Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Majanuni Book 3 Complete Hausa Novel 1,212 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kafin a tura maka kudink'a sai da aka sheda min, Yau ka tabbatar da cewa ni din ba 'karamin mutum bane ko?" ya fada cike da izzah da ginshera! Alhaji Sammani ya ce." Wai don Allah ina ka samo wannan mutumin domin daga jin muryarsa bai yi kama da abokanan hurd'ar mu ba." Murmushi yayi kafin ya ce." Haihuwa ce tayi min rana saboda haka mu bar maganar kawai, kai kayi nufin tozarta ni Allah bai nufa, sai ka tura min abinda yayi saura nawa dake hannunka, daga haka ala'karmu ta yanke." Ya na gama maganarsa ya kashe wayar yana jan tsaki, account number ya tura masa yana jiran ya ji alert. Cike da kwarin gwiwa ya fito daga d'akinsa! ya bankad'a labulan dakin yana kiran sunanta. Ba ta amsa ba sai ido kawai da ta zuba masa. Ya ja mugun tsaki kafin ya ce." Na yarda ke ce ki ka karya ni, ba tun yau ba malamina ke sheda min hakan, rabon wad'annan yaran nake zaune dake, amma ki sani, Mariya ta fiye min ke duk da bata raye ina alfahari da ita, domin ta haifa min yarinyar da ta share min hawaye, ba zan ga ji da sheda miki cewa ke da yaranki baku da amfani a guri na ba." Yana gama maganarsa ya saki labulan ya kama hanya yayi ficewarsa zuciyarsa fes! gabadaya duk wani damuwa da lalure-lalure da yake sun tafi sakamakon shigowar kud'i, a maimakon ya je ya mayar wa da dillali kudin ya bashi takardar gidansa, kawai sai ya cigaba da fantamawa da kud'in, ya gwammace ya zauna a matsayin d'an haya a gidan, domin zuwa yayi ya bashi kudin hayar shekara biyu dubu dari biyu da ashirin, yasa abinda ya rage a aljihunsa ya cigaba da buga barikinsa. Baba Asabe tayi-tayi dashi kan cewa a je ayi binkice a can garin nasu amma fafur! ya'ki a lokacin har ya so yayi mata rashin kunya! Kawu Musa ya ce kawai ta kyaleshi kamar yanda ya fad'a mata cewa uwarsa da ubansa ne kawai za su fad'a masa magana ya ji akan wannan al'amari to tunda basa raye babu wanda ya isa domin dai yarinya 'yarsa ce shi yake da iko da ita! Baba Asabe har kuka tayi saboda tsabar 'bacin rai tana jin takaicin abinda mutumin yake mata, wato ita ta gama yi masa wahala yana nuna mata iko. kawai sai ta barwa Allah al'amarin, ta tsananta da addua. 'Bangaran masoyan kuwa sun sha'ku sosai ta waya domin kalaman soyayya suke aikawa da junansu babu dare babu rana. Ranar juma'a 20/3/2021 aka d'aura auran, babu laifi d'aurin auran ya tara mutane, amma duk yawancinsu mutanan Hujaj din ne, sai wakilan ango guda biyu da suka bada sadaki, kuma suka kar'bi auran bisa yarjewar addinin musulunci. [12/10, 9:53 AM] Bintu: 49&50 'Yan Allah ya sanya alhari da 'yan gulma sai shige da fice suke a gidan, ita dai Baba Asabe kallonsu kawai ta keyi saboda ta san mafi akasarinsu, ba alheri ne ya shigo dasu ba, domin da kunnanta ta ji wasu mata suna maganar cewa; ai auran kawai aka d'aura amma babu lefe babu komai, asali ma angon yana da matsalar k'wak'walwa sannan ba shi da wani cikakken asali. ire-iren wannan zantukan jama'a suka ke'be guri guda suna yi. Amarya kuwa sam ba ta sanya damuwar komai a cikin ranta ba, ta na ji ko babu lefe za ta iya zama da masoyinta burinta ya cika za su rayu cikin inuwa d'aya. Kitso akayi mata 'kananu irin na bare-bare