Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 21

Chapter 21

Mabaraciya Book 2 Complete Hausa Novel 1,187 words 0 views Progress saved
Download Book

damu da zuwa gidan kowa ba " akwai matsala kenan Aunty " karki damu Insha'Allah zamusan yadda zamu tsara sa ,kici gaba da tafiya ba tare da yagane ba ko ? da sauri Meerah tace " me kike tunanin samu sanar masa ya yarda kinfa san halin yaya ,akwai saukin kai kam amma ,a irin wannan baya sanya ,ni wlh nafara jin na sare akan lamarin nan Aunty " badai nice nace kibarni dashi ba to ai nasan me zan faɗa masa kedai kiyi ƙoƙarin cire damuwar nan a fuskan ki saboda kar ya sake zargin wani abun. "to shikenan Aunty Insha'Allah bama ze gane komai ba Rufaidah# da dare Hajia saudah na shirin tafiya ɗakin Abba ,kasan cewar yanada ɗaki a kowane party ,kuma taji shigowar sa tun ɗazu dan haka take shirin tafiya ,seda takammala komai kafin Rufee tace "am Mama wurin Abba zakije? Kallon ta Hajia saudah tayi tace "ko akwai damuwa da hakan ne" a'a Mama kawai dai naso mu ɗanyi magana ne "ta faɗa tana sosa kai ,dawo wa Hajia saudah tayi ta zauna ta ce " ina jinki "Mama dama da baki nan ne Abba yakemin magana akan aure ..."se kuma tayi shiru " go on ina jinki ,kinada wanda kike so kenan?Ehhh Mama sedai yadda naga Abba ya nuna tare yakeso ya aurar dani da Rumaisa ne abun beyimun ba , kinyi alƙawarin idan na tashi aure za'ayi bikin da ba'a taɓa yinsa ba a garin nan ,to me yasa zece wai ayi tare da su salon munafurci ne kawai Mama wlh sekinga irin abubuwan da sukayimin da ba ki nan ,Abba ma se faɗa yakemin ,wai inada baƙin hali " ajiye zancan su a gefe maganar haɗa bikin ne dai ko ni bazan lamunta ba to hala itama ta samu me so ne? Taɓe baki Rumaisa tayi tace "ni ina zan sani kinsan ba shiga sabgar su nikeyi ba " washe baki Hajia saudah tayi tace " to ke wa kika samo mana ,danfa har munso mu haɗaku aure keda yaron Hajia Sa'a"ashe Allah ya tsare dai ban amsa ta kai tsaye ba nace se na tuntuɓe ki ,ashe ma ke kinada wanda kike so ,to waye kuma ɗan waye?". "Haba Mama waye kuwa idan ba Ya Mu'aiseen ba ,ina kinsan da wannan zancen da daɗewa "ashe baki da hankali Rufaidah ban sani ba me zakiyi da wannan shegen yaron ,da baya son uwarki baya ƙaunar ta ,ban taɓa samun matsala da Alh ba se a dalilin sa to idan ma mafalki kikeyi ki falka dan bazan taɓa goyon bayan wannan sakarcin ba ,na faɗa miki,tun wuri kisake tunani kisamu wanda ya dace dake ,ko kuma ki amince da Anwar ɗan wurin Hajia Sa'a dan ko babu abinda ake nema ga namiji wanda baya dashi ,kyakkawa ne ajin farko na tabbata idan kika ganshi zasan yafi wancen sakaran komai ,sune suke da kuɗi ,mulki ke komai na da kika sani na rayuwa Allah ya basu ,rashin amsa mata da banyi ba bawai yana nufin dan bazan basu bane , a'a nayi hakan ne saboda na nema miki daraja ,kina lokacin da zaki fitar da wani mijin daban amma wlh idan kikayi wasa zansa Alh ya aura miki Anwar koda bakya son sa"tana gama faɗa ta bar dakin dan bata son Rufee ta karya mata zuciya wannan ihun na na ƙarfin haline ,Allah kaɗai yasan irin son da takeyiwa wa Rufaidah amma batajin hakan zesa ta yarda ta auri wani sakarai wai Mu'aisam Mutuwar zaune Rufaidah tayi dan bata taɓa tunanin zuwan ranar da zatace tana son abu Mama tace a'a