Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 20

Chapter 20

Mabaraciya Book 2 Complete Hausa Novel 1,176 words 0 views Progress saved
Download Book

kira yasaka Ameerah sauke ajiyar zuciya dan ta fahimci ta firgita ne a tunanin ko itace Yaya Maryam " Hajia Lafiya kuwa " matan suka tambaya "Mama menene kin san ta ne? Itama Rufaidah ta jefa mata tambayar "tunawa da tayi Maryam ai ko a lokacin Babbace kuma an tabbatar mata da mutuwar ta ,se ta sauke ajiyar zuciya a ɓoye tana sai-saita kanta ,batare da ta amsa tambayar da suke yi mata ba ta samu wuri ta zauna " Mama dan Allah menene ,kardai yarinyar nan mayya ce dubi yadda kika firgita daga ganin ta. To ke Ameerah daga ina kuma kuka ɗauko wannan yarinyar daga ganin ta bata da gaskiya ,bare ma daga ganinta irin buzayen nan ne na daji kinsan su da shegen rashin imani kuma akasarinsu mayu ne "haka dai sukeyita suratai ,amma Hajia Sauda bata ce komai ba ,ita kuma Ameerah se warar ido takeyi dan maganar gaskiya yanzu kam a tsorace take. tana tsugune a wurin Mu'aiseen ya shigo ,ɗaya bayan ɗaya yake kallonsu so yake yi ya fahimci abinda ke faruwa amma ya kasa ,zama yayi kan kujera yace " Mama andawo lafiya "cikin sanyin murya ta amsa shi abun yabashi mamaki sosai yanayin yadda yaji muryar ta kamar tana cikin damuwa dan baze iya tuna yaushe ne maganar arziki ya shiga tsakanin su ba ,abun da ya sani dai shine idan ta zo garin ze zo yayi mata sannu da zuwa shima saboda yasan idan be zo din ba ze iya kawo ɓacin rai tsakanin sa da Abba daga ƙarshe ma abun har ya dawo kan Ammi shiyasa yake ɗaukar duk wulaƙancin ta " ita wannan da lafiya take kuka" ya nuna Ameerah " yaya wlh tunanin mukeyi ko mayya ce daga ganin ta Mama ta rikice mana " cikin ko in kula yace " dama ke bakisan ta kika ɗauke ta aiki " yaya a titi fa nagan ta tana gantalin Bara shine na temake ta" batare da ya kalli Meerah ba yace mata "ƙarfe nawa kike tashi daga aikin ? cikin muryata da ta fara dishewa tace " ƙarfe 2 " duba wrist wach dinsa yayi yace " yanzu 2:40 ,hakan na nufin zaki iya tafiya "da sauri ta miƙe "haba yaya ya zaka ce ta tafi bayan bamusani ko da gaske mayyar bace"ganin irin kallon da yayi mata ne yasaka ta yin shiru ,dan batason faɗa yana shiga tsakanin su tunda tanason ya aure ta ,ita dai Meerah da sauri tafita da ga falon dan bata taɓa tunanin zata ga Hajiya Sauda ta firgita haka ba. kallon Rufaidah yayi yace " tun za'aje ake shiri base an dawo ba ,meyasa tun farko bakiyi bincike akan ta kafin ki ɗauke ta ba ,and da ace mayya ce ai ke zata fara cinyewa kafin Mama "haba kaiko ya daga shigowar ka bakasan kan magana ba zaka sallami yarinya ,yanzu idan mayya ce ai gobe ba zata dawo ba "cikin matan da suke zaune ta faɗa " ɗaga mata hannu yayi yace "se kijira goben idan bata dawo ba ,se ku fara nemawa Mama magani "tashi yayi yace " to Mama Allah huta gajiya ,daga haka yabar falon. yana fita suka fara zaginsa "wai Hajia har yanzu shegen yaron nan yana nan da jin kansa ,kiduba yadda yake magana cike da isa se kace shine me gidan " still Hajia Sauda batayi magana ba ,seda Rufaidah ta girgiza ta da karfi " wai Mama menene ko da gaske mayyar ce nifa yarinyar tabani tsoro "se yanzu ta sauke ajiyar zuciya ,cikin son kauda zancen tace " lafiya lau kawai yarinyar tayi min kama