Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

Mabaraciya Book 2 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

so ta sake haɗuwa da Rufee har ta bar gidan ,a zaune ta sameta tana ninkin kaya da alama daga shanya ta kwaso su ,ganin yadda Larai ke binta da ido ne yasa tayi murmushi,tana yiwa kanta mazauni tare da faɗin " Aunty har kingama aikin kema? Ganin Larai batace komai bane yasaka ta faɗin " lafiya dai? Ajiyar zuciya ta sauke tace " Kinkuwa san ganganci da kika yiwa kanki bana tunanin zaki ci gaba da aiki gidan nan ,dan wlh kinci Sa'a Hajia bata nan da se ta saka an wulaƙantaki tukuna ta koreki ,saboda tana matuƙar son Hajia Rufaidah,Sam batason ɓacin ranta amma naga kin dage kina mayar mata da magana yau ba ke ba harni nasan se ɓacin rai ya shefeni dan a fusace tafita gidan nan " ayya Aunty to miye lefina itace fa ta buƙaci na bata amsa ,shine ni kuma ba bata " cab! amma dai bakisan wacece ita ba ko? gyara zama Meerah tayi cike da rashin damuwa tace " yawwa faɗa min ko ita ɗin wacece Kinga se na kiyaye gaba" Rufaidah da kike gani su biyu ne a wurin Hajia saudah yayarta tayi aure shekara biyu kenan da suka wuce ,kaf a duniyar nan bana tunanin akwai abinda Hajia saudah keso fiye da Rufaidah, duk kuɗin da kikejin ana faɗar me gidan nan yana dasu to Hajia ta fishi saboda ita ɗin irin matan nan ne da basu dogara da dukiyar miji ba sosai take neman nata gashi tana te mako sosai shiyasa takeda jama'a don kuwa idan taxo garin nan zakiga ko yaushe gidan cike da jama'a sedai tanada isa ita ma kamar yadda kika ga Rufaidah banbanci shine ita bata wulaƙanta talaka amma kuma a gabanta Rufee xatayi wulaƙancin bata cewa komai bansani ba ko saboda son da takeyi mata ne Da ido kawai Meerah take bin Larai ganin yadda take yabon kirkin Sauda , murmushi tayi tace " Allah sarki kice ita tana da kirki ni har najima da tana nan kila da zamu ɗan fi samun alkhairi ko" sosai kuwa gaskiya tana da Alkhairi base kuɗin aikin ka take baka ba kuma idan zata koma haka zata baka kuɗi da yawa tace kayi mata addu'a" cike da jin daɗin labarin Larai Meerah tace " to wai ita wane irin business takeyi haka?shiru Larai tayi kamar me tunani zuwa can tace "to gaskiya dai ban sani ba ,amma dai ko wane irin business ne nasan babbane kam shiyasa bata iya zama anan ,mijinta yayi har ya gaji mafi yawancin lokaci ma idan Kinga tazo to tana neman masu tayata raba kayanne dan tana ƙorafin ma'aikata sunyi mata kaɗan ,saboda hidimar raba kaya wai idan sun iso ,shiyasa ma kike ganin bata aje masu aiki anan da yawa da tazo taga me aiki se tace zata tafi da ita can wai acan tafi bukatar su ,saboda jigila"kiran da Rufaidah ta ƙwallowa Larai ne yasakata tashi da sauri dan amsa kiran.ajiyar zuciya Meerah ta sauke "kenan idan ina zama da Larai zan ƙara fahimtar wasu abubuwan ,lalai Hajia saudah ta cika shu'umar mace ,wato ta killace ta ta yar a gida tana kai ƴaƴan wasu....... Akwana a tashi babu wuya ,yau ga shi Meerah ta kai tsawon sati biyu da fara aiki a ƙarƙashin Rufaidah,babu abinda yake bata mamaki kamar ganin yadda Rufee ta fita harkarta ,sam bata shiga sha'anin ta ,duk da hakan yayi mata daɗi ,amma kuma wani ɓangare na xuciyarta yanaso ko da rashin mutuncin ne yariƙa shiga tsakanin su ,domin tana kallon illa da yawa a rayuwar Rufaidah ,ace teenager like Rufaidah