Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

Mabaraciya Book 2 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

da kus kure tayi ko tana sane tayi ba ,nidai a wurina tozarci ne " to me kikeso ayi ? murmushi Rufaida tayi tace " ta wulakanta ,na nuna mata talaka ba kowa bane " bakida damuwa akan wannan Fatima tafada tare da tabbaci ,kallon mamaki Rufaida tayi mata ,a gajarce tace " kinsan tane? "Bansanta ba amma ,wulakantacciya kamar ta ai bazatayi wuyar gani ba ,kedai kibar komai a hannuna ,namiki alkawari zan kawota har inda kike yanzu bari natafi ,kinga yamma yayi ,gashi dad dina yana a gari, let me have ur contact pls ,mikamata waya Rufaida tayi, alamar seda ita tasaka nata, murmushi kawai Fatima tayi na jinjina isa da takama irinna karamar yarinya kamar ta ,kai wannan da a gidan sarki tazo ai ba'asan kuma mezatayi ba...... Comments nd share Vote and follow me on Wattpad damselfeedo #Real@Bazamfaria *INTELLIGENT* *WRITERS* *ASSOCIATION* (On ward together) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* By *FIDDAUSI* *SANI* (damselfeedorh) 🅿️:9️⃣ ,,,,,,Tana fita gidan ,sai ga Meerah tafito a inda ta la'be cikin satsarfa tace "Fatima ya kukayi ? Hararan ta tayi tace "shiga ki tambayota ,wai ke Meerah duk saboda me ne kike wannan Mirmushi Meerah tayi tace " kedai ki kyauta ta zato akaina ,yanzu kinyi duk abunda nace "ehhh kam kuma nayi mata alkawari zan kawoki a gareta sedai bansan ta ya ba "ta hanyar 'yar aiki Meerah ta tare nunfashinta ,anjima zaki kirata ki tabbatar mata kinsamu address dina ,daga bisani zaki bata shawarar hanya mafi sauki da zata wulakanta ni shine ta 'daukeni aiki ,ke zakiji da komai ,jinjina kai kawai Fatima tayi , tace shikenan duk yanda mukayi zan kiraki a waya yanzu sauri nakeyi na bar motorn Momy a can ,godiya sosai Meerah tayi mata tukuna kowa yakama gabansa Koda Meerah ta koma gida a cikin dakinta ta samu aunty tayi ta gumi da alama tunani takeyi Wuri tasamu ta zauna,cikin sanyi murya tace " Aunty sannu da gida ,bata amsata ba sema fada da ta fara yimata " yanzu saboda Allah Ameerah abunda kikeyi ya dace kenan,kamarki da kananun shekaru ace kina yawo lungu-lungu kamar marar mafadi ,wai duk da sunan daukar fansa ,yakamata ki natsu kisani ke macece me karancin shekaru sannan kuma bakida kowa se Allah shin taya kike tunanin zaki iya ja da Saudah macen da kowa yabon halinta yakeyi na tabbata bakida karfin da zaki dauki fansa akanta ,murmushi Meerah tayi tace "Aunty yanzu fa kika gama fadar banda kowa se Allah,idan ko hakane kinga ni nakeda babban bango domin duk wanda ya dogara da Allah to ya isar masa ,kedai kimun fatan alkhairi,yanzu ma da wani labari nazo miki Kwanan nan zanfara aiki a gidan Yusuf Tsoho ,kuma a matsayin me yiwa 'yar Hajia Saudah hidma ,Aunty zatayi magana Meerah ta tareta da fadin " karkice komai Aunty domin bana fatan Allah yakawo ranar da zanyi musu dake ,nasani akwai risky cikin lamarina ,amma nabarwa Allah komai ya shigemin gaba ,bawai kawai saboda fansar yayata bane aa ceton 'yayan yama'ah da yawa ,wayanda Saudah tayi nasarar lalata rayuwarsu ,idan bahaka ba Allah ne kadai yasan wayanda zata 'bata anan gaba ,bayan ita tana nan ta kebe 'yarta da nufin karta lalace Wlh nayi alkawari kamar yanda tayi sanadiyar lalata 'yaran wasu haka nima se na saka yarinyar ta ta lalace wannan alkawarina ne ,iya mamaki Meerah ta baiwa aunty"to kitafi kici abincinki tun safe bakici komaiba tana gama fada tabar 'dakin Bayan kwana biyu Rufaida