Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

Mabaraciya Book 2 Complete Hausa Novel 1,188 words 0 views Progress saved
Download Book

yimiki ba ,ni da zaki bi nawa ma da kinbar mata shi can su karata ,amma ina mamakin me wanan Alh yake da kike masa wannan son har kike ɓoyemana saninsa ,ko kina tunanin zamu iya kwace Miki shine,kinsani dai ni Namiji baya gabana ,idan ko kikaga nabashi kaina to inada bukatar wani abunne" Murmushi Hajia saudah tayi tace " komai zan faɗa baza ku gane ba mijina ba kamar sauran mazan bane shidin na dabanne ,ni ce nasan kan abuna ,saboda haka kudena ma tunanin wai zan barshi ,a'a ko ba komai auren ma wani kariya ne a tunanin ku idan da banda aure waye ze yarda da zaman nan da Nike ai dole za'a zargeni ,amma da yake Alh wayayyen mutun ne rayuwar sa irin na turawa baya tauyewa mutum hakkinsa tunda na faɗa masa dalilin zamana anan shikennan ya yarda so kudena wanna maganar ,jibi zan tafi amma bazanfi sati ɗaya ba dan a wannan karon inaso na shiga kauye saboda na samo mana yaran da suka dace" da harara suka bita a kaikaice ,saboda sunajin haushin yadda take nuna mijinta yafi kowa, bayan wasu daga cikinsu a ta dalilinta suka rasa nasu auren........ Follow me on wattpad@damselfeedo Real Bazamfaria❤️ *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* ( *On* *word* *together* ) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* *By* *FIDDAUSI* *SANI* (damsel feedorh) 🅿️:1️⃣4️⃣ Ameerah# A ƙofar gidansu ta tarad da wata haɗaɗdiyar motor tayi parking,da kallo takebin motar Kasan cewar baƙin galass ne bata iya ganin wanda yake ciki ,sedai a zuciyarta tana mamakin wanda yayi kasadar shigowa da mota lungun su dan ta tabbata se yasha wuya kafin yafita ,idan ma beyi Sa'a ba yaran unguwar zasu zane masa mota ,janye idon ta daga motar tayi tanufi shiga cikin gidan su " Ameerah" ta tsinkayi ankirata da wani calm voice ,faɗuwa taji gabanta yayi batasan dalili ba , addu'a tayi tana jiyowa dan ganin wanda ya kirata ,jiyowanta yayi dai² da isowarshi inda take ,dan zare ido tayi ganin kamar ta ganeshi ,shine mutumin nan da yataɓa neman ta shiga motan shi " Kinyi mamakin ganina ko? ai nafi 2 hours a wurin nan ina jiran dawowar ki saboda na fahimci kamar bakison magana a titi ,any way sunana Muhsin ni managern banki ne ,inada mata da yara biyu kuma gaskiya a da banda ra'ayin karin aure saboda gwargwado matata tana kula dani amma tunda na ganki naji na kamu da sonki ,shiyasa ranar da kika ƙi yarda nakawo kiga se nabiyo bayanki har seda naga unguwar da kike ,fatan zan samu karɓuwa a gareki"ya ƙara sa yana kafeta da ido. Kamar yadda yake kallon ta ita ma kallon sa takeyi ,dan sosai yabata mamaki,koda bata taɓa soyayya ba amma bata tunanin haka tsarin yake ,daga ganinta bema nemi izinin ta saurare shi ba kawai ya saki baki se zuba yake ,koda ace tanada ra'ayin soyaya ma yanayin tsarin sa beyi mata ba " ke nike saurare ranki ya daɗe " murmushi tayi wanda ya kasance kamar halayyarta ne yawan yinsa ,cikin sanyin murya ita ma tace " kayi haƙuri baza'a barni nayi soyayya a yanzu ba" tana faɗa masa bata jira jin me zece ba kawai tayi shigewarta gida kasancewar dama a bakin zauren gidan suke. Murmushi Muhsin yayi dan ze iya cewa ya hango alamun nasara dan ya fahimci yarinyar xatayi sauƙin kai,bin gidansu yayi da ido a ranshi yace "tabbas masu kyau na