Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 19

Chapter 19

Majanuni Book 3 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kama da ta rainin hankali! kwana d'aya kacal da aurensu ya dauk'e mata miji ya kai shi uwa duniya, zai zo yana tambayarta sai dai idan shine yayi mata cikin. ita da zuciyarta take magana. Hajiya Saude tasa dariya da fadin." Kai ma dai da wani abu, to idan shine a tunaninka za ta fad'a maka ne? ni ma hasashe kawai nake. Ba tare da ya ce komai ba ya dubi agogon dake daure a hannunsa, ya kalle ta da fadin " Hajiya zan fita" Ta ce" To Allah ya bada sa'a." ya amsa da "ameen yana kokarin tashi. Shukura ta fito daga d'akinta. Sai ya tsaya yana kallonta, ta ce." Daddy ina kwana?" ya amsa babu yabo babu fallasa. Ta ce."Hajiya ta fad'a maka sakon mommyna." Ya kalli Hajiyan domin jin 'karin bayani. Ta ce" Neman magana ne kawai irin na Hajiya Fatima, mun shirya dawowa gida ne shine take ba mu sa'kon gaisuwarta gare ka. Bai ce komai ba ya kama hanyar fita, sai suka bi shi da kallo jikinsu a sanyaye Hajiya ta riga tasan halinsa tun yana yaro mutukar ya bar abu to bar shi har abadah, wannan dalilin ne yasa take tausayawa Hajiya Fatima duba da irin wahalar da take sha a kansa ya'ki sauraranta, shekara da shekaru da rabuwar auransu, ta'ki aure ita lallai tana jira yazo ya mayar da ita d'akinta, in da shi kuma ya ci alwashin sai dai ya mutu babu aure mutukar sai ya zauna da ita ne. 'Yan uwa da ita kanta kakar tasa sunyi-sunyi har sun ha'kura, domin mai daki shi ya san in da yake masa oyoyo, shi kadai ya san irin wahalar da ta bashi a lokacin da suke tare. **** BAYAN KWANA BIYAR Tana zaune 'kasan kafet tana cin abinci wanda ci kawai ta ke yi saboda ta kori yunwa ba wai don abincin babu dadi ba, A'a sai don ta san mutukar ta kwanta da yunwa to tabbas zata tashi a galabaice! shiyasa take tuttura abincin tana had'awa da ruwa. Motsi ta ji ana kokarin bud'e kofar shigowa, gabanta ya yanke ya fad'i! ta tsirawa kofar ido tana addua a zuciyarta, domin ba ta kawo cewa mijinta bane ta fi tunanin maigidan ne da yake kai mata hari a duk lokacin da su had'u sai ya san yanda yayi ya ta'ba jikinta, wannan abu yana yi mata ciwo mutuk'a! ita ba abun ta zazzage shi ba tana cikin gidansa, sai dai duk sanda ya ta'ba jikinta ko ya cire mata dankwali sai ta yini tana share hawayen takaici wanda ya ajiye ta ma bai ta'ba ri'ke mata hannu ba amma shi kuwa har ya samu sararin rungumeta yana tatta'ba wasu abubuwa na jikinta. Da 'karamar wayarsa yake haske falon ya hange ta zaune kamar kace kyatt! ta ruga a guje! Ganinsa yasa ta sauke ajiyar zuciya tana godewa Allah a cikin ranta da sauri ta je ta rungumeshi kawai sai ta fashe da kuka! tana sake matse shi a jikinta. Wani yanayi ya shiga amma bai bari yayi tasiri a tare dashi ba. yasa hannu ya cire ta daga jikinsa hanyar dakinsa ya nufa ba tare da ya ce mata uffan ba. A sanyaye ta je ta zauna tana kallon d'akin dake rufe don bayan shigarsa mukulli yasa ya kulle ba tare da ya tsaya ya saurareta ba. Kwanan 'kunci da 'bakin ciki tayi ido luhu-luhu! ta tashi don ba ta iya shiga kicin ba kwanciya tayi lamo kan kujera zazzabi na neman rufe ta. Tsayin kwanaki uku da dawowarsa uffan be ce mata ba, ko ta gaishe shi