Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 11

Chapter 11

Majanuni Book 3 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fada da farko cewa." Mutumin nan sanadiyarsa na fita daga cikin rud'ani, to wallahi ko doke-doke yake yana tsince-tsince a bola hakan ba zai hana ni na bashi yarinyar nan ba, dalili ya rufa min asiri na a lokacin da yake daf da tonuwa". Jiki a sanyaye ta ce Allah ya sanya alheri. Ya amsa da "Ameen ya cigaba da cewa." Gobe da sassafe zai zo ya d'auke ta su tafi can abujan inda yake aiki, yayi alkawarin cewa bayan an kwana biyu, zai zo ya dauke ni domin na je naga mazauninsu, na amince da maganarsa dari bisa dari! ke Shahida wannan mutumin daga yau shine uwarki shine ubanki! kuma mijinki, yi nayi bari na bari, ke ki ka ganshi kina so ki ka amince da auransa, saboda haka kada naji wata magana ta biyo baya wannan shine abinda zan fad'a miki." Ta d'aga kanta da fadin." Insha Allahu zanyi kokarin yi masa biyayya Baba a cigaba da yi mana addua'a." Ya kalli Baba Asabe da fad'in." Ko akwai nasihar da za kiyi mata domin tafiya nake so nayi da ita can gidana da wuri za su wuce." Ta ce."Ai ka riga ka gama yi mata nasiha Jamilu ni kuma a suwa! a matsayinka na ubanta ai ka gama komai.'' Ko a jikinsa, ya kalli Shahidan da fad'in " Ki shiryo ki fito ina waje ina jiranki." Ya mi'ke tsaye tare da zura hannu cikin aljihu, dubu uku ya d'auko ya ajiye a gabanta da fadin " Allah ya bamu alheri.'' Cike da rashin kuzari ta bishi da kallo tana Allah wadai da mugun halinsa. Ta juya ta kalle ta tana zaune ta kasa tashi ballantana ta shirya kamar yanda ya umarce ta. Ta d'an bud'e muryarta da fad'in." Ki tashi ki sanyo mayafi ki bishi Shahida ai magana ta 'kare, ni dai nayi iyakar bakin kokari na akan lamarin, ba zanyi miki baki ba sai dai adduar Allah ya tabbatar da alheri." Wani irin kuka ya kufce mata sai kawai ta rungume ta a jikinta tana fadin." Baba don Allah ki yafe min kada ki k'ulla ce ni, ki cigaba da yi min addua." Tana kuka sosai ta ce " Shahida addua a kanki ai yanzu na fara, ba zan daina ba har sai ranar da Allah ya dauki raina, amma har a cikin raina ban so kiyi wannan rayuwar ba, na so ki auri miji nutsatstse mai hankali d'an gari mafi kusa dani wanda zai kula min dake da lalurarki, amma hakan bai samu ba, sai wannan kaddara to ina rokon Allah yasa ta zama alheri." Sosai suka rungume juna suna ta kuka! Saliha ta dinga kyalkyala musu dariya tana yi musu vedio, da 'kyar suka rabu da juna kowanne zuciyarsa babu dadi, mussaman Baba Asabe da har yanzu abin bai kwanta mata a rai ba. Ita kuwa Shahida kukan rabuwa da ita kawai take, amma a cikin zuciyarta ba ta tunanin komai face alheri domin ba ta tsammanin cewa masoyin nata zai cutar da ita. To tun a mota ta sha jinin jikinta gabad'aya sai tayi sanyi jikinta ya mutu! ta dinga kallonsa a fakaice! tana jin wani irin tsoro a cikin zuciyarta. Gabad'aya kamar tunda aka hallice shi bai ta'ba dariya ba, fuskarsa murtuk! sam ya ma'ki yarda ya kalle ta ballanatana ta samu sararin yi masa wata magana, tun bayan da ya d'auko ta daga gaban mahaifinta ya rikid'e! ya zama mara farin ciki ko a motar ma bai yarda ta zauna a kusa dashi ba, cewa yayi taje can ta zauna cikin mata 'yan uwanta. Ta dinga tunane-tunane marasa