Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Majanuni Book 3 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fa babu ruwan Babanmu shine ma ya ce na tashi na tafi kada dare yayi min." Ta ce." To a ina kika tsaya har goma na dare." Kai tsaye ta ce.'' Ina tare da Baban Baba." Gabanta yayi mummunan fad'uwa!" Baki na rawa ta ce'' Baban-Baba kuma?" Ta amsa da "Eh." tana kokarin tashi tsaye. Ta cigaba da cewa." Ya zo ne saboda ni, kuma mun tattauna maganganu masu muhimmanci! wallahi Baba baki ga yanda rayuwarsa ta sauya ba dama na ce miki ba mahaukaci bane." Baba Asabe jikinta yayi sanyi sosai kawai ta dinga kallonta ta gaza cewa komai, mamaki da al-ajabin al'amarin kawai take. A daran ranar dai da 'kyar Baba ta iya rintsawa tsabar fargaba da tashin hankalin da take ciki na al'amarin yarinyar da wannan mutumin da take zargin wani abu a kansa. Mamakin ta ya kara tsananta lokacin da Shahidan take sheda mata irin maganar da suka tattauna dashi. wato Maganar aure da kuma taimakawa mahaifinta da zai yi." Ta kalle ta da fadin." Shahida anya kina da hankali kuwa.? Kafin tayi magana Saliha ta kyalkyale da dariya da fadin." Ras! take tsabar iskanci ne wallahi! amma Baba ki kyale ta kawai jiki magayi ta je ta aure shi jikinta zai gaya mata." Baban ta girgiza kai da fadin." A'a Saliha ba za ayi haka da ni ba, domin yarinyar nan amana ce a hannuna ban bari ta an aura mata Saminu abbatuwa ba to kuwa ba zan bari ta auri mahaukaci ba." A hankali suke maganar dan kada ta ji." Ta kalle su ranta a masifar 'bace ta ce." Baba na san duk kokarin ki kada nasha wahala a rayuwa! wallahi nayi imani da Allah mutumin nan ba zai azabtar dani ba, yana sona ina sonsa mai zai sanya ki dinga mugun tunani akan al'amarin, ni dai mutukar kina so ki ga farin ciki na to ki amince da abinda nake so kuma ki bini da addu'a. Sai kawai tayi shuru tana kallonta gabadaya jikinta ya mutu ta rasa yanda za tayi ta kamo bakin zaran. [11/25, 10:02 AM] Bintu: pege 43&44 "Ranka ya d'ad'e wannan mutumin da ka sa nayi maka binkice a kansa har ila yau magana d'aya ce kamar dai wancan lokacin; ma'kotansa da jama'ar unguwa ba su ba da kyakykyawar sheda a kansa ba, duk wanda zai bud'e baki yayi magana baya fad'in alherin sa, ranka ya da'de wannan shine labarin da nasa mu a kansa cewa d'an ca-ca ne wasu ma suna zargin yana harkar bariki." Cikin ladabi ya 'karasa maganar da yake tafe da ita. Jaridar dake hannunsa ya ajiye a gefansa, ya mayar da hankalinsa gare shi ya ce." Sule ka tabbatar da Gaskiyar maganar nan? kasan duniya ta lalace mutane basa kunyar sharri! yarda da amincewa ne yasa na sanya ka gudanar min da wannan binkicen, ba naso daga baya wata magana fito." "Ranka ya dad'e hakane wallahi ba za a ta'ba had'a baki dani a cutar da kai ba, duk maganar da na fada gaskiya ne akan Hujaj sai dai ma'kotansa sun bada sheda arziki akan mahaifinsa, sun tabbatar min da cewa shi mutumin kirki ne domin har ya rasu bai ta'ba aikata alfasha ba." Ya ce."To godiya nake Sule za ka iya tafiya." Har ya niyyar tashi sai ya koma ya zauna yana d'an shafa 'keyarsa tare da sinne kai. "Sule Ya akayi ne? da alama akwai magana a bakinka ." 