Chapter 1
Chapter 1
[11/10, 1:25 PM] Bintu: _MAJNUN!_ *'BOYAYYAN ATTAJIRI* *NA* *BINTA UMAR ABBALE🍒* ___ *MANAZARTA WRTS ASS* Pege 37&38 'Kamshi turaran ta ne ya sheda masa zuwan ta gurin. Cikin nutsuwa ya d'ago kansa daga barin karanta jaridar da ke hannunsa. 'Bata fuskarsa yayi yana yi mata wani irin kallo na tuhuma. Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba ta fara kokarin zama a kujerar dake fuskantar sa. A tsawa! ce ya dakatar da ita daga abinda take shirin yi. "Ka da ki sake ki zauna anan gurin.'' Ya fada yana zare mata gabad'aya idanuwansa yanda ya tsani mutuwarsa haka ya tsane ta Fatima tayi masa illah a rayuwarsa. Da hannu ya nuna mata hanya da fadin." Fita ki bani gurin tun kafin ranki ya 'baci." Ta girgiza kai still da murmushin a fuskarta ta ce." Ai ko babu komai ka tsaya ka saurare ni domin kaji da abinda nake tafe, idan ban ci albarkacin Shukura ba sai na ci arzikin zumuncin dake tsakaninmu." Tsaki ya ja ya koma ya zauna tare da cigaba da karanta jaridar dake hannunsa. Gurin yayi shuru na minti biyar kafin ta sauke zazzafar ajiyar zuciya ta kalle shi wani irin bala'in son sa na ratsa dukkan sassanan jikinta, ita ce tayi wauta a wancan lokacin, gashi yanzu yayi mata nisa tayi-tayi ta shawo kansa ta kasa, saboda babu wacce ya tsana sama da ita.'' "Maganar Shukura nake tafe da ita." Ta yi maganar idonta a kansa. Shuru bai d'ago kansa ba ballananta ya bata amsa. sai ta d'ora da fadin." Aiki na samo mata a babban kotun birnin tarraya ina fata ba zaka watsa min 'kasa a ido ba." Babu walwala a fuskarsa ya ce." Babu wani aiki da Shukura za tayi, buri na na ga na aurar da ita ga wanda ya da ce, saboda haka wannan maganar ki ajiye ta a gefe.'' "Me kake nufi kenan.? ta fada d'a b'acin rai a tare da ita. Ya ce." Ban amince da kud'irin ki ba." Sai ta fusata! "Amma dai ka san ba kai kad'ai ka ke da iko da ita ba ko? "Yes na sani da ni da ke muka haife ta amma abinda nake so shi za a yi idan kuma akwai matakin da zaki d'auka bisimillah." Fuska a tur'be ta mi'ke tsaye! "Shikkenan tunda haka ka ce zan nuna maka nawa ikon a kanta." Fuuu! ta bar gurin ranta a mugun b'ace! Dogon tsaki! ya ja ya bita da mummunan kallo har sai da ta fita daga gurin. Ya d'auke kansa yana jan ajiyar zuciya tare da tuno kuttun 'bakin cikin da ta k'unsa masa a can baya. ******* Da azama ta shiga d'akin sai dai me? tuntube tayi da ita a raku'be jikin dirowar gado ta hada kanta da gwiwa tana wani irin kuka mai tsuma zuciya! Gabanta na fad'uwa ta ambaci sunanta a sanyaye ta ce." Shahida ba zaki fada min abinda ke damunki ba ko? kullum sai ki 'buya a daki kina kuka idan maganar Saminu ce ai ta mutu ki daina damun kanki mutu'kar ina raye ba zan bari mahaifinki yayi miki auran dole ba." Jin yanda take tausar ta da kalamai masu sanyi ya sanya ta sassauta kukan da take yi ta sa hannu ta goge hawayen dake gudana a fuskarta ta ce." Baba ba zaki iya magan ce min matsala ta ba, watakila ma idan na fad'a miki damuwa ta ki kira ni mahaukaciya, shiyasa na gwammace damuwar da nake ciki ta zama ajali na." Maganar ta doke ta sosai! kafafuwanta su kayi sanyi sai ta nemi guri ta zauna tare da fadin." Shahida wace irin damuwa ce wannan ? wacce har ki ke ikirarin ta zama ajalin ki, kada dai a kan mahaukacin mutumin nan ki ke nema ki kashe kanki."