Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 25

Chapter 25

Mabaraciya Book 2 Complete Hausa Novel 1,178 words 0 views Progress saved
Download Book

ya dosa titi ba tare da ya tambayeta inda ze kaita ba ,se hakan yasaka ta tunanin shi wane irin mutum ne idan bata manta ba ai Fatima tace yana da kirki sedai ita kam sam bataga wani kirki a tattare da shi ba ,dan haka ta kudurta wa ranta idan zasu kwana su wuni yana shawagin nan bazata buɗe baki ta faɗa inda xe kai ta ba ,sedai idan shine ya tambaye ta ,dan bata sa shi ya ɗauko ta bare yazo yana wani shan kamshi" mtsswww" ta ja tsaki wanda har se da yadan jiyo ya dubeta ,ganin hankalin ta ma yana a wajen motar se bece komai ba ya ci gaba da tafiyar sa, shiru shiru ,har seda taji motar tayi parking da mamaki ta ke kallon wurin da ya tsaya ,tabbas unguwar su ne sedai be shiga lungun ba a bakin titi ya tsaya " to ya akayi yasan unguwar da take, anya kodai dama ya santa ne " idan kingama ƙauyancin zaki iya fita " ya faɗa batare da ya kalleta ba ,buɗe fita tayi daga motar tana magana na kasa-kasa tana hararsa ,da karfi ta rufo masa kofar ,irin wai ita taji haushin nan ,har ta tafi sekuma ta dawo daidai wurin glass ɗin da yake tace " Nagode" tare da turo baki kamar wacce aka yiwa dole,daga haka ta ci gaba da tafiyar ta ,be san sadda murmushi ya suɓuce masa ba ,dan shi al'amuran yarinyar mamaki suke bashi ,wani lokacin tayi kalar muna fukai ,wani lokacin kuma tayi kalar natsuwa yau dai zallar tsiwa yagani a tattare da ita ,shi be masan dalilin da yasa ya ɗaukota a motarsa ba ,koda yake Rumaisa ce ta jajibota zan yi mata warning kuwa ,dan banason yarinya marar kunya. # *hi guys nasan da yawan* *ku* , *kun* *matsu kusan asalin labarin shin wacece Meerah me Hajia Sauda tayi mata da har take da wannan alwashin* ? *Waye* *Mu'aisam? Da shi da Rufee ko akwai aure a tsakanin su? Idan akwai dole akwai wanda ba ɗan gidan ba kenan to waye daga cikinsu? Rufee ko Mu'aisam? Ya kudirin Hajia Laura shin da gaske xatayi nasarar lalata Rufee ko kuwa ,kai guys akwai abubuwa a dunkule yasin😂 it's mistery story kusan haka salona yake 😜 ga duk wanda ya karanta Sahibul ƙalbi, Asalina ,tabbas suma sunzo ne a dunƙule* ❤️ *kude* *kuci gaba da bibibiyata Much luv and endless* *care* ❤️ Follow me on Wattpad@damselfeedo Real Bazamfaria ce ❤️ *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* ( *On* *word* *together* ) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* *By* *FIDDAUSI* *SANI* (damsel feedorh) 🅿️:2️⃣1️⃣ Bayan kwana biyu Rufaidah ta sake samun Hajia Sauda da zancen Mu'aisam,wanannan karon sosai taci mata mutumci ,saboda haka ta yanke shawarar samun Abba da zancen ,a lokacin yana sa shen su Ammi dan haka ta saci jiki ta same shi ,yana gishin giɗe tayi sallama ,amsawa yayi yana tashi zaune " a'a Rufaidah kece cikin daren nan? " Ehhh Abba barka da dare "wuri ta samu ta zauna tace "Abba, dama.." se kuma tayi shiru ta kasa faɗa ,tattara hankalin sa yayi kanta dan yasan tunda yaganta haka to maganar me muhimmanci ce " come on Rufaidah menene? ina fatan dai ba wani matsalar bane " Abba dan Allah ka temaka min wlh ina matuƙar son Yaya Mu'aisam nide bazan iya auren wani ba sedai na zauna bazanyi aure ba" ta ƙara sa kamar xatayi kuka " shiru Abba yayi ,dan gaskiya ba ita ya so aurawa Mu'aisam ba ,sedai babu