baya amsawa, fushi yake sosai! da ita. idan ya fita tun safe baya shigowa sai dare wajejen sha biyu. Sosai ta shiga damuwa matsananciya tun tana zazza'bi! sama-sama har ya kai ta 'kasa! ta dinga kwara amai, yana daki ya ji kakarinta! da sauri ya fito ya tarairaye ta bayan ta gama aman ya wanke mata baki ya kai ta kan kujera ya kwantar. Kicin ya shiga ya had'o mata shayi tea. da kyar ta iya shan rabin kofi ta koma ta kwanta tana lumshe idonta, gabad'aya yanzu ta daina sonsa tunda bashi da imani. Tsayin kwana uku yana kula da ita kafin ta warware sosai! sai aka koma 'yar gidan jiya, yana amsa gaisuwarta amma baya tsayawa suyi doguwar magana da juna ballantana ya ji damuwarta. Wannan abu yana mata ciwo sosai! cikin ranta sai nadamar auransa take. **** "Saliha jiya nayi mafarki da Shahida cikin wani yanayi mara dad'i." Baba Asabe ke wannan maganar lokacin da take d'ura man gyada a kwalba. Hankalinta na kan wayar dake hannunta Ta ce."Hum Baba Asabe kenan." Ta ce."Ko za ki yi mata magana ne da wayarki." Ta ce'' Baba raba ni da yarinyar nan don Allah na san dai mahaukacin nan ya fara cin ubanta." Ta ce." Saliha fata nagari lamiri, ba na jin dadin irin wannan maganganun da ki ke akan Shahida. Murmushi tayi kafin ta ce" Bari na tura mata text (sak'o) na san idan ta gani za ta bada amsa, tunda kin san dai idan an kira ta a waya ba lallai ne ta ji ba. Ta ce."To shikkenan Allah yasa mu ji alheri. Ba tare da ta bawa maganar muhimmanci ba ta amsa da "ameen" ***** _"Ke Shahida dama ba komai ne yasa na turo miki wannan text din ba. Baba Asabe ta dame ni wai lallai ta na so ta ji lafiyarki, saboda haka sai ki bata amsa."_ Wannan shine abinda Saliha ta rubuta. Tana hawaye take tura amsa kamar haka. _"Wallahi ina nan lafiya lou Saliha ki kwantar mata da hankali ki ce ina gaishe ta da kyau zan kuma zo ba da jimawa ba"_ Daga dakinsa ya fito ya ga tana kuka! sai tayi saurin share hawayen amma ba su daina zuba ba. Ya zo ya 'karbi wayar yana dubawa. Tausayi ta bashi ganin irin amsar da ta bayar, hakan ya sake tabbatar masa da cewa lallai zata ri'ke masa sirrin gidansa cikin ko wane hali. Bai nuna farin ciki a fuskarsa ba, sai ma yasa wayar cikin aljihunsa ya ci kunu sosai! ya zauna yana fuskantar ta. Zaman da yayi ta san DA WATA A 'KASA, sai ta sunkuyar da kanta tana neman sassauci gurin Allah. Ya bud'e muryarsa sosai yanda za ta ji ya ce." Maigidana ya sake tura ni legos domin wani aiki! zan tafi yanzu don na kammala duk wasu shirye-shirye, saboda haka ina sake gargad'inki da kakkausar murya! ki kula da abinda zai 'bata masa rai! domin ya fi karfin komai a guri na, bayan haka kuma da kud'insa na aure ki, yana da iko dani da abinda na mallaka! duk abinda yake buk'ata kiyi masa, ki kula da kakarsa da kyau! wannan shine gargad'in da zanyi miki.'' Hawaye wani na bin wani ta ce." Don Allah kada kayi min haka, ka nema min alfarma a gurinsa ka tafi dani duk in da za kaje domin ina bukatarka a kusa dani, bayan haka kuma wannan mutumin bashi da hali mai kyau! farautata yake a duk sanda ya tura ka wani gari." Ya mi'ke tsaye! cikin fad'a ya ce" Sharri za kiyi masa? me zai yi dake? ina abin burgewa da sha'awa a jikinki da

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});