sai k'unshin salatif da makociyarsu tayi mata, ta sanya sabuwar atamfa wacce ya kawo mata a din'ke da mayafi da takalmi, Rabi makociyarsu wacce tayi mata k'unshi itace tayi mata kwaliyya dai-dai gwargwado tayi kyau tana ta murmushi, mutane na ta'ba ta suna mata Allah ya sanya alheri. Can gidan Hujaj kuwa Talatu kamar ta zuba ruwa a kasa tasha ganin yanda al'amarin auran ya kasance, babu lefe babu wata hidima da ango yake wa amarya. babban farin cikin ta da ta samun labari cewa ai angon ma bashi da hankali asalinsa mahaukaci ne kawai ya d'an samu sau'ki ne! wannan al'amari yayi mata dadi sosai, kawai sai ta kwantar da hankalinta ta cigaba da sabgoginta, ko gidan bikin ba ta je ba, Jamila ce kawai tayi wanka ta shirya ta tafi. ita da sauran yaran suna gida duk wanda ya shigo sai sun labarta masa abinda yake faruwa. Da magariba Hujaj ya shigo gidan; kalau dashi cikin sabuwar shadda babba riga da 'yar ciki, komai sabo ne a jikinsa sai walwala yake kamar bai ta'ba shiga wani rikici ba. A tsiyace! ta kalleshi kafin ta ce." 'Karya banza da wofi ina zaune labarin komai ya same ni da har kake wani fuffuka kana murna ka dauki 'yarka ka bawa mahaukaci wanda ba a san asalinsa ba." Ya ce." Ai gwara ita akan ke da 'ya'yanki, Talatu daf ki ke da ki bar gidan nan, ki rubuta wannan ki ajiye mutsiyaciya kawai duk kin tsiyata ni, zan dai auro wacce take dai-dai da arziki na." Ta buga cinya da fad'in" Ai wallahi 'karya kake Jamilu, ai na ci gida ko ka sake ni ba zan fita ba ina nan daram dam." Ya ce." Tunda gidan ubanki ne ai sai ki zauna sakarai shashasha! kawai." 'Kwallah ta ciko idonta tana rawar murya ta ce. " Shashasha ba, ai ka santa. A sukwane ya gaura mata mari! wanda sai da ta ga gilmawar taurari! ya nuna ta da yatsa da fadin." Wallahi ki ka sake wata magana a bakin auranki domin dama na ga ji da zama da ke mahaukaciya kawai." D'aki ta shige tana wani irin kuka mai tsuma zuciya! Hadiza tana kwance a kan gado tana danna wayarta, uffan ba tace ba, gabad'aya ma hankalinta yana kan hirar da take da saurayinta. Bayan sallar isha'i Hujaj ya dira a gidan, Baba ta shimfid'a masa tabarma suka gaisa kamar abin arziki. Shahida ta fito ta gaishe shi, ya amsa kafin ya ce ta nemi guri ta zauna. Gurin yayi shuru na minti biyu yayi gyaran murya da fad'in." To Alhamdulillhi, bu'katata ta biya gurin ganin na auran da yarinyar nan a in da ya da ce! wannnan mutumin ya fitar dani kunya saboda haka ko da yana tsince-tsince ne akan bola zan iya bashi auran 'ya ta saboda yayi min abinda ba zan mance ba. Shahida 'ya tace, ni ne ubanta ni nake da iko a kanta, saboda haka babu wani mahalukin da ya isa yace ga yanda zan yi da abinda nake da iko a kansa. Ta ce." Dakata! Jamilu." Ya kalle ta ido cikin ido. Ta cigaba da cewa." Ai na dauka arziki ne ya kawo ka gidan nan ashe rashin kunya ka zo kayi min." Ya ce." A'a ba nufi na kenan ba. Ta ce." Idan ba nufinka kenan ba mai zai sanya ka dunga wasu maganganu masu kama da jirwaye." Ya ce." Surutai nake ji a gari cewa wai na d'auki 'yata na bawa mahaukaci wanda ba a san daga ina ya fito ba, naga dai ni na hai fi abata, kuma wannan maganar nasan daga gidanan ta fito." Ta tsira masa ido kawai tana kallonsa, ya cigaba da cewa."Kamar yanda na

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});