? Jin abinda Baban tace yasa ta 'kunshe bakinta da tafin hannunta domin ta hana kukan dake k'okarin kufce mata fita. Ta dinga girgiza kanta zafafan hawaye na sharara a fuskarta, murya a sar'ke da yanayin harshenta ta ce." Ki daina kiran sa da wannan sunan domin bai cancanta ba wallahi shi din ba mahaukaci bane kuma zan iya sadaukar da farin ciki na akan sa." Jikinta ya 'kara yin la'asar jin furucin da yarinyar tayi. ya kamata ta daina tsawwala wa domin ba ta san abinda Allah ya lullu'be ba amma babu shakka al'amarin yana bata tsoro mutu'ka! Ta ce.'' To na ji na daina kiran sa da mahaukaci ko zaki iya fad'a min abinda ya same shi domin tabbas ruwa baya tsami banza Shahida baki ta'ba shiga damuwa ta kwana da kwanaki ba irin wannan ko shakka ba nayi akansa ne." Hanci taja tana jin wani irin rashin dadi a tare da ita ta ce." Yau tsayin kwana goma kenan ban sanya shi a idona ba tun bayan korar da akayi masa daga mazauninsa shikkenan ban sake ganinsa ba, ko na je bakin kasuwar haka zan dawo gida gabad'aya ma mutane sun watsar da kayan sa a bola sai filin gurin tunda mai motar ya d'auke abar sa." Wani irin sanyi ta ji a zuciyar ta amma ba ta nuna a zahiri ba, sai ta shiga girgiza kai cikin alhini da damuwa ta ce." Ayya! Allah sarki shi yasa ashe kwana biyu na ga ba kya kai masa abinci ashe abinda ya faru kenan amma na tausayawa mutumin nan wallahi." Zuciyar ta ta 'kara yin rauni! kukan da take dannewa ya kufce! ta ce." Ni yanzu ban san ya zanyi ba zuciyata tana so ta gan shi ban san a wane hali yake ciki ba, ya kamata a taimaka masa." Kallon tausayi takewa yarinyar domin kuwa Allah ya jarabce ta da soyayya a in da bai da ce ba sai dai addua kawai. Ta ce." Ki share hawayen ki ki daina kuka insha Allahu zan taya ki da addua kuma zan sanya ayi miki saukar al'kur'ani a kan lamari idan da rabon zaku sake had'uwa sai Allah ya had'a ku a wani guri na daban." Hannunta ta ri'ke da fadin." Na gode Baba Allah ya saka miki da alkairi, insha Allahu nima zan dage da addu'a Allah ya bayyana mana shi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali." ******* "Alhaji Sammani mai leshi wani d'an kasuwa ne wanda ya kasance abokin hurd'ar Hujaj ta 'boye! shima yana caca kuma yana samun alkairai sosai yana kasuwancin ne kawai domin kawar da hankalin jama'a daga kansa. Tarin kud'ad'an da yake bin Hujaj ba za su lissafu ba, domin gabad'aya duniya ta juya masa baya komai nasa ya tsaya cak! sai buge-buge! yake yana yawon malamai k'auyuka da zaurukan malamai ba irin wanda bai je ba domin a duba masa me yake faruwa da rayuwar sa. Kimanin miliyan biyu da rabi Alhaji Sammani yake bin sa, kuma a wannan lokacin ya bu'kaci da ya bashi kud'insa domin yin wata bu'kata! Ya rasa ina zai tsoma rayuwarsa yayi nan yayi can fagau-fagau! ya zama wani shashasha! har ya fara surutai a hanya, shawarar da ya yanke shine sanya gidansa a kasuwa domin ya biya bashin kudin da ake bin sa! [11/14, 11:03 AM] Bintu: _MAJNUN!_ *'BOYAYYAN -ATTAJIRI!* *NA* *BINTA UMAR ABBALE🍒* ______ *MANAZARTA WRTS ASS* Pege 39&40 To koda ya sanya gidan nasa a kasuwa bata canza zani
Table of Contents