Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

Chapter 23

Mabaraciya Book 2 Complete Hausa Novel 1,194 words 0 views Progress saved
Download Book

gaskiya babu lefi itama Saudah tana ji da kyau wanda kusan ma shine abinda ya fara jefa ta wannan rayuwar Bayan Meerah tagama gyara ɗakin Rufaidah se tace da ita ta shiga dakin da yake opposite na Mama ne kitabbata kinyi komai yadda ya kamata,kuma ki kiyaye hannun ki da ɗaukar abun da xe iya zamo miki masifa"Murmushi Meerah tayi tace" karki damu shi kansa hannun ai dole ze kiyaye ,dan yasan ba'an halicce shi saboda ɗaukar abinda bana sa bane ,shiyasa yafi sabawa da neman lada ,bara nayi sauri kar na ɓata lokaci" haka ta fita tabar Rufaidah ciwon zuciya ,dan ita fa bata gane magana Meerah ta faɗa mata ba kawai dai taji haushine ganin taki nuna ta damu da maganar da tafaɗa mata A ƙofar ɗakib ta ja ta tsaya ,se kuma xuciyar ta keyi mata tunanin " yanzu idan kika shiga ta murƙushe ki cikin ɗakin nan fa? anya ba gangancin zanyi wa kaina ba? kai ina ma ai bazata fara aikata hakan ba tunda tasan zan iyayun ihu na tona mata asiri " da wannan karfin gwaiwar ta samu ta sai-saita natsuwrta tayi knocking , sedai shiru babu amsa ,ganin tayi har sau uku ba'ayi magana ba se tayi tunanin ko bata ciki ne saboda haka kawai ta murɗa ta shiga saboda ,ganin dakin yayi kura sosai ga kuma toilet a sake da alama anyi anfani da shi anmanta ba'a rufe bane ,sam bata kula da Hajia saudah da ke can wani ɗan lungu da ke tsakanin gado da madubi ba ta duka ne da alam tana neman wani abune ,shiyasa Meerah bata kula da ita ba ,ganin ɗakin yana bukatar gyara na musamman se kawai ta cire hijabin ta ta aje gefe ƙyam saudah ta kafe idon ta akan Meerah ,dan kuwa irin tight shirt dinann ne a jikin ta ya ɗame ta sosai hakan yasa duk wani hallita da baiwar da Allah yayi mata ya bayyana ,ga gashin ta da ta tufke a gefen kafaɗa ,yawun wahala saudah ta sauke " ashe duk yadda take tunani ma yarinyar ta wuce can tabbas wannan zata kawo kudin da bata taɓa samu da wata mace ba ,dole ne ta ajiye kishi gefe ta mora kuma tabawa se Sanator su mora dan tana da tabbacin ze iya bayarda ko nawa ne akan wannan . Meerah da bata san wainar da ake tuya ba ,ta saki jiki aikin gabanta kawai take gashi har wani girgiza jiki take wanda ita a wurinta sauri takeyi while Haija saudah kuwa mutuwar zaune hakan ya sakata. Tsaf tagama gyara toilet din kafin ta zo tafara gyara gado yaye bedsheet ɗin da ke shinfiɗe tayi ,ta je tasaka a ta buɗe weldrop tana neman wani ,cikin Sa'a kuwa ta samu zuwa tayi zata shinfiɗa ,mamaki ne ya cika Hajia saudah ƙarfin halin yarinyar ko waye yabata damar canja wa ,duk masu aikin su babu wanda yataɓa haka sedai idan itace taga yayi mata datti idan sun shigo se ta ciro masu tace su shinfiɗa wannan ,amma ita ta saki jiki kamar tana gyaran gadon gidansu ,seda Meerah ta shinfiɗa ta zo wurin soke gefe da gefen gadon ne idon ta ya sarƙe cikin na Hajia Sauda ,ihu ta saki dan har ga Allah taji tsoro ,cikin sarƙewar murya Hajia Sauda tace " ke..la.fi.ya? Ita fa a tunanin ta ko tsawa tayiwa Meerah ,sedai batasani ba duk wanda yaji maganar ta ze iya fahimtar cikin halin da take ,da sauri Meerah ta rarumi hijabin ta ta saka ,ta dawo " dan Allah Hajia kiyi hakuri wlh bansan kina ciki bane nayi knocking naji shiru "Hajia saudah bata son Meerah ta fahimci wani abu se ta fitar da wayarta. Kamar