Chapter 7
Chapter 7
a wannan lokacin sai na ji zuciyata har gangar jikina sun ƙi amincewa da suna iya zama da Yarima Faysal, mutumin da yake taƙama da mulkin ƘASAITA,shin ko dai ni ce ban san son ba, ban kuma san makarai da makangan so ba? Tambayar tawa babu mai amsa mini ita. Ganin har ƙarfe uku na dare ta yi yasa na miƙe na yi alwala domin in ragewa kaina da zuciyata zafin da suka ɗauka, sannan in roƙi Allah da ya zaɓa mini abokin zama wanda yake mafi alheri a gareni, Anwar ko Yarima, saboda ni na kasa gane wa nake so a cikinsu. Ƙarfe goma na safiyar yau juma'a sai ga ɗan aike daga fadar Sarki,magatakarda ya kawo mini saƙon zungureriyar takardar da ta ƙara tayar mini da hankalina,dama daga wanka na fito, cikin nauyin jiki don ma na samu na ɗan gyara fuskata, da ɗan mutstsuka mai ina shirin saka kayana saƙo ya iso mini. Tun da na zauna a gefen kujerar tsakiyar ɗakina ban iya ma buɗe takardar ba, saboda ji nayi kamar kaina ba a wuyana yake ba,ni kaina ban san iya mintunan da na ɗauka ba a nan zaune, sai da Mansura ta shigo sannan na ji tana tambaya ta wai lafiya? Duk maganar da take mini a farko na ɗauka mafarki nake, sai da na ji an dafa mini yatsun ƙafafuna, sannan na ɗaga na gan ta a durƙushe gabana. Ban san hawaye nake fitarwa ba sai da na dawo hankalina ga shi duk tafiyar nan da na yi ban ji na je kowacce duniyar tunani ba,ni dai cewa na yi ko kuwa don haukan minti biyar ɗin da aka ce duk ɗan adam na yin shi duk rana kenan dai shi na yi a zaune. Miƙawa Mansura takardar na yi na ce karanta mini da ƙarfi. Da ta karanta sai na ji ba wata takardar tafiya gida ba ce,ko ince takardar rabuwa da Yarima ba, ashe ta saƙon in je Sarki na kirana ce,in an sauko daga masallaci,tana gamawa na ce mata je ki waje ga ni nan zuwa, to ina za ni? Wa zan gayawa? Tunanin da na cigaba da yi kenan. Cikin mintuna baƙwai sai na ji Aunty Salwa ta faɗo mini a raina, na yi sauri na miƙe na ɗauko wayata na daddana nambobin, minti ɗaya aka ɗauka, ina fara gaya mata abin da ke faruwa. Ya isa haka ta ce mini,in je tana son ganina,ba zancen waya ba ne ba, saboda haka in tambayi Yarima in fito da wuri,in biya ta gidanta. Wannan fa ya bani ƙwarin gwiwar in shirya in isa gidan Yarima,a yanzun ɗin nan. Baƙar shadda ce Galila, wacce aka yi wa aikin hannu, duk ta sha ɗigon farin aiki, ƙasan zanin kuwa aiki ne mai yanka-yanka, iya kusurwar cinya yake, sai hannu iya rariyar hannuna, duk ya sha tsagun irin na jikin zanan. Turare na ɗauka hannuna ina shirin fesa shi a jikina, sai na ji murɗawar ƙofar ɗakina a hankali, ban yi tunanin juyawa in ga kowa ke shigowa ba, saboda ganin ina tsaye a jikin madubi kenan ko wa ye zan gan shi ta cikin madubina. Gabana na ji ya yi wani abu wanda ya ratsa mini naman jikina ya bi ta cikin jinina har ya fito ga saman fatata. In da gashin da ke saman fatar duk ya miƙe tsaye, wannan ne na ji ana cewa tsigar jiki. "Me ya kawo mini? Ganin Yarima da na yi ta cikin madubina ya shigo da doguwar rigar bacci jikinsa mai wani irin aikin sarauta, amma iyakacinsa bakin ƙofa, ya jingina da ƙofar ya mayar da hannayensa