kyau a cikin zuciyarta! amma ba ta bari abinda take rayawa a ranta yayi tasiri ba, kawai sai dinga nanata innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Tunda take bata ta'ba doguwar tafiya irin wannan ba shiyasa gabad'aya! jikinta ya mutu! ta gaji sosai! sai addua take Allah ya sa su sauka lafiya! ko ta samu ta mi'ke k'afafunta! Matar dake kusa da ita ta bata pure water "Kar'bi ruwa 'yan mata naga kamar kin gaji." Ba ta ji maganarta ba kawai dai ta ga tana mi'ko mata ruwa. Da sauri tasa hannu ta kar'ba ta bud'e baki za tayi magana, ya juyo daga mazauninsa wata muguwar harara ya daka mata fuskarsa a mugun had'e! Sai tayi saurin sunkyar da kanta gabanta na wani irin fad'uwa ta mayarwa da matar ruwan da sauri! jikinta sai rawa yake. Matar ta bi ta da kallon mamaki! sai kuma ta ta'be bakinta ta ajiye ruwanta da fadin."Kin yi wa kanki." A galabaice suka isa abuja! yanda ta fahimta kamar tafi kowa galabaita watakila saboda rashin sabo ne. Ya riga ta fita daga motar yana tsaye yana jiranta ta fito. a gajiye likis ta fito, nan ta ga yanda ya sa bakin gilashi a idonsa tare da rufe kansa da bakar hular sanyi. ta dan tsaya a gefansa tana bin tashar da kallo! ga rana ta k'wallare! jama'a kowa na gabatar da abinda yake gabansa. Hannunta ya ri'ke! ya jata suka nufi wata rumfar kwano gurin wata mai sayar da abinci bayerabiya. cikin harshen turanci suka gaisa kafin ya shedawa matar cewa ga ajiyar yarinya ya kawo mata ta bata abincin da zai isheta anjima zai turo a d'auke ta, wanda zai zo ya d'auke ta sunan Sule." Ta Amsa da "to kafin kalle ta da fad'in." Zo ki zauna." tana nuna mata wata kujera. Gabanta ya dinga duka yana daka! hawaye suka ciko idonta! ita dai ba ta ji abinda suke cewa ba amma ta fahimci kamar barin ta zai yi a gurin ganin yanda matar ke kallonta tana nuna mata gurin zama. Ta ri'ke hannunsa tana girgiza masa kai! wasu zafafan! hawaye suka kufce mata. Saurin d'auke kansa yayi ya cire hannunsa daga nata ya kalli matar da fad'in." Tana da matsalar kunne ba sosai take ji ba." Da kansa ya ja hannunta ya kai ta ya ajiye a kan kujera, fuska a murtuke ya ce" Zan je wani guri ne shiyasa na kawo ki anan na ajiye amma zan turo a dauke ki kada ki damu." Bai jira tace wani abu ba yayi saurin barin gurin ko waiwayenta be yi ba. Duk kyawun abincin bai bata sha'awa ba, gabadaya ma ba ta cikin nutsuwarta, tsoro da fargaba sunyi mata dabaibaiyi, tunani ma ta rasa wane kala za tayi, sa'i da lokaci ta ke share hawaye tana bin tashar da kallo da nazarin wace rayuwa za ta fuskanta a nan gaba. Ekeke matar dake sayar da abincin kenan, ta kalleta a karon da ba zai lissafu ba, domin tun tana lallabata ta ci abincin har ta gaji ta zuba mata ido! sai dai haka kawai take tausaya mata idan ta tuna cewa kurma ce ba ta ji sosai, ta yi tunanin abubuwa da yawa akan yarinyar, ta tunanin mutumin yayi kawalcinta ne domin ya dinga biyan buk'atarsa! Sai daf da magariba Sule ya je domin d'aukarta! Ko kusa ko alama bai gane ta ba ballantana yayi tunanin wani abu, ko da yake can baya da ya je binkice lokacin da abin ya faru duhun dare ya shigo da kuma cikowa ta mutane shine dalili. Su ka gaisa da Ekeke kafin ya sheda mata shine Sule ya zo tafiya da

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});