Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Mabaraciya Book 2 Complete Hausa Novel 1,175 words 0 views Progress saved
Download Book

tana jansu Rumaisa a jikinta. *Manage pls wlh yau na* *fita ne *banaso* *nayi* *disappointed naku shiyasa nayi muku wannan** Real Bazamfaria ❤️ *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* ( *On* *word* *together* ) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* *By* *FIDDAUSI* *SANI* (damsel feedorh) 🅿️:1️⃣6️⃣ kamar kullum , Ameerah tayi shirinta da wuri dan zata iya cewa tunda tafara wannan aikin to bata taɓa saɓa lokacin da Rufee ta bata ba ,cikin doguwar rigar atamfa da ɗan farin hijabin ta yiwa Aunty sallama ta tafi Saukanta daga kan mashin yayi dadai da zuwan Mu'aiseen,da alama ya dawo daga motsa jiki ne , da sauri ta biya me mashin kuɗin sa tashige ciki dan tana kula da irin kallon da yake yi mata. A kitchen tasamu Larai gaisawa sukayi kafin ta shiga ciki dan fara aikin ta ,kamar kullum ƙasa take fara gyarawa kafin Rufee ta tashi bacci se ta gyara saman,cikin natsuwa take aikin ta ,bayan ta gama morpin se ta dawo guguan plasman da ke manne a falon , motsin da taji ne kamar anshigo yasakata waigawa dan a tunanin ta ko Larai ce sedai arba da tayi da wani Farin dattijo yana sanye da farar jalabiya se counter da ke makale a babban ya tsan sa ,sunkuyawa tayi tana gaishe shi ,cikin fari'a ya amsa mata tare da tambayar ta Rufaidah "bata riga ta tashi ba " shine amsar da ta bashi ,ganin bece komai ba yasakata tashi tana faɗin" bara na kirata" dan ta fahimci shine Alh Yusuf tsoho dan taga yana kama da Mu'aiseen,dakatar da ita yayi da cewa " No dawo ki zauna" dawo wa tayi ta tsuguna a kasa ,tayi shiru tana jiran taji aiken da zeyi mata ,se taji yace " baki daɗe da fara aiki anan bane ko? Kai ta ɗaga masa dan batasan dalilin tambayar tasa ba " shiyasa ai naga kamar bakisan tsarin gidan ba ,idan Rufaidah tana bacci ba'a tashin ta harse ta falka da kanta saboda tana fama da chronic headache (migraine) so idan aka tasheta wani lokacin kanta daya harba shikennan se rashin lafiya" Allah yabata lafiya ,ban sani bane " Murmushi yayi yace ai nasan baki sani bane shiyasa na faɗa miki ,amma ke anan garin kike " ehhhhhh anan nike " ya sunan Mahaifinki? samun kanta tayi da ɓoye masa sunan Mahaifinta kawai se tace Labaran( sunan mijin Aunty kenan) ajiyar zuciya taji ya sauke "tare da faɗin " je ki ci gaba da aikin ki " ajiyar zuciya ita ma ta sauke dan ta fahimci be gane ta ba ,dan se yanzu ta tuna fuskan shi ,shine mutumin nan da suke zuwa wurinsa itada Abbanta lokacin batada wani wayo. da sauri ta samu ta kammala lokacin har yabar sashen ,zama tayi kan ɗaya daga cikin kujerun falon tana tunani " tabbas idan dai har haka wasu ke rayuwa to zata iya cewa suna cikin halaka ,yanzu kamar Rufaidah ,saboda wani dalili da be kai ya kawo ba za'a ba'a tashin ta sallah shiyasa se ta gadama take tashi ashe tun tana yarinya ne akayi mata wannan sabon kuma abun takaicin wai uba mahaifi da aka sani da sa ido da kula akan addinin iyalinsa ,shine ke faɗar wai ba'a tashin ta ,mutum nawa ne keda cutar da tafi nata amma hakan be zama uzuri gurinsu sun wo fantar da ibada ba, and migraine ai ba ko yaushe yake tashi ba ,yanzu yarinyar da ko yau akayi mata aure zata haihune suke treating lyk a baby ,waye ze kula mata da tarbiyyar yaranta idan tayi aure ta haihu