Chapter 33
Chapter 33
Allah ki rarrashe xuciyarki , Rufaida ,ga yaron Hajia Sa'a wlh yafi Mu'aisam komai idan ma baki son shi ,to ki fitar da wanda kikeso mana amma dai ba Mu'aisam ba . da kyau Rufaidah take kallon ta dan son yiwa kalamanta fashin baƙi shin mene ne to tsakanin ta da Mu'aisam bayan rashin son shi da ta san batayi? "Shikennan Mama ni zan tafi se na dawo " ganin kamar Rufee tafara karyowa ne se Hajia saudah tayi mata murmushin yaƙe tace " kidawo lafiya ,me za'a dafa Miki kafin kidawo? Ko jiyowa batayi ba tace " komai ma"..... Comments and share Real Bazamfaria ce ❤️ *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* ( *On* *word* *together* ) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* *By* *FIDDAUSI* *SANI* (damsel feedorh) 🅿️:2️⃣5️⃣ Bayan kwana biyu Mu'aisam yana zaune falo yana kallon labarai , sega Rufee ta shigo , cikin takunta irin na yanmata masu ji da kansu, banda tashin kanshi babu abunda jikinta keyi , kujerar da ke kallon tasa ta zauna , cikin muryarta me hade da yanga tace " barka da hutawa Yaya" ta gefen ido ya kalleta kafin ya amsata da " yawwa " duk da yanayin kwalliyarta ya burgeshi musamman kanshin jikinta Wanda tunda ta shigo falon ya sauya , shi mutum ne da yakeson mace me kwalliya da kamshi , kuma duk Rufee ta hada su sedai baya jin ze iya sonta kodan sabotada uwarta , ganin shirun yayi yawa se tace " am Yaya dama cewa nayi ko zaka kaini shopping idan baka komai " Me ya samu motarki da bazaki fita ke daya ba? Ya tambayeta yana tsareta da ido " haba Yaya yanzu dan Inada mota shine bazaka kaini ba , naga a gidan nan duk wanda ze fita kaine kake kaishi , se nice bazaka kaini ba , wai Yaya me nayi maka kake min haka naga nida su Rumaisa duk dayane koma nace nafisu tunda ni yanzu akwai maganar aure a tsakanin mu me yarage nan da 2 weeks fa shikenan " cikeda kosawa da maganarta yace " wayanda kike ganin ina fita dasu basuda mota ne kekuma yar gata ce ina yaran gidan nan ke kadai ce kikeda mota , kuma kidena tunanin wai zakifi wasu gareni , dukan ku kannena ne babu wani abu bayan wannan " Suna cikin maganar ne Rumaisa ta shigo da alama dawowar ta kenan daga school, ganin su zaune a falon se batayi kokarin zama ba tana gaishe da Mu'aisam tayi gaba abunta , seda ta shiga dakin ne ta tuna da tambayar da takeso tayiwa Rufee saboda haka ta fito , suna nan zaune kamar yadda ta barsu , sedai wannan karon Mu'aisam yana cewa Rufee " tajira idan anyi sallar la'sar se yakaita , murmushin samun nasara tayi har zatayi magana se kuma tayi shiru ganin Rumaisa tana nufosu Kusa da ita taje ta zauna tace " nikam sis Rufee na manta kwana biyu na dena ganin Ameerah a gidan nan Allah dai yasa kafiya " ya mutsa fuska tayi tace " waye kuma haka?". "wata yarinya da takeyi miki aiki ,kamar dai bata daɗe da fara aiki a gidan nan ba ai tanada kirki wlh ,nima ban kula da rashin ganinta ba se jiya ne naga auta tana da kumburi da na tambayeta menene shine tace wai taje part din Mama neman Auntyn ta amma bata ganta ba ,to yau da safe ma ta shiga wai bata ganta ba ,kinsan Auta tuni ta maƙale Aunty Meerah dai "haɗe fuska Rufee tayi taja dogon tsaki,dukansu kallon ta sukayi dan basu san