amma Sam bata damu da ibada ba ,koda harda rashin zuwa makaranta da kuma hulɗa da batayi da jama'a,dan ko a ɗan zuwan da takeyi ta fahimci cewar ,rayuwar kaɗai ci Rufaidah keyi dan bata taɓa shiga sashen su Mu'aiseen ba ,haka idan ba shine yazo nan sashen su to babu wanda yataɓa zuwa daga can sashen. tana cikin wannan tunanin ne xuciyarta ta kwaɗaitar da ita son shiga bangaren su Haisam ,san ko tunda take zuwa gidan ,iya kacinta shiga sabgar aikinta babu ruwan ta da kowa ,ɗakin Larai ta leƙa se ta sameta kan dadduma da alama bata idar da addu'a ba ,saboda haka kawai ta nufi sashen su Mu'aiseen kanta tsaye batare da tunanin komai ba Tun daga nesa take jiyo hayaniyar mutanen gidan ,lokacin da ta karasa bakin kofar da ze sadata da main falon su ,se taja ta tsaya tanabin takalman da ke zube a kofar ,se hayaniya suke da alama musu sukeyi akan wani abun ,ɗaya bayan ɗaya takebin takalmin da ido kamar me son gano wani abu ,ganin idan ma ta shiga batasan abinda zata ce dasu ba ,se kawo ta jiyo ta fito ɓangaren. Sedai abinda Meerah bata sani ba shine tun shigowar ta Mu'aiseen ya ganta ,tsaye yayi yana tunanin yarinyar ,tabbas yana zarginta sam bai yarda da itaba, zuciyar sa na bashi cewar wasu suka turota gidansu ,dan su cutar dasu ,idan ko hakane yazama dole yasaka ido sosai a kanta kuma zejawa Rufaidah kunne ,duk da yasan ba kula masu aiki takeyi ba ,xeyi bincike sosai akanta. Seda taje tayiwa Larai sallama ,kafin ta wuce gida. Niger state Hajiya Sauda ce zaune a tsakiyar aminan ta ,magana sukeyi amma sam baka jin me suke faɗa da alama suna tattaunawa ne akan abinda ya shafe rayuwar su wanda basa so kowa yaji ,sun daɗe a haka kafin kira ya shigo a wayar ɗaya daga cikin su ,kallon juna sukayi ,se ta saki muemushi tace "Alh Tanko ne kisan sa sarkin naci tunda yaga hoton wata baby a wayana shikennan ya ɗaga hankalinsa kuma na faɗa masa cewar tawa ce bazan bashi ba amma ya dage ,akan ze bani ko nawa ne wai yarinyar irin wacce yakeso ne"ta karashe faɗa tana yamutsa fuska " haba ke ko Hajia mene ne idan har ze bada abinda kikeso aikawai kibar masa ,ga matan nan da yawa kuma kwanan nan Hajia saudah zata yi tafiya na tabbata zata samo mana wasu hot babies kinsan dai Hajia bata tafiyar banza" dukan su kallon Hajia saudah sukayi,cikin son tabbatar da Abinda Hajia Laura ta faɗa ,gyaɗa musu kai tayi cikin tabbatar wa tace " kema kinsan hana wa Alh Tanko yarinyar ze iya janyo mana matsala ,sune masu ɗaure mana gindi da yanzu zaman Niger yafi karfin mu kuna sane da sa idon da mutanen gari sukayi mana ko? to ki kwantar da hankalinki ,ki ta tsesa sosai kuma ai zaku iya riƙa anfani da ita ku duka biyun Kinga kenan riba kan riba" Hakane fa Kinga farko duk banyi wannan tunanin ba ,amma Hajia Sauda yaushe ne tafiyar ina fatan dai bazaki ɗauki lokaci a can ba?". "Ehhh to kema kinsan badan Alh yace ze dawo daga Cyprus ba to babu abinda zesa na koma gida yanzu ,to bazan iya barma munafukar matarsa shi ba ,shegiya wai ita me kirki duk abinda zanyi mata bazata taɓa tankani ba ,shiyasa nagaji na ƙyaleta ,raina yana baci idan naga tana mammanewa Alh" tafaɗa cikeda takaici ,tsaki Hajia Laura tayi tace "wlh Hajia ni kina bani mamaki ,miye abun kishi ga namiji ,bayan macece keyi miki abinda ko rabinsa baze iya

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34