komai tunda Allah yasa beriga ya furta wa kowa ba and dukan su ƴaƴan sane "ashsha saboda kina son yayanki shine duk kika zama wata iri haka? Ko shine yace baya sonki?". A'a.Abba Mama ce tace bazata bari na aure sa ba wai ita tana da wanda take so na aura ,dan Allah Abba katemakeni ,kasan halin Mama, bansan me yasa bata so na' auri Yaya ba " karki damu Rufaidah,ni nasan ta inda zan ɓullo mata kisaki ranki ,aure kamar kin auri Mu'aisam ne kinji ,banason kisa damuwa a ranki ,jeki kwanta " to Abba nagode Allah ya ƙara girma ,seda safe " har takai ƙofar fita se ta dawo ,kallon ta yayi yace " wani abunne? dama Abba banaso kafaɗawa Mama nice naxo" murmushi yayi mata " karki damu kedai ki saki ranki ita ai bata isa ta hana abinda nayi niyya ba ,shiɗin ɗan uwanki ne dan haka ita bata isa ta rabaku ba" "cikin jin daɗi tace " to Abba Nagode sosai Allah yaƙara girma". Bayan kwana biyu Abba ya tara duka iyalan sa ,duda seda aka kai ruwa rana kafin Hajia Sauda ta yarda ta sameshi a sashen Ammi ,se wani harare² take Mu'aisam ne ya buɗe musu taro da addu'a ,kafin Abba ya fara magana " maƙasudin taraku anan ,ba wani abu bane face saboda ke Rufaidah da kuma Rumaisa ,duk abinda yakamata nayi muku nayi to gaskiya yanzu so nike na aurar daku na huta naji da su Mimi" wannan abun da yafaɗa yaƙara ƙona zuciyar Saudah " dan haka idan kuna da wanda kukeso ku sanar dani, dan banaso nayanke hukunci kuga kamar banyi muku adalci ba ,ke Rufaidah dake zan fara shin kinada wanda kikeso ne? Ɗago kai tayi ta kalli Hajia Sauda,aiko tayi mata wani kallo me haɗe da gargaɗi ,wanda duk a idon Abba ne ,da sauri ta duƙar da kanta kasa cikin rawar murya tace " a'a Abba ni babu wanda nikso " girgiza kai kawai yayi yana maida akalar tambayar sa akan Rumaisa " Abba kasan ni ban rigada na kammala karatuna ba " Rumaisa aure ai baze hanaki karatu ba , sedai idan kince bakida wanda kike so a yanzu to wannan kam ,zanyi miki uxuri saboda karatun amma kitabbatar kafin ki kammala kun shirya kanku da wani ,idan ba haka ba ni zan zaɓa miki kamar yadda zanyiwa ƴan'uwanki a yanzu . Mu'aisam ,nasani kai yaro ne me biyayya,dan haka nayi shishigi a cikin rayuwar ka ban sani ba ko zakayi farin ciki da hakan ,na yarda da tarbiyyar ka Mu'aisam ,a kwai kuma dalilan da yasa nayi maka wannan zaɓin ,iya sani na dakai ,na sha tambayar Ammin ku ko kana da wacce kake so amma dai amsar ɗaya ce babu shekarun ka se ƙara ja sukeyi amma sam kai babu tunanin auren a ranka ,Amminku itama ta saka ma ido ,saboda haka ga kanwar ka Rufaidah nan ,nabaka ita kuma banason auren ya wuce sati 3 masu zuwa ,ina fatan zakuyi min biyayya ku rike junanku amana. duka mutanen Uku a firgice suka kalli Abba ,Ammi ,Hajia Sauda,da kuma uban gayya Mu'aisam,da yaji zuwan maganar a bazata ,meyasa Abba xe zaɓa masa Rufaidah bayan duka halayyar ta babu me burge shi? innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,kawai yake maimaita wa cikin zuciyar sa ,dan har wata zufar wahala yaji tana titsatso masa "Wlh Alh baka isa kayi kyautar ƴata a wurin da ba'a son ta ba kuma na barka , taya ma ka rasa wanda zaka zaɓa mata se waƴanda kasan cewar ba ƙaunar mu suke ba ,idan har yazama dole ne se kayi haɗin naga akwai mace a ɗakinsu meyasa baka bashi ba ,ok se tawa " yar ko to idan ma

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34