dalilin tsakin ba ,ganin irin kallon da Mu'aisam keyi mata ne yasaka ta wayancewa da faɗin " kedai Rumaisa akwai ki da shirme ,duk akan *Mabaraciya* kike wannan rattafen ,ina zan san inda take ,wataƙil ko sun gama magana da Mama ne dan kamar naji tace wai da ita zata koma ,tunda Kinga m zamana takeyi kuma yanzu aure zanyi so babu kowa a gidan dan haka zata tafi da ita,nifa banma yarda da yarinyar ba " da sauri Mu'aisam ya kalleta har ya manta ma da badashi suke maganar ba se samun kansa yayi da tambayar " meyasa Mama zata tafi da ita ,ina ga kawai ku sallame ta ,dan ba ma lallai bane iyayen ta su amince a bar garin nan da ita ba " to kai Yaya miye naka ,kasan dai talakawan nan yadda suke bare ma su da suke neman kai da ita suna ganin kudi da gudu zasu amince ,ni bama zanso hakan ta faru ba kasan fa duk yaran da Mama take ɗauka tana sakasu school ne cikin lokaci zaka sun waye ,nikuma bazan so hakan ya faru akan wannan ba "Mu'aisam bece komai ba yaci gaba da kallon sa ,saboda zuciyarsa da ta tafi dogon nazari na dalilin da zesa Meerah tabar kedi Cikeda Mamaki Rumaisa tace " aikam dai Ameerah tana da kirki sis Rufee bansani ba dai ko kece baki fahimci hakan ba ,ni damuwa ta ma kar ace ko batada lafiya ne ,gashi ban tambayeta gidan su ba bare naje na duba ta ,dan ko Ammi ta damu da rashin zuwan nata" Allah wadaran naka ya lalace ,kice kune kuke sakar mata fuska shiyasa har take tunanin kawomin raini ,yanzu idan ba neman suna ba ne xe kaikimu wurinsu ,koda nasan ma ba samunta xakuyi ba dan na fi tunanin a bakin hanya seke kwana itada iyayen ta so don't bother ur self" jeki ki shirya yanzu idan nadawo sallah zamu fita da Rufaidah se mutafi dukan mu harda Auta ma kishirya ta " ba tare da dukan su sun san me yake nufi da hakan ba ,suka amsa da to " duk da kasan zuciyar Rufee ba haka taso ba ,taso ne Sufita su kaɗai saboda su fara samun kusanci da juna ,akwai kuma maganar da take so suyi ,wanda tasan matuƙar suka fita waƴan nan jarababbun to ba sake wa zasuyi ba ,bata so ta koma sashen su dan kar Mama ta gane cewar zasu fita da Mu'aisam dan haka tayi zaman ta anan , toilet din da kecikin falon Rumaisa ta shiga ta ɗauro alwala ,da tafito ta kalli Rufee da take canja channel tace " sis Rufee ko zakiyi alwala ne akwai ruwa a cikin toilet "batare da ta kalli Rumaisa dake maganar ba tace " am off salat" taɓe baki Rumaisa tayi tana shigewa bedroom. cikin doguwar Riga ta shirya tayi kyau sosai fitowar ta yasaka Rufee kallon ta batadai ce komai ba itama Rumaisa batayi mata magana ba ,ta shiga ɗakin Ammi lokacin ta sameta tana sallah saboda haka direct kan gado ta nufa dan tashin Nawwara dake bacci ,bubbuga bayan ta tafara, kasancewar batada nauyin bacci se gashi ta budé ido ,tana ganin Rumaisa tafara narke fuska kamar zatayi kuka tace " Yaya baccin be isheni ba " ok bara mutafi mu barki to dama Yaya yace natashe ki zamu fita shopping" ai tana jin zancen yawo se ta tashi da sauri ,tana faɗin " to mutafi" hararan ta Rumaisa tayi tace " kinyi sallah ne da zaki ce mutafi kuma kinsan baxaki bimu a haka ba ko? Nawwara batayi magana ba ta shiga toilet da sauri alwala tayo ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34