Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Chapter 12

Kasaita Book Two Complete Hausa Novel 1,234 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kawai na yi ƴar dariya, shi ma sai ya ƙara yin murmushi, sannan ya tashi ya zauna ya kishingiɗa a cinyata da take durƙushe, sai a lokacin ne ma hankalinmu ya kai ga abin da ya kada shi. Takalmana ne da na yi jifa da su muka gani a gefe ɗaya, yasa hannu ya ɗaga takalman ya kalleni sai kuwa muka yi dariya gaba ɗaya, amma irin mai kama da murmushin dariya,yana cikin haka ne ya juyo ya haɗa goshina da nasa, sannan ya rataye hannayensa bayan wuyana. Cikin yanayin dariya ne ƴan hawayen da suka fito a lokacin da nake faman son in ga ya tashi suka gangaro, sai na ji ya saki takalmin ya ɗago fuskata yasa hannayensa duk biyun ya lalubo kumatuna, sannan yasa manyan ƴan yatsunsa yana goge mini hawayena tare da girgiza kansa alamar a'a. Sai kuwa na jina lumshe idanuwana ina yin ƴar wata dariyar kuka-kuka, murna-murna, sannan na sunkuyar da kaina sosai na ci gaba da ɗan kukan murna,gashin kaina kuwa ya zubo ya rufe mana fuskokinmu. Ina jinsa ya sa hannayensa ya tattare gashina, sannan ya ɗago kaina da hannayensa, kallon da ya yi mini yasa a take na ji na nutsu, saboda haɗa ido huɗu da muka yi da shi,kafin in yi wani motsi tuni ya kai bakinsa ga nawa, kafin inyi wani tunani har ya lalubo harshena ya riƙe. Wasu tsutsotsi na ji suna yawo a kaina na yi sauri na ƙwace bakina, amma sai na ji kuma na faɗa ƙirjinsa na ƙwanta,jin ya mayar da ni ya rungume tare da sumbatar gefen wuyana cikin nutsuwa na ji ya ɗagoni yana sumbatar ko'ina na jikina, wata zuciya ta dinga karanta mini maganar da Aunty ta yi mini amma wajen da ta ce. "Muddin jikinku ya fara haɗuwa, to dole ne so ya shiga mai tsanani, ba zai iya rabuwa da son taɓa jikinki ba, har sai ya tabbatar da kin zama tasa, wannan kuma shi ne zaman aure mai haifar da so,ƙauna,kulawa da juna,ki yi haƙuri idan hakan ta iso gare ki, wannan shi ne auren." Kafin in dawo daga tunanin sakan uku sai dai na ji kamar jikina ba riga, kafin in yi wani abu sai na ji har hannuwan rigar mamana sun dawo cinyar hannuwana, kafin in ƙarasa tuna me nake ciki, sai na ji laɓɓansa a saman ƙirjina. Tabbas ajiyar zuciyar da ya fitar mai ƙarfin gaske ba ta hana ni ɗago kansa ba, na girgiza kaina, wanda idanuwana ke a rufe,jin ya ambaci sunana cikin wata ɓoyayyiyar murya yasa na yi saurin miƙewa tsaye,a tangal-tangal na isa bakin gadona na zauna,a lokacin ne na samu damar gyara rigunan jikina, na ɗago na kalli Yarima Faysal da ke durƙushe a inda na bar shi. An ɗauki mintuna biyar kowa na haka, sannan na ji ya zo ya zauna kusa dani, ya ɗauki wata minti biyun kafin ya yi komai ko in ce yayi magana, ya ɗan ja numfashi a hankali, sannan na ji ya fara magana. "Ya kamata a ce komai ya wuce a tsakaninmu,ya kamata a ce yanzun mun amince da junanmu ko ma samu rayuwar aure mai ƙyau,ni na san laifina ne tun farko, amma yanzu ni na san dole in zama ƙasa gare ki, na yi tunanin shi mulki ko ina ma yinsa ka ke yi ashe ba zai yiwu ba ga iyalinka ba waɗanda ka ke ƙauna, waɗanda su ne rayuwarka gaba ɗaya." Kada ki ji haushina ko kiyi mamakina, wallahi