bayan ita kanta tana da ƙarancin tarbiyyar. Tayi nisa sosai cikin duniyar tunanin ta har batasan lokaci ya tafi ba se saukar zagi ,me haɗe da tsawa da taji akanta " Uban wa yabaki damar zauna mana a inda muke zama ,kina matsiyaciya ƴar matsiyata ne zaki zauna min anan ,ok ki kina tunanin shirun da nayi miki yana nufin nabaki dama ne kiji daɗi to bara kiji ,alƙawari na ɗaukar wa kaina maganin kin wulakanta yanzu ma ina tunanin abinda zanyi miki ne wanda harki koma ga Allah baxaki manta ba wanda zesa kigane banbancin da ke tsakanin talaka da me kuɗi ,ko da yake na daɗe ina tunanin cewar gata nayi miki ɗaukoki daga yawon titi kina bara na kawo ki gidanmu ,amma wlh se kin kwanmace yawon bara akan zaman gidan nan ,shegiya me fuskar jajayen Aljanu. Ita dai Meerah da ido kawai take binta dan kallon taɓaɓɓiya yanzu takeyi wa Rufee ,to miye banbancin ta da Mahaukaciya ,ace mace sam ita a rayuwarta bata san menene mutunci ba " kina bacci Alh yashigo ,harma ya daɗe anan sedai be samu ganinki ba inaga Yakamata kitafi kigaisheshi dan yasan cewar kin tashi lafiya ko" Meerah ta faɗa cikeda rashin damuwa kai kace ba ita Rufee tagama zurfawa zagi ba, aiko iya baƙin ciki Rufee ta shaka dan idan akwai abinda ke ƙara sakata baƙin ciki befi idan tayiwa Meerah masifa itakuma taƙi kulata ba ,har xatayi magana kuma se ta fasa kawai ta fita daga falon " kyaji dashi masifaffiyar banza banazo nan saboda ke bane da uwarki zanyi dan zaman jiran ta nike ,badan haka ba ko ance kibuɗe baki ki zagi Ameerah ai zaki musa ,mtsswww se kace garesu farau arxiƙi kome dai ida masu arxiƙi wannan ranar da ta fahimci arxiƙin da take taƙama dashi ko na miye to bansan ya xatayi ba " ita kadai tayita da batun ta daga ƙarshe dai ta wuce sama dan gyarawa kafin ta janyo wata masifar. Rufaidah na fita ta nufin ɗakin Abba ,saboda ma bata so ta haɗu da ɗaya daga cikin su Ammi se kawai tabi ta baya inda kai tsaye xe sadata sa falon Abba dan tanada tabbacin yana ciki shikaɗai saboda a irin wannan lokacin yakan buƙaci keɓewa a cewsrsa ze huta ne to baya buƙatar ganin kowa Knocking tayi ,daga ciki Abba yabata izinin shiga,da Sallama ta shiga , sedai haɗe fuska tayi sakamakon ganin Rumaisa a ɗakin ,dukansu suka amsa mata sallama wuri tayiwa kanta ta zauna " Abba ina kwana an ce ka shigo ina bacci ,ai bansan zakazo da na tashi da wuri " Murmushi Abba yayi mata yace " karki damu ,kintashi lafiya ko " Ehhh Alhmdulilah Abba ya gajiya "ba gajiya ya amsa mata " bakiga ƴar' uwarki ba ? Yafaɗa yana kafe ta da ido dan ganin tunda ta shigo bata kalli Rumaisa ba ,narke fuska tayi kamar xatayi kuka tace " na ganta mana " amma shine kika kasa yimata magana wai Rufaidah meyasa ke bakijin magana ina jiyan nan nagama yi muku faɗa akan ku haɗa kanku" haba Abba nide bansan me akafaɗa maka akaina ba wannan karon duk kabi ka tsaneni ,ina nice babba idan gaskiya za'ayi waya kamata ya gaisheda wani a tsakanin mu ?. "Ungo nan Rufaidah"Abba yayi mata daƙƙuwa " ni kike faɗawa idan gaskiya za'ayi ok wato yanzu banyi gaskiya ba ko " yi haƙuri Abba ,ai tana da gaskiya nice yakamata na gaisheta ,but banyi hakan ba nikuma a tunanina na amsa mata sallama ,shiyasa naga babu bukatar se na gaishe ta ,amma tunda gaisuwar takeso zanrika gaisheta ,shikennan ko?Rumaisa tafada tana kallon Rufaidah ,harara ta zabga mata tare

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34