irin wuraren nan wanda talauci ya boye a gansu bare har a ga kyansu yanzu wannan da ace gidan masu kuɗi take aikam da se irin yaran masu kuɗi nan zata aura" matarshi ya koma se gashi yafito da wata leda a hannunsa irin na shopping dinnan ,duk da dai kayan ciki kamar bamasu yawa bane saboda ledan ba wata babba bace ,waige² yafarayi dan neman yaron da ze aika,cikin Sa'a ko ya ga wani yaro ya fito daga wani gida kiran yaron yayi ya basa ledar yace " shiga ka kaiwa Ameerah kaji" Koda Ameerah ta shiga gidan ta same Aunty zaune kan tabarma daga dan jikin kitchen ɗin su inda inuwa tafara kaiwa ,a gajiya ta zube itama tana faɗin "wash "sannu kin gaji ko" wlh kuwa Aunty nagaji ga yau garin ana rana ,yunwa ma nikeji me kika dafa mana? "Bansani ba haka kawai kina wahalar da kanki, ni tsoron da nikeji ma kar se yayanki ya dawo ya ce baxaki ci gaba ba" toro baki tayi tace nide Aunty kibani abinci naci kinji " tashi tayi ta dauko mata abincin harda pure water me sanyi ta kawo mata "tnx Aunty na uwar gidan yaya ,idan dai kikaci gaba damin irin wannan ai zan hana yayana ya karo aure " au Meerah kice da har yana tunanin ƙarin aure anya yarinyar nan ba wani shirin kikeyi dashi ba? hhhhh Aunty kenan kema kinsan ai daga ke ba ƙari"dariya itama Aunty tayi tace " Meerah aishi ƙarin aure ƙaddara ne bare ma ni dinnan idan na hana yayanki yaƙara aure ai banyi masa adalci ba ,tunda dai kingani ni ba haihuwa nikeyi ba ko a haka yayimin halacci duk da nasan yana buƙatar yara amma yana ƙoƙarin ɓoyemin" ajiye cibin da ke hannun ta tayi ,tace " haba Aunty kinsanfa likitoci sun tabbatar da lafiyan ku lau ku duka kawai dai lokacine beyi wa ,wani rabon a nesa yake , Insha'Allah very soon zaki haifa mana babies karki just we shall keep on praying" ganin kamar Meerah ta damu ne se Aunty tayi Murmushi tace " karki damu Meerah kinji ,ɗazu ma anzo neman ki ,wai wani ko wa nade manta sunan da yaron ya faɗa nace bakinan ,hala ko na samu surikine" tafaɗa cikin zolaya ,rufe ido Meerah tayi ,kafin tayi magana ma se ga yaron da Muhsin ya aiko ya shigo Meerah ya mikawa ledar yace "Aunty wai gashi inji wani me mota " kasan cewar duk yaran unguwar da haka suke kiranta dan duk ranar Thursday nd Friday tana tarasu tayi musu lesson ,shiyasa dukansu suke sonta saboda tana da son yara Da ido suke binsa daga ita har aunty. Ganin ita batada niyyar karɓa ,se Aunty ta karɓa tace " kace ta gode" Ajiye ledar Aunty tayi batare da ta buɗe ba ,tace " wai Meerah ba yunwa kikace kinaji ba se wasa kikeyi da abincin idan baxaki ci ba ai da rufewa kikayi" batace komai ba ta ci gaba da tsakurar abincin dan neman yunwar da takeji tayi ta rasa tunani take waye Muhsin kuma menene dalilinsa nayi mata haka ,ok ko yayi ne saboda ya dauka ita maƙwaɗaiciya ce ,abun hannun sa zesa ta so shi " kayi a banza dan bazan taɓa son ka ba " kideyi a hankali bakinsa gaba ba wataƙil zaki iya son sa" seda taji maganar aunty ne sannan ta gane cewar a fili ta faɗi maganar ,rufe abincin dake gaban ta tayi tace " Aunty wlh fa ni ban san shi ba bansa wanda ya nuna masa gidan nan ba ,kuma saboda beda kunya wai har yake faɗa min yana sona ,ni me zanyi da wanda yakeda mata? Dariya Aunty tayi tace ,kice saboda matar sa kike kishi to ke miye naki tunda yasan yanada matar kuma yace yana sonki,idan dai

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34