Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Kasaita Book Two Complete Hausa Novel 1,225 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

alkyabbata a hannunsa, na mayar da kaina na sunkuya a inda ya iso, ya tsaya gabana tare da miƙo mini alkyabbata,na karɓa muna kallon-kallo da shi. Sannan na murɗa ƙofa zan fita, ya juyar da kai tare da ɗan asirtaccen murmushi, wanda da gani tare yake da takaici, saboda fitowar da ya yi tare da numfashi, sai da ya yi irinsa ya kai sau baƙwai, sannan ya ja baya na buɗe ƙofar, ya yi saurin riƙo hannuna. "Yasmin stay with me." Na girgiza kai, na saɓula hannuna na yi gaba, sai dai na jiyo shi yana kiran. No! No!! No!!!" Ɗinsa da ya saba kira,ko waigowa ban yi ba. Da gudu na haye saman ɗakina, ina zuwa na faɗa gadona, sai da na mayar da numfashi ya fi talatin kamar wacce asma ta taso mata, ga idanuwana a lumshe, sannan na ji tunani ya zo mini. Shin ko wannan shi ne SO? Na girgiza kai,ba zan so Yarima ba. To me ye wannan? Oho, abin da zuciyata ke faɗa kenan,nan take ta juya linzamin tunaninta ga abin da ya faru ƴan mintuna da ba su wuce goma ba da suka wuce. Jikina na ji ya kama rawa shi kaɗai, na yi sauri na miƙe tsaye, sai na ji kamar jiri na shirin kada ni, na yi saurin zama, na cire mayafin kaina na jefar da shi ƙasa, na juyar da kaina, kamar wacce ta rasa abin da ke yi mata ciwo a jikinta, na sunkuyar da kaina, gashin kaina ya zubo a fuskata,a inda na tura hannuwana duk biyun cikin gashina. Na samu mintuna goma sha biyu a haka, sannan na ji kamar an sumbaci bayana, na yi saurin ɗagowa, amma ban ga kowa ba, na yi murmushi na miƙe na nufi banɗaki. A banɗaki na cire kayana duka na shiga ruwan wanka mai ɗumin gaske,wai ko abin da nake ji ya sake ni. Tsayin mintuna biyar na yi kawai na miƙe da sauri, saboda tunanin da ya faɗo mini a lokaci ɗaya. Na ɗaura tawul na fito da saurina,wai ji nayi kamar an bugo mini waya,ba abin da ya faɗo mini kuwa sai maganar Sarki. "Zan turo a kira mini ke kin ji." Hankalina ya tashi matuƙa, gobe, gobe lallai zan shiga damuwa kenan in an rabani da Yarima. Na yi saurin tunano Anwar a zuciyata, take sai na ji bana son tunaninsa,na fi son tunanin Yarima,shin ina son Yarima? Ba amsa, na ɗauki rigar bacci ta da su Mansura suka ajiye mini na zura a jikina, da ƙyar na iya ɗaga ƙafata na zura ɗan diras ɗin da ke kusa da ita, na isa ga madubi na taje kaina tare da ƙara gyare shi. Rigar baccin doguwar shimi ce har ƙasa, orange colour da ƴan hannuwanta guda bibbiyu a kowanne ɓangare sai ɗan leshi da ya ratsa saman ƙirjinta, ruwan lemo ce mai santsin gaske. Na feshe jikina da turare madadin in haye gadona sai na ji na kasa, buɗe ƙofar barandar gaban gidan na yi na fita. Kamar yanda na saba a kullum yau ma haka na yi, shi ne in ware hannayena duk biyun,yau ma kuwa na samu sa'ar garin yana fitar da iska mai sanyin gaske, wadda ta taimaka da wasa da gashin kaina, idanuwana kuwa a lumshe suke, amma na kasa tunanin komai a yau. Cikin wani sanyin jiki da sanyin zuciya, na ji tunanin Yarima ya faɗo mini a zuciyata a iya nawa tunanin, sai na ji dama Yarima ya iso yanzu,can ɗayan gefen na zuciyata kuwa, sai ya dinga karanto ni a jikin Yarima,a cikin