da wata ƙawata da ta rasu ne wlh shine fa da na ganta se na tuna da ƙawata ,mutuwar ne ta dawo min sabuwa "ayya Allah ya gafarta mata "suka haɗa baki " Ameen ,zan shiga ciki ina bukatar hutawa zamuyi magana anjima ......... *Kwana biyu nafara* *ƙyiuwar typing kuyi* *haƙuri pls* *Comments and share* Real Bazamfaria ❤️ *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* ( *On* *word* *together* ) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* *By* *FIDDAUSI* *SANI* (damsel feedorh) 🅿️:1️⃣8️⃣ Yau kam jiki babu kuzari Meerah ta shiga ,gida ,ƙarin sayin jikin ta ma da ta samu Yaya Labaran ya dawo ,a tsakar gida ta samesu dan haka ta ɗan zauna suka gaisa ,kafin ta shiga daga ciki Bayan ta wuce ne Yaya Labaran ya kalli Aunty yace " wai Nafisa lafiya Ameerah take kuwa se nake ganin kamar tana cikin damuwa tunda ga yanayin gaisuwar da tayimin zan iya fahimtar hakan ,wai daga ina ma take tun ɗaxu nike tambayar ki se kwana-kwana kikeyimin. Ayya,Yaya na faɗa maka ta je gidan ƙawarta ne kuma ma bata daɗe da fita ba kaikuma ka shigo ,maganar damuwa kuma ,xe iya zama ko yau da gobe ne kasan sha'anin rayuwa ,amma dai lafiya lau muka tashi a gidan nan zan tambaye ta ko akwai abinda yake damunta ne zuwa anjima . Tashi yayi yana saka takalmin sa " to shikenan ni dai zan fita se zuwa dare ko zan dawo dan zan zazzaga ne kinsan na daɗe wanan karon banzo ba tun a mota,su Kabiru suke kirana "adawo lafiya, ka gaishe su Yana fita Aunty ta tashi da sauri kitchen ta shiga ta ɗaukowa Ameerah abincin ta ,a zaune ta sameta tayi tagumi da duka hannunta biyu ,tayi nisa sosai a duniyar tunani,Aunty ta ta bata ,sauke ajiyar zuciya tayi tace " Aunty kece ,zauna mana "ta faɗa tana matsa mata gefen katifar ta ,zama Aunty tayi ,tana kallon ta batace da ita komai ba har tsawon lokaci seda ta gama nazarin ta " Hajia saudah tazo ne? Da sauri ta kalli Aunty cikin mamaki tace " ya akayi kika san haka? Murmushi tayi tace " iya wannan firgicin da kike ciki ya isa sanar dani cewar fuskar Hajiya Sauda ne ya samar dashi a xuciyar ki ,sedai tambaya na anan taya hakan ya faru ,bayan nasan Ameerah bata da tsoro musamman ga abinda ta saka a gaba? . "Hmmm Aunty bazaki gane bane nifa ba ita bace ta saka ni jin tsoro ,kawai dai yadda suke neman maida zancen wani iri Hajiya Sauda ta ganni shine ta firgita ,a tunanin ta ko Yaya Maryam ce ,to shine fa sukace wai sedai idan ni mayya ce taya ma za'a ce daga ganina ta rasa hankalin ta daƙyar Allah ya temakeni ,ɗan ɗan gidan ya shigo ,yace na tafi ,dan na rasa yadda zan wanke kaina ,saboda wlh nima firgicin da ta shiga ya bani mamaki ,dan ba wannan nike so ba nida nikeso na shiga jikinta ,to idan tayi sanyi ² dani ai komai xe lalace min. " Hajia saudah bazata taɓa ganin ki ta kasa tankawa ba ,dakuwa bata ɗauke ido ga yara mata bare ke ,kawai dai yanxu tayi shock ne da ganin ki amma ina tabbatar miki cewar ,kafin gobe tunanin ta ze dawo ke kuma se kisan yadda zakiyi da ita "yawwa Aunty sega yaya ya dawo duk na tsorata yanzu ya za'ayi na rika fita daga gidan nan "Ameerah nima tunanin da nike kenan sema Kinga yadda ya tsareni da tambayar ina kike ,kuma na fahimci kamar be gamsu da cewar da nayi gidan ƙawarki kika je ba,wai yasan baki

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34