'Dan murmushi yayi ya ce." Ranka ya dad'e na jima ina mamakin al'amarin tun a karon farko da ka sanya ni wannan aikin, sai nake tunanin wani abu, na ce kodai mun kusa samu uwar d'aki ne?" Maganar ta sanya shi dariya ya ce." Sule ai na d'auka za ka bukaci zuwa gida ne domin dubo iyali ashe ba hakan bane.?" Da murmushi a tare dashi ya ce." Da wannan maganar ma Alhaji amma ina bu'katar ka bani wannan amsar idan babu damuwa." Shuru yayi na minti biyu kafin ya ce." Hakane maganar ka Sule, yarinyar mutumin nan nake so na aura insha Allahu." Da walwala a tare dashi ya ce." Ma sha Allah Alhamdulillhi ranka ya d'ade Allah ya sanya alkairi yasa za ayi damu Allah kuma yasa abokiyar arziki ce." Ya amsa da "Ameen suma ameen." Shuru gurun yayi na minti biyu kafin ya ce." Amma Alhaji baka ganin hakan zai janyo maka wata matsalar duba da cewa uban yarinyar bashi da kirki! akwai ma'kiya wad'anda suke jiran 'kiris su samu abun yayatawa a gari." Murmushi yayi ya ce." Sule kada ka damu da hakan, insha Allahu alkairi ne zai biyo bayan al'amarin, ba mu nufi kowa da sharri ba, duk wanda ya nufe mu dashi to babu shakka sharrinsa zai koma kansa." Ya ce." Wannan haka yake fatan alkairi Alhaji tabbas idan hakan ta kasance za mu fi kowa farin ciki." "Ma sha Allah." Abinda ya fada kenan; ya dauki jaridar da ya ajiye ya dan kishingida kan kujerar da yake zaune, ya ce." Ina fatan ka shedawa Labaran cewa bayan sallar la'asar za mu fita." Yana k'o'karin tashi ya ce." Eh Alhaji na sheda masa umarinka tuntuni." To bayan fitar Sule da minti goma kira ya shigo wayarsa. Koda ya ga wanda yake kiran sai ya ajiye ya cigaba da abinda yake. Sai da ta kira sau uku tukkuna ya daga, shuru yayi bai ce mata komai ba. "Daddy ina kwana." ta fada cikin rawar murya. A dakile ya amsa. Sai ta fashe da kuka tana bashi hakuri "Daddy don Allah kayi hakuri ka ji." Gyaran murya yayi babu walwala a tare dashi ya ce." Shukura kin zama mara ji ko? Fatima ta na yi miki hud'ubar banza kina dauka, kamar ni ubanki na baki umarni ki tsallake! ki fita ba tare da izini na ba, har na fita baki dawo ba shin me kike so ki zama?" A sanyaye ta ce." Daddy wallahi ba 'kin bin umarnin ka nayi ba, tsoro nake na fad'a maka gurin da zan je, na san ba zaka bari ba shiyasa na tafi amma ai Hajiya ta sani na fad'a! mata. "Shukura saboda kin san bana tsallake maganar Hajiya shiyasa ki ke had'a ni da ita ko?" "Ba haka bane Daddy." Ya ce." Nayi 'karya kenan." "A'a Daddy ba kayi 'karya ba kawai dai na ga itama Mamana tana da hakki a kaina babu laifi idan na je in da take." Ya ce." Ok to ki tattara kayanki gabad'aya ki koma gurinta kada na dawo na same ki a gidana." Tana kuka take bashi hakuri! Ya ja tsaki! da fad'in." Wallahi kiyi hattara da wannan uwar taki bata da kirki! sannan magana ta dake ta 'karshe shine kiyi gaggawar fito da mijin aure a cikin masu sonki domin ba zan lamunci sakarci ba." Yana gama maganarsa sai ya kashe wayar ya ajiye ransa a 'bace! Shiru tayi da wayar a hannunta tana tunanin abinda zai biyo baya, ta san halin mahaifin ta kaifi daya ne, baya magana biyu, mutum ne shi da bai yarda da shiriri ta ba, ita kuwa a yanzu dai babu wani wanda zata nuna a matsayin wanda za ta aura domin har yanzu ba ta samu wanda yayi dai-dai da rayuwarta ba, tunani mai zurfi ta shiga domin nemo

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});