tana dannan wa tace " ya Sunan ki? Suna na Aminatu waye Mahaifin ki? raurau tayi da ido kamar xatayi kuka tace " Labaran dan Allah Hajia karki koreni ni wlh zanyi duk abinda kikeso ,indai zan samu kudi iyayena talakawa ne ,nikuma banaso na tashi cikin rayuwar talauci ,shiyasa ma nake wanann aikin da zan samu wanda yafishi ma zanyi....... *Yanzu za'a fara wasar* Amma *babu tabbacin kusamu karashe dan wlh na raina wa comments ɗInku ,kuma indai mutum ya sanni to ya san halina dan na dakata da labarin nan ba sabon abu bane a gareni har sadda kuka shirya gyarawa se muci gaba* Akwai ƙura fa ,dan kunji Rufee tayi scarce a wannan page ɗin to tana can tana nemawa kanta mafita ne dan dole zata aure Mu'aisam😂 Masu yimin comments ina godiya kuma wlh inajin daɗi , luv you so much billahi❤️❤️ Comments and share Real Bazamfaria ce❤️ *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* ( *On* *word* *together* ) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* *By* *FIDDAUSI* *SANI* (damsel feedorh) 🅿️:2️⃣0️⃣ *This* *page goes to my VIP my Mom @Maryam Sa'ad and Anmata Khairatu* *nasan cewar* *zeyi muku daɗi* *dan anzo wurin da kukeso* *ina godiya da* *soyayyar ku gareni Allah yabar ƙauna*❤️ Murmushi Hajia saudah tayi mata ,tana faɗin " jeki karasa aikin ki" kamar gaske Meerah ta tashi cikin mutuwar jiki tana ci gaba da gyaran gadon ,tashi Hajia Saudah tayi tabar mata ɗakin ,tana fita Ameerah ta sauke ajiyar zuciya ,tare da zama daɓas kan kadon ,duk da tana cikin murnar ganin tafara samun nasara ,amma gaskiya xuciyar ta cike take da tsoro ,ga kuma tunanin idan Hajia Sauda ta bukaci tafiya da ita garin da take rayuwar ta ya xatayi kennan ,tasan ko giyar wake Yaya yake sha baze taɓa amincewa da ta tafi wani wurin ba ,dama dai ace ta shirya tafiya garin su,ta wannan hanyar ne kawai take tunanin nasara Hajia Saudah ta na fita daga ɗakin tayi saving vidion da tayiwa Meerah ,da sauri ta turawa Hajia Laura ,dama tana online tun ɗazu take tsimayen zuwan sakon yana shiga kuwa tayi azamar buɗewa ,da kyau take kallon Vidion kashe data tayi ,dan taga kamar zasu fahimtar juna baki da baki ,dan haka se ta kira Hajia Sauda Tana ɗagawa tace " wlh Uwar daba ke ɗin nan me Sa'a ce ina kika samo wannan gashi da ganin idon ta xatayi kwaɗayi Kinga baxaki sha wahala akan ta ba ,kai gaskiya ta haɗu ,amma menene abun da kike tunani ze miki shamaki da ɗauko ta ,ina da bakinta naji ta fadi cewar tana neman aikin da yafi wanda takeyi ,kuma ma iyayenta talakawa ne kawai inaganin ,kayan abinci zaki siya kicika mota kikai musu ,daganan se ki nuna musu kina tausayin rayuwar yarinyar ne saboda haka zaki tallafa mata zaki tafi da ita inda kike aiki kisakata school,ina dama akan wannan tsarin kike ,to miye matsalar ?". Dariya Saudah tayi tace " wlh Hajia ina akan wannan tsarin sedai haka kawai xuciyata bata kwanta da yarinyar ba inajin tsoron ta janyo min matsala" mtssww Hajia wani lokacin kinada abun takaici menene matsalar kimsan dai babu wanda ya isa yayi exposing naki,saboda kinada kima da mutumci a idon jama'a ,ke ko ba haka ba bana tunanin akwai hukumar da zata iya hukunta ɗaya daga cikin mu ,kin manta masu hukumar ma munayi musu amfani to ,Kinga idan kina jin tsoro ne akwai plan B" ina jinki menene shi? Yawwa shiryawa zanyi inzo kawo miki ziyara ,daganan se nace dama ina

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34