tagaji da jiran kiran Fatima gashi bataso ta kirata hakan ze zama kamar raini ne a gareta ,se jujjuya waya takeyi,hakan nan dai ta daure ta danna kira , ringing biyu Fatima ta 'daga shiru Rufaida tayi daga can Fatima tace " hi bab , Rufaida bata amsa ta ba se cewa tayi " I have been waiting for ur call but yuh didn't,are yuh ok? "Yes am ok wlh abubuwane dai suka sha kaina ,sedai nayi iya kokarina naga na kawota gareki but is yet to be possible,but there's only one way ,a wukance Rufaida tace " just go to the point am all ears murmushi Fatima tayi tace "Sunan yarinyar Ameerah iyayenta miskinai ne ,da baran da takeyine take rufa musu asiri tayi yawon neman aiki har tagaji amma bata dace ba "yuh mean she's educated? Rufaida ta katseta "no sorry I mean aikatau irin na gidaje House maid ,ajiyar zuciya Rufaida tayi tace "to wace hanya ce kike nufin inada "kawai 'daukarta aiki zakiyi kinga ta hakane zaki wulakanta ta yanda kikeso,ki nuna mata banbanci da ke tsakanin me kudi da talaka kaskantacce irinta,cikeda gamsuwa Rufaida tace "tnz alot dear, I will talk to my mom ,nasan dai bazata hana ba amma yakamata na fada mata ,bye,bata jira cewar Fatima ma tayi hang-up ta ajiye wayar.... '''''Hajia Saudah da ke zaune tsakiyar wasu mata ,dukannin su babu mai suturar arxiki a jiki,dayar ce tayi mika tare da fadin "nikam wai yau haka zaki barni a gidan nan ,no more enjoy gaskiya da sake tafada tana hararar Hajia Saudah,murmushi tayi mata ta bude baki zatayi magana se ga kiran Rufaida ya shigo wayarta ,ware ido matan sukayi don ganin wata damsel cute tayi appearing a gaban wayar ,da sauri Hajia Saudah ta bar wurin tare da kara wayar a kunnen ta "Mom Rufaidah ta fada a shagwabe ,ajiyar zuciya Saudah ta sauke ,itama cikin tsan tsar kulawa tace " Auta menene ,sake narkewa Rufaidah tayi tace "Mom gaskiya nide zan biyoki niger I have tired been alone ,babu kowa kusa dani and kince baki yarda nayi kawance ba ,kuma gashi Business dinki baya barinki zama tare da ni ta karashe maganar kamar zatayi kuka "Haba one and only ni kaina ko yaushe tunanin ki nakeyi ,shiyasa nake son na gama harhada komai na dawo da kasuwan cina anan gida ,karki damu Dadyn ki yakusa da wowa ,nasan ze rage miki kewa ok? Ta karashe maganar in a wisfer tone . Tabe baki Rufaidah tayi tace " to dama so nake asamamin wata 'yar aiki "ina Sharifa ko ta dena zuwa ne Momy ta tambayeta "nop kawai dai ina ra'ayin wata ne tabata amsa a takaice saboda sam batajin dadin nisan da Hajia Saudah takeyi da ita,kuma da tayi korafi ta nuna tana sonta ,katse mata tunani tayi da fadin "shikenan,bari zanyiwa me kawo masu aiki magana ta samomiki " No Momy na rigada na samu wata ma, kawai dai nakira ki ne saboda kisani ,shiru Hajia Saudah tayi kamar me tunani se kuma tace "shikenan bye take care ,da ga haka ta datse kiran A bangaren kawayen ta kuwa tunda ta fita suka fara musu kowa yana fadin shi za'a mallakawa wannan yarinyar ,dayar ce me suna Hajia Asabe tace ita idan ma ta samu wannan to kawai ciniki zasuyi da Hajia tabata auren ta domin gidan ta zata wuce da ita kai tsaye suna cikin wannan musun ne Hajia Saudah,ta shigo sedai wannan karon fuskarta a hade saboda bata so ma suga damar da zasuyi mata magana "Hajia nace wannan yarinyar zan mallaka miki ko nawane ,domin ki sadaukar min da ita domin da ganinta ,se tayi dadin makin luv ,kinga yarinyar Masha'Allah kirnjin nan tab da shi ga Dan bakinan wallahi har

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34