tunanina ne na ji kamar an bi nawa hannayen a hankali, wani daɗi ya dirar mini a zuciya. Cikin tunanin kuwa na ji an haɗe ƴan yatsun hannuna da nashi waje ɗaya an runtse su, cikin ƙwanciyar hankali ya rungume bayana a ƙirjinsa, sumbatar da ya kaiwa wuyana shi yasa na saukar da ajiyar zuciya mai fitar da sauti. Hankalina gaba ɗaya na ji ya ɗauke har ya zamo na manta mai nake ji a jikina, ƙwaƙwalwata ta fara karanto mini da in buɗe idanuwana da suka yi nauyi in ga ko zan ga Yarima a barandarsa. Cikin sakan biyar na ji hankalina ya dawo a jikina, madadin in jini ni kaɗai ina tunanina, sai kawai na tsinci kaina da jin ɗumin mutum a jikina, gaske ne,ko dai har yanzun mafarkin tunanin ne nake yi,jin sautin numfashi na tashi a kunnuwana yasa na buɗe idanuwana da sauri. Na razana, na tsorata, duk a lokaci ɗaya da na ji bakina ana Yarima, na yi ɗan gaggawar fizge jikina na ja baya, kenan mafarkin tunanin da nake yi da gaske ne, na girgiza kai tare da ɓata fuska. "Me ke damun ka haka? Bana son abin da ka ke yi mini,ba na..." "Yasmin ya isa haka nan,don Allah, na san na yi miki laifi a baya, ya kamata ki zamo mai yafe mini." Ya matso ya tallabo fuskata Wacce gashi ya rufe ta, yasa hunnunsa ya gyara gashin zuwa baya. "Yasmin." "Ni fa ba zan..." "Yasmin kada ki faɗi abin da zai ƙara tayar mini da hankali." "Ka manta gobe ne ranar ƙarshena da kai,ka ga ba zancen wani gyara a nan." "Na sani Yasmin,ki yi tunani kada kiyi tunanin ko yaudara ce tsakanina da ke, wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Tun a ranar da na gan ki a titin Ahmadu Bello Waya, har zuwa yau ban taɓa daina tunaninki ba, matsalar da na samu shi ne ban san gidanku ba, ina shirin in bincika Allah ya haɗa ni da ke a wajen fati,a ranar na so mu daidaita sai ma ta ƙarasa ƙwaɓe mana." Ya ɗan tsaya ya mayar da numfashi, ya saki fuskata, ya durƙusa a gabana. "Please Yasmin ki taimakeni,ki zauna da ni." Na tsugunno nima na fara magana a hankali, kamar yanda yake yin tasa. "Ba zai yiwu ba Yarima,ba zan iya zama da kai a wannan matsayin naka na mulki ba,ko tari na yi duk gidan nan an sani, har zuwa gidanku." Na miƙe na koma ɗaki na zauna gefen gadona. Mintuna baƙwai da zamana ya shigo ɗakin shi ma ya iso gaban gadon ya tsaya. "Ba zan taɓa cewa na haƙura da ke ba, ba kuma zan gaji da baki haƙuri ba, ba zan taɓa mantawa da cewa ina son ki ba, Allah ya gani, na yi miki abubuwa ne domin ki so ni, nima amma na yi kuskure." Ya juya ya tafi ya ja mini ƙofar da har sai da na ɗan tsorata. Na koma na ƙwanta a rigingine, na dafe kaina da hannayena na yi tsaki, na juya na tashi zaune, na mayar da numfashi na tashi na je na rufe ƙofar gaba, na koma na kulle ƙofar ɗakina, na zare makullin na kashe dukkan fitilun ɗakin, na ɗaga filo na saka makullan, na koma na shige bargona, kaina ne kawai a waje, inda idanuwana ke kallon duhuwar ɗakina, duk da hasken da ke shigowa ta kafar labulaye ya ɗan taimakawa ɗakin da rage duhu sosai. "Yarima!" Shi na faɗa a fili, na tuna da maganar Sarki, na tunano Mama da ta ce Sarki ba ya magana ya tayar da ita, hawaye na ji sun gangaro mini,wata zuciya ta tambaye ni, "Shin ko

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});