Chapter 6
Chapter 6
tafada batare da alamar damuwa ba Follow me on wattpad@damselfeedo Yuh can drop ur comment via my watsap no 08039228702 #Real@Bazamfaria *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* ( *On* *word* *together* ) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* *By* *FIDDAUSI* *SANI* (damsel feedorh) 🅿️:8️⃣ ,,,,,,Meerah na komawa gida Aunty ta sakata gaba da tambayoyi sedai takasa fa'dawa aunty gaskiyar shirinta akan Saudah ,da ta dameta da tambayar Ina ta tafi se kawai tace da ita " gidansu Saudah nakoma na gani ko ta dawo ,yanayin da tayi maganar ne ya bayya nawa aunty cewar karya tayi sedai ,batayi mata musuba ta kyaleta Bayan fitar Meerah ,Fatima tafara tunanin shin ta ina zata cika alkawarin da ta daukarwa Meerah ,ta sani ba lallai bane Rufaida ta kulata,domin shegen jin Kaine da ita ,amma dole zata kusanceta saboda bataso takasa cika alkawarin Meerah kuma tanada assurance cewa koma menene to alkhairi ne Meerah zata aikata. Bayan kwana biyu ,Fatima ta shirya ta tafi gidan su Rufaida ,seda ta tabbata tayi shiga na alfarma ,ta yanda komai wulakancin Rufaida bazata wulakanta ta ba ,magiya tayiwa Momynta akan tabata aron mota ,dakyar ta yarda ta bata key ,cikeda jin dadi kuwa ta nufi gidan Yusuf tsoho ,horn tayi mai gadi yabude mata get ,cikeda isa ta kunnan kai cikin gidan da wani irin gudu ,bata tsaya ko inaba se wurin da aka tanada domin a jiye motoci ,ta dade zaune a motorn tukuna ta fito ,tafiya take irin na Clasic lady kai da kaganta kasan sun tara duniya tunda ga yanayin motorn dake driven dole ka girma mata ,kamar ta shiga tagaida 'kawar Momynta sekuma tayi tunanin hakan na iya bata mata shiri ,deciding tayi kawai ta tafi part dinsu Rufaida ,cikin sa'a kuwa tana hawa corridorn da ze sadata da ainahin sashen ,suka ci karo da Rufaida,rasa me zatace mata tayi saboda haka tayi kamar bata ganta ba ,tana shirin gibta ta ta shiga ,ta tsinkayi ego voice dinta tanafadin " hey where yuh wanna go ? tabe baki Fatima tayi itama cikin nata salon tace "am looking for Hajia Aisha ,cikeda mamaki Rufaida ta kalleta " there's no Aysha in our family yuh can back to ur home and ask the real address " OK do me a favor pls ,Fatima tafada tana kallonta ,batare da Rufaida ta kalleta ba tace " am all ear's " let me have some rest before I leave I have so tired ,tafada with tired voice Shiru Rufaida tayi kamar mai nazari ,ganin haka yasa Fatima juyawa tare da fadin " OK tanz tafada kamar da gaske tafiyar zatayi "zo mu shiga ,murmushin samun nasara tayi tare da fadin " to ,Rufaida ta shiga agaba tana binta abaya Harcikin falonsu tayi mata iso ,haka Fatima takoma tamkar wata sakarya domin ganin tsari da kyau irin na gidansu Rufaida ,abunda yafi dore mata kai befi ganin komai yanada banbanci da na su Mu'aiseen ba tamkar ba' a karkashin mutum daya suke ba ,da ta tuna da irin dukiyar da Hajia Saudah ake fadin tana dashib,se taga ai wannan ba komai bane ,tana zaune Sega mai aikinsu ta kawo mata drinks tare da gaisheta ,ko kallonta batayi ba zata wuce ,Rufaida tace " Waze zuba mata lemun " no kibarta kawai bakiji me najiba ai bazan iya shan abunda ta ta ba ba tafada cikeda sigar wulakanci ,murmushi taga Rufaida kamar yanda take zato ,itama murmushin tayi domin saboda itane yasa tayi hakan duk da harga Allah taji babu dadi na wulakanta yarinyar ,amatsayinta na 'yar adam Suna zaune shiru ,kowa se dannan wayarshi yakeyi ,kamar batason magana tace " sorry sis na bata miki lokaci zaki fita ko bari ma nawuce ,murmushi Rufaida tayi tace " babu komai fa dama shopping zan tafi " ayya to ko mutafi kinga dama nima shopping zan tafi shine mom dina tabani sako nakaiwa 'kawarta Hajia Aisha gashi nazo kince banan bane ,saboda haka kawai mutafi ,tashi sukayi suka tafi ,kowa motor dinshi yanufa ,sedai Rufaida tayi mamakin ganin irin motorn da Fatima ta shigo ,lallai ba karamar yarinya bace ,kalar motorn da take ta rokon Hajia Saudah ta seyan mata ,tana ganin kamar ita 'yargata CE ,segashi wata har tarigata yi ,da wannan tunanin suka fita gidan ........ ,,,,,,,basu zarce ko ina ba se Jifatu super market,siyayya sukayi sosai ,bayan sun fito ne zasu shiga motor ,adaidai bakin motorn Rufaidha ,Sega wata mabaraciya ,yanayin tufafin jikinta kawai XE tabbatar maka da tana cikin wani hali ,Sam hankalin Rufaida bekai gareta ba ,sejin tayi anjanyo d'an mayafinta ,cikeda mamaki ta juyo ita a zatonta ko Fatima ce setaga sabanin haka ,a zabure ta ture matar cikeda kyankyami tace " bakida hankali zaki tabani da 'kazamin hannunki ,zuge jaka tayi tajefa mata ,wasu kudi ,tabude motor zata shiga " ita wannan mabaraciyar ba kaskantacciyar da zaa jefawa kudi ta dauka kamar anwatsawa kaji hatsi ,maganar tashiga kunne Rufaidah da kyau ,kallon mamaki tajuyo tanayimata se a lokacin ta kula Ashe yarinya ce Mabaraciyar ,murmushi tayi ,cikeda wulakantarwa tace " bakida banbanci da kastantacciya ,domin kowa yaganki yaga ,mafi wula'kantacciyar mace ,da shi mabaraci har wani matsayine dashi INA bara kikazo kuma nabaki ,idan bakiso zaki iya xubdarwa du'kawa tayi ta tsince kudin daga kasa ,seda takalleta sama dakasa ,tukuna ta watsa mata ,mamaki ne Yakama Rufaida tarasa cewa komai ,sema duniyar tunani da tashiga , shin me wannan mabaraciyar take ta'kama dashi da har zata mata haka "wai me kike jira baki shiga motor ba ,ta tsinkayo maganar Fatima . Nuna mata ,wacce ke gabanta Rufaida tayi ,kallon ta tayi cikin sa'a kuwa suka hada ido ,batasan lokacin da tace Meer.....se kuma tayi shiru sakamakon ,girgiza mata kai datayi " kinsanta ne Rufaida ta tambaya ,yamutsa fuska Fatima tayi tace " taya kike tunanin zansan ,irin wannan tafada tana nuna Meerah kamar taga kashi ,kawai dai ina mamaki yanda kamarki kika dauki wannan lokacin ,tare da ita ,kina sha'kar warin jikinta ,abun takaicin ma duk carbondioxide dinta ,shine me zama oxygen a gareki . "Ke dakata Mara tarbiya ,Mira tafada kanta tsaye " nice yakamata nayi gaugawar barin wurin nan tun kafin fushin Allah ya sauka ga yayan barayin gomnati kamarku ,har ya shafeni ,kuna zaune anacidaku da dukiyar talakawa ko ,to ni da kuke gani nafijin dadin rayuwa ta ahaka MABARACIYA akan na ginu da dukiyar haram ,hannu Rufaida tadaga da nufin ta mareta da sauri Fatima tarike " don't be anger pls ,kwace hannun ta tayi sedai tayi rashin sa'a domin kuwa Meerah hartayi nisa ,a fusace ta shiga motor, ganin yanda temper dinta yayi high ne yasaka Fatima yiwa motorn ta key ta zagayo tashiga na Rufaida, itace tayi driven Suna cikin motor ne sako yashigo a wayarta ,dubawa tayi kamar yanda tayi zato kuwa Meerah ce ,karantawa tayi ,tayi mamaki sosai jin abunda Meerah tace tayi kuma as shine next plan dinsu ,bataso Rufaida ta zargi wani abu shiyasa ,bata rubuta reply ba. Suna kaiwa gida a fusace Rufaida ta balle murfin motor ta fita, jakanta ma anan tabari ,se Fatima ce ta daukan mata ,zagayen falo tasameta tanayi " miye na damuwa don wata mabaraciyar ta yi kuskure a gareki domin na tabbata kuskure ne batasan ko kedin wacece ba " bandamu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34