tana sake tuno jan kunnen da mijin nata yake mata akansa. Abincinsa ya fara ci ba tare da ya sake kallonta ba. Ta saci kallonsa ta gefen ido, sai ta ga babu walwala a fuskarsa. A hankali ta kama hanyar matattakalar bene tana addu'ar neman tsari a zuciyarta. Tsaruwar d'akin sam bashi ne a gabanta ba, babban burinta ta gama abinda take yi ta fita. Tana tsaka da gyara shimfid'ar gadon ya shigo dakin. Gabanta ya tsananta fad'uwa! duk sai ta rasa abinda za tayi, ta dinga sauri tana jere filo sam ta'ki kallonsa sai sanda ta ji kamar yana murzawa 'kofar mukulli (key) sannan ta zabura! ta kalle shi, lokacin ya rufe 'kofar ya nufi inda take. [12/15, 12:28 PM] Bintu: 57&58 A tsorace take kallonsa a lokacin da yake 'kokarin zuwa gurin da take tsaye. Cikin wata irin tafiyar isa da ta'kama! ya tsaya daf da ita hucin numfashinsa na dukan fuskarta. hannu ya sa cikin aljihu. kafin yasa d'aya hannun ya rungumota jikinsa! rikon tsauri! yayi mata da hannu d'aya yana sumbatar gefen fuskarta. Wani irin hauka da buge-buge! ta shiga yi duk domin ta 'kwaci kanta daga hannunsa! ta samu gefen kafad'arsa ta gartsa masa cizo! wanda yayi sanadiyar sakinta, sai ta matsa gefe tana mayar da numfashi tare da wani irin kuka! mai ciwo! jikinta na kyarma! tsigar jikinta gabad'aya ta tashi. Kallonta yake da idanuwan da suka sanja launi! ta zabga masa muguwar harara! cikin tsananin jin ciwo da takaicin abinda yayi mata ta ce." Wallahi ka ji kunya! ashe dama baka da kirki ko?" Ya tsira mata rikitattun idanuwansa dake cike da tsantsar fitina ta shekara da shekaru! gabad'aya yarinyar ta gama tayar masa da hankali. Ta je ta rarumi gwangwanin turare a kan madubi ta jefa masa tana kuka ta ce." Sai Allah ya saka min abinda kayi min, kuma sai na fad'awa mijina." Ya 'bata rai! kafin ya bud'e muryarsa sosai ya ce" Kafin ki fad'a masa ni zan riga ki, dake dashi duk abin iko na ne, saboda haka ki fice min daga daki" Da k'arfi ya k'arasa maganar yana nuna mata hanyar fita da hannunsa. Ta sake d'aukar wani gwangwanin ta je fa masa wanda ya sauka a goshinsa, tana zubar da hawaye ta ce" Ban yafe ba daka ta'ba ni." yanda ta ke rawar jiki da yanda take kuka har cikin ranta ya tabbatar masa da cewa ta ji ciwon abinda ya yi. Sai ya mi'ke da azama ya nufe ta, ta zabura! a guje tayi hanyar fita, garin kici-kicin bud'e kofar ta zame ta fad'i a gurin, rintse idonta tayi ganinsa a tsaye a kanta ya yi mata rumfa. Ta rufe fuskarta da tafin hannunta "Don Allah kada ke ta min haddi, ka dubi darajar aure kada ka sake ta'ba ni." tafad'a jikinta na wani irin rawa. Hannu biyu yasa ya d'ago ta ta mi'ke tsaye, ya tsirawa fuskarta ido, hawaye sai tsare suke a saman fuskar, harshe yasa yana tsotse hawayen, gabad'aya k'afafunta suka kasa d'aukarta, sai k'o'karin zubewa take a gurin, yana tallafota. Yanzu ma haukan ta sake yi masa tasa dukkanin 'karfinta ta dinga dukansa a k'irji har sai da ya saketa, ta zube a gurin tana wani irin kuka mai cin rai! Tayi tur! da wannan rayuwa da take. tayi Allah wadai da ita. Ya tsuguna gabanta tare da k'okarin daidaita yanayinsa ya ce." Ko na kwanta dake mijinki babu abinda zai ce, saboda iko na ne, ke kuma baki da wata daraja! sannan na ji kina maganar aure! to ki daina daukar wannan auran naku da mutunci, domin duk ina da labarin yanda akayi shi, da kud'i na aka fansheki a gurin mahaifinki, saboda haka ina da iko da damar nayi duk abinda nakeso dake. Wani irin kallo take masa bakinta ya mutu murus! gabad'aya ta rasa a wane mizani za ta ajiye maganarsa. Ganin tayi sanyi ta gagara magantuwa yasa ya mi'ke tsaye, anan ne ta girmansa ya bayyana sosai! ya tashi, saboda yanayin kayan dake jikinsa masu kwanciya a jiki ne, wannan dalilin yasa girmansa fitowa, gaskiya ta tsorata! da yanayin, sai tayi gaggawar d'auke idonta tana kiran sunan Allah a zuciyarta, tunda ta ke, bata ta'ba ganin girman namiji irin haka ba sai akan wannan mutumin da yake kokarin keta mata alfarma. "Tashi ki fitar min a daki.'' Maganarsa ta dawo da ita hayyacinta, da sauri ta tashi har dankwalin kanta yana fad'uwa, anan ne ya ga tarin sumar kanta, ya sake shiga rud'ani, domin a rayuwarsa yana masifar son mace mai gashi, kawar da kansa yayi daga barin kallonta ya nuna mata hanyar fita da fadin." Yanzu nan zan kira mijin ki na sheda masa irin zagi da cin mutumcin da ki kayi min." Ya fadi maganar ne yanda za taji. Muguwar harara! ta buga masa kafin ta ja dogon tsaki! ta fita ta barshi a tsaye da kwantaccen murmushi a fuskarsa. Jiki a mace ya nemi guri ya zauna tare da dafe kansa, gabad'aya jikinsa ya rikirkice sha'awa ta shekara da shekaru ta taso masa, bai san ya zai yi ba a halin yanzu. Yinin kuka da damuwa tayi, duk ta tsargi kanta da kanta, sa'i da lokaci idan ta tuna al'amarin sai gabanta yayi ta fad'uwa, adduar kariya kawai ta lazumta domin ita kad'ai ce magani a gare ta. Wajejan goma da rabi na dare ya turo mata text cewa ta kiyayi 'bacin ransa idan ya dawo domin ya ji labarin abinda tayi wa maigidansa saboda haka tayi gaggawar zuwa ta bashi hakuri. Amsa ta bashi kamar haka; "Da kasan abinda ya faru a tsakanina dashi ba zaka fad'i haka ba maigidanka mutumin banza ne don haka ni ba zan bashi hakuri ba. Sai ya bata amsa da cewa; Ashe kuwa auranki yana gargada domin kuwa mutukar ba ki je kin bashi hakuri ba wallahi zan iya sakin ki." Jikinta yayi sanyi jin abinda ya ce. sai tayi shuru tana tunanin yanda za ayi ta je ta bashi hakuri bayan tasan shine mara gaskiya. Ya sake turo mata da wani sakon, cewa; "Lallai kada ta tsallake umarninsa a daran nan taje ta bashi hakuri. Agogo ta duba sha d'aya saura na dare, ya za'ayi ta iya fita a wannan daran. gaskiya sai dai da safe, shima don ba yanda za tayi ne. Yau cikin hijabi har 'kasa ta shirya jikinta, babu walwala a tare da ita nufi cikin gidan. Zaune a falo ta same shi kan wani keke irin na motsa jiki, yana

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});