ya goya a saman ƙirjinsa ya harɗe ƙafafunsa da juna, tare da mayar da kai ya jingina shi a jikin bakin ƙofa sannan ya ɗan ɗaga kansa sama da turaran a hannuna na ɗan wayance na iso wajen da yake a tsaye. "Yarima barka da asuba." Ya juyo da kanshi ya kalleni, sannan ya amsa da laɓɓansa ne kawai na ga sun motsa, har da lumshe idanuwa da buɗewa. "Lafiya?" Ya juyo ya kalleni,a take na ga idanuwansa sun yi jajir. "Da ki kaga me?" Ya faɗa cikin maganar raɗa-raɗa. "Idanuwanka na ga sun yi ja.” Sai na ga ya yi murmushin da ya dinga fitar da sauti, sai na ga ya wuce ni ya shiga cikin ɗakin ya samu kujerar da ke tsakar ɗakin ya zauna, sannan ya ɗago hannu ya yafito ni, ya nuna kusa da shi, ma'ana in zo in Zauna. Ban wani nuna damuwa ta ba na iso amma sai na ji na kasa zama saman kujerar na koma gefe ɗaya na zauna a ƙasa, madadin ya yi magana shi ma sai na ga ya zamo ƙasa ya zauna kusa da ni, na yi alamar zan matsa, gaba ɗayan shi ma ya juyo gare ni tare da kaikansa wuyana. Cikin maganar raɗa na ji ya yi magana. "You hate me.” Ya ƙara yin sama da kan shi zuwa daidai kumatuna. "Sarki ya aiko in je." Na yi saurin faɗa ina mai alamar tashi, yasa hannuwansa duk biyu ya rungumo ni jikinsa ta gefena. "Yarima." "Yasmin, Yasmin, Yasmin,jiya na ƙwana ina roƙon Allah ya cire mini ke daga zuciyata but still... Na lura ke har yanzu zuciyarki ba ta son zama da ni." Ya yi murmushi. "Nayi tunanin in zo in yi sallama da ke, Idan har na fahimci ke har yanzu you don't want to stay with me,saboda ni na san halin Sarki, ba ya sauraran komai idan ya riga ya faɗi magana.” Duk wannan maganar da yake yi a cikin raɗa yake yin ta, irin ta marar lafiya, sannan ga shi ya matse ni a jikinsa, sai shinshinar min wuya yake,yana ƙara tura kansa cikin wuyana,ni kuwa idanuwana a lumshe suke ban da numfashina da ke neman ɗaukewa. "Ba zan iya tsallake duk hukuncin da Sarki ya yanke min ba, amma zan ɗan yi iya ƙoƙarina in ga ko na samu nasara.” Ya yi shiru a daidai lokacin da ya juyo da fuskata a tasa. "Amma na yanke hukuncin barin ƙasar.” "Saboda me?" Na faɗa a sanyaye nima. "Saboda ke.” "Kai da baka so...” yasa yatsunsa biyu a laɓɓana yana zagaya su, wannan yasa ban iya ƙarasa magana ta ba. Na yi ɗan hanzari kaɗan na miƙe, saboda jikina da na ji ya fara rawa. "Wai me ye haka Yarima?” Na yi irin maganar nan wacce da ji na da ƙyar na ƙwato ta daga bakina, ya mayar da numfashi ya kai sau baƙwai, sannan ya miƙe tsaye. "Sorry.” ya juya ya tafi, har ya kai ƙofa na tuno da maganar zuwa gidan Aunty Salwa,na yi masa magana. "Yarima,ni zan je gidan Aunty Salwa yanzu, bayan masallaci nima zan wuce Sarki ya aiko in je." "Ki gaishe ta.” Kawai ya ce ya juya ya fita,a inda nake tsaye a nan na durƙushe na yi wajen minti talatin sannan na samu da ƙyar na miƙe na ƙarasa shiryawa. Ban ƙara ganin Yarima ba sai da na shiga ɗakin Hajiya a nan ne take ce min Yarima na cikin ƙuryar ɗakinta a ƙwance, ban iya tambayarta ba ko lafiya sai na ji zuciyata tana son ta ganshi, na san kuwa ba zan taɓa iya wuce Hajiya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24