ba ,a iya saninta duk abinda takeso shi Mama keyi koda kuwa hakan be gamshe ta ba "kai wasa Mama take wata ƙila dai saboda bata cikin kwanciyar hankali ne shiyasa tayi mata hakan dan ta kula tun abinda ya faru ɗazu har yanzu bata dawo dai² ba ,kema Rufee meyasa zakiyi mata wannan maganar bayan kinsan bata cikin natsuwa"duk zuciyar ce ke faɗa mata wanann ,kuma ta yarda da hakan ,dan haka bata wani damu ba ,takoma ɗakinta tayi kwanciyar ta ,se kuma abinda ya faru tsakanin Hajia saudah da Meerah ya dawo mata ,abun ya matuƙar bata mamaki ganin irin firgicin da dukansu suka shiga anya basun san juna bane ? "Kai ina ma Mama zata san wannan matsiyatan tun da ta san babu wani alaka ma da ze iya shiga tsakanin su ,to ko de mayyar ce? Idan kuma hakane da gaskiyar Ya Mu'aisam da itace zata fara cinyewa ,amma dai bara tagani wlh idan har gobe Mama bata dawo hayyacin ta ba to se tasaka an kama Meerah kai ba itaba ma har shegun iyayen ta "da wannan saƙe-saƙen har bacci ya ɗauke ta . Meerah# da wuri tagama shirinta ,bayan tagama aikin gida kamar yadda ta saba ko wace safiya bata fita se ta ragewa Aunty aiki ,dawo wa tayi ta zauna tana jiran fitowar Aunty saboda tanaso taji ya sukayi da Yaya, ya amince ko kuwa ,ganin lokaci yana ƙure mata ,se duba agogon wayarta takeyi ,daga ƙarshe dai ta yanke shawarar zuwa ɗakin su ta duba su ,a bakin kofa sukaci karo da Aunty , murmushi sukayiwa juna suna shigowa ɗakin "nasan ko wani bacci bakiyi ba ko kina tunanin ko Yaya ya amince ko a'a"wlh kuwa Aunty ,inajin tsoron yaki amince wa ,kinsan wanann mijin naki se ke "dariya tayi tace aikuwa dai dan gashi na tsara sa ya amince harda baki kuɗin abun hawa "kai Aunty da gaske nikam ne kika faɗa masa haka? Banyi tunanin ze amince cikin sauƙi ba " Meerah kenan duk yadda kike tunanin Namiji ,to ba komai bane a gaban matar sa sedai idan ita ɗin batasan kimarta ba ,bayan ya dawo ne dai yaganni kamar ina cikin damuwa ,shinefa yaketa tambayar menene ,nace masa babu komai ,dana ga ya damu kansa shine nace " wlh Yaya wani ,karambani nayi ,se yanzu ne nake nadamar yinsa batare da na ji ta bakin ka ba ,inajin tsoro bansan tata zaka ɗauki al'amarin ba ,wato gani nayi Ameerah ko yaushe tana zaune a gida ita ba karatu ba kuma ba sana'a ba ,se zaman banza shi ne ,ranar da naje gidan ƙawata na sameta tana koyar da yara dinki ,se nayi sha'awar itama Meerah ta koya ,nasan gaba zeyi mata anfani a rayuwar ta ,to shine fa take zuwa kullum da safe zuwa karfe 2 ta dawo jiya ma da kadawo baka sameta ba tana can ne ,naji tsoron na sanar dakai ne ,saboda bansan ya zaka ɗauki zancen ba ,amma dai dan Allah kayi haƙuri ,karkace zata dakata da zuwa" Shiru yayi ,yana saurare ,kafin ya ja dogon nunfashi yace " Haba Nafisa wanann ai abun karuwa ne menene na ɓiyemin kuma ,bawai zan hana ta bane ,amma baki ganin illa a cikin sammakon da takeyi tana fita sanin kanki ne se tayi tafiya kafin ko zata samu abun hawa ,banason wani abu ya sameta kamar yadda ya samu Maryam " Insha'Allah Yaya babu abinda ze faru se Alkhairi kaaide kayi mana fatan nasara " to shikennan Allah ya temaka yabada abinda ake nema" kinji fa yadda muka yi dashi ,har tabada kuɗin abun hawa". Rungume ta Meerah tayi

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34