Yasmin ban san aure ba, ban san so ba ban taɓa tsayawa na kalli ƴa mace ba balle har in ji ta a jinin jikina. Yasmin sai ke,ki ture auren haɗi a tsakaninmu,ki mayar da shi mu ne muka ga juna muna so,in ke ba haka ba ne a zuciyarki wallahi ni,ni na ganki na ji ina son ki tun ranar farko. A lokacin da na zo gidanku ganin ke ce ki ka fito matsayin matar da aka zaɓa mini na ji daɗi,sanyi a zuciyata, amma tsananin mulkin da yake a kaina ya hana ni nuna miki. Ke wallahi na ma nuna, tunda da ba ke bace ba,ba kowacce ta isa in tako in bata haƙuri har in bi ta gidan Yayarta. Yasmin na baki rayuwata gaba ɗaya, wallahi ba zan iya rabuwa da ke ba, har sai na ga kin zama jinina, na zama naki. Yasmin ke ce wacce ta taɓa sace zuciyata gaba ɗaya. Ki tausaya ki so ni,ko ƙya dawo mini da zuciyata ta cigaba da tunanin rayuwa da ke. Na san za kiyi shakkun zama da ni, wallahi ki cire duk wani shakku,ki ɗauka kin samu mijin da sai abin da ki ke so za'ayi miki, matsawar bai saɓawa shari'a ba,na karanta takardar Aunty na ji matsalolinki,ki yi haƙuri, zan ɗauki mataki mai ƙarfi a kan abubuwan da ba ƙya so a cikin gidana. Ki yi tunanin yanzun kunnuwa da idanuwan Sarki da jama'a da dama yana kanmu ya kamata mu kuma mu basu mamaki." Ya sauko ya zo saitina ya durƙusa a gabana. "Yasmin ki rufa mini asiri kada ki sa a raba ni da ke, wallahi mutuwa zan yi idan..." Na yi sauri na sauko na rufe bakinsa da tafin hannuna,ni na kasa gane kaina, ina son Yarima ko kuwa tausaya masa nake yi? Ya kamo hannuna ya sumbaci bayan hannun, sannan ya juyo da tafin hannunsa ya miƙo mini. "Na fi son ki amince da kanki,ki ɗora mini amanarki a tafin hannunki ki saka mini ita a nawa tafin hannun,in kuma har yanzu ba ƙya sona ki bani amanar ni zan yi miki abubuwan da zasu sa ki so ni." Na kalli tafin hannun sannan na juyar da kaina. "Please, Yasmin,kada ki guje ni don Allah." Na tashi na koma na zauna a gadona, ya ƙara matsowa ya ɗora hannunsa a cinyata. Na tunano yanda Sarki ya ce mini da irin ƙaunar da ya nuna mini,na tuno Mamee tare da Dadyna, na tunano Aunty Salwa,na ga ita ma kamar yanda aka kawo ni haka aka kai ta, amma yanzu ƴaƴanta uku,shin ko shi ne son? Ko shi ne auran? Na juya na kalli Yarima da ya ƙura mini idanuwa,na tuno irin mulkin da ke gare shi, ban da dukiya da barori,ƙarti da ƴanmata, da tsofaffi, amma yau ga shi yana yi mini magiya da in so shi. Zuciyata a take ta amince da in so shi, na juyo tafin farin hannuna na kalla, wanda na ga tsagu guda uku manya, amma na tsakiyar ya shiga cikin babban ɗaya, ke nan ni da Yarima, sai son da Yarima ke mini ne ya shiga cikin jikina, na matsa, hannuna na ɗora a saman hannunsa sai na ji ya yi ajiyar zuciya ya riƙe hannun nawa sosai. Na samu na karɓe hannuna sannan na koma gadona na ƙwanta a gicciye, ina jin Yarima ya taso ya zauna a gadona, wanda ya lalubi makunnin fitila ya kashe, sai dai na ga duhu a cikin runtsatstsan idanuwana, ina ji ya juyar da ni nayi rigingine ya zuge zib ɗin da na lura ya tsone masa ido, idanuwana na ƙara runtsewa da ƙarfin gaske a lokacin da na ji ya juyar da ni yana saɓule rigar jikina. Na yi saurin ƙanƙame

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});