Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

Kasaita Book Two Complete Hausa Novel 1,217 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

jikina da na ji hannayensa na ƙoƙarin ɓalle ɗan masankallin da yake riƙe da rigar mamata, na runtse hannuwan gam da na ji ya kai wa tsakiyar bayana sumbata, ban dawo daga tafiyar balaguron da na yi ba sai naji ya haɗani ya rungume a ƙirjinsa ta bayana, gashin da ke ƙwance a ƙirjinsa ya tsirar mini fatar bayana, tabbas na fitar da numfashi wajen kala goma a lokaci ɗaya, amma har a yanzun na kasa gane me ye so da ƙauna. **** **** **** Motsin da na dinga ji yana tashi sama-sama cikin hankalin, shi ya farkar da ni daga baccin da nake yi, na buɗe idanuwana da ƙyar sai na ga hasken fitilar gefen gadona, amma ta ɓangare ɗaya, na ɗan juyar da kaina a hankali gudun kada inyi motsi da ƙarfi. Yarima na gani tsaye gaban durowata ɗaure da tawul a jikinsa. Kunya ta saukar mini tare da wani ɗan saurayin murmushi, duk da na san hankalinsa ba kaina yake ba, ina kallo har na ga ya janyo wasu kayan daba zan iya shaidasu ba, saboda ɗakin babu haske sosai, ina kallonsa ya iso wajen gado ya ajiye su a inda na yi saurin runtse idanuwana ganin yana shirin cire tawul ɗin jikinsa. Cikin dabara na mayar da kaina inda yake da farko,bai fi minti ɗaya ba na ga ya nufi gaban madubina ya ɗauki turarena ya fesa, wata wauta irin ta Yarima har da sumbatar ƙwalbar turaran nawa sannan ya ajiye kai tsaye ya nufo inda nake ya zauna kusa da ni sosai. Na yi saurin lumshe idanuwana tamkar bacci nake, ina ji ya dinga shafa kumatuna, ya shafi gashin kaina, ya sunkuyo ya sumbaci kumatuna, yasa hannu ya dinga zagaya laɓɓana. "Beautiful,Ina roƙon Allah ya taimakawa rayuwarki, yasa ke ce matata har in mutu, ya sa ki haifa mini ƴaƴa masu tarbiyya kamar ki. I love You." Ya ɗaga hannuwana da suke waje ya janyo bargo a hankali ya lulluɓe ni, sannan ya sumbaci kafaɗa ta. Ina jin motsin janyo durowa a hankali, bayan ƴan mintuna kuma sai na ji an rufe ta, ina jin tashinsa can kuma na ji ya dawo ya sumbaci bakina. "I miss You." Ya zaro hannuna ya tura a ƙirjinsa. "Kin ji yanda ƙirjina ke bugawa don zai rabu da ke." Ya miƙe ya tafi. A hankali na buɗe idanuwana sosai amma zuciyata ta cika da tunanin ina Yarima za shi a cikin daran nan? Na ɗauki wajen minti uku ina tunani tare da al'ajabin fitar Yarima da dare kamar haka,ban kai ga tunani ko baiwa kaina amsa ba, sai kawai na ji ƙarar tashin mota, hankalina na ji ya tashi matuƙa, wannan ne yasa na yi saurin ƙwaye bargon da ke lulluɓe da ni cikin sauri na miƙe saboda kawai in ga inda motar za ta tafi a tsohon daran nan. Cikin lokaci ɗaya abubuwa uku suka saukar mini shi ne mayar da ni baya da aka yi aka ƙwantar da ƙarfi, al'ajabi alamar tambaya. Al'ajabi shi ne ganin jikina ba kaya. Tambaya kuwa,me ya sameni naji jikina ba ƙarfi? Mayar da ni baya kuwa shi ne jikina na ji ya riƙe gam, ga mugun ciwo da na ji yana yi. To me ye kuma? Kafin in karanto amsa kuwa, sai gani ina kokawar jan bargo da lulluɓe kaina saboda firgita da nayi jin wata ƙara na tashi kusa da ni, cikin rawar jiki na samu na lalubo makunnan da ke ƙarƙashin filona tare da karanta Ayatul kursiyu na daure na kunna fitilar ɗakina. Hasken da ya gauraye ɗakina ya yi sakan uku kenan da kamawa amma sai ta cikin bargo na iya leƙo idona ɗaya, da ido ɗayan nan na dinga bin ɗakina da kallo,in ga ta inda ƙarar nan ke fitowa,saman ƙaramar ƴar durowar da ke kusa da gadona (side bed) na ga ɗan ƙaramin agogon tsugunno, sai a lokacin na ji ɗan kuzarin miƙa hannu in ɗauko shi domin kashewa. *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 8 Lokacin da agogon ya nuna kuwa biyar saura ƙwata na asuba. Me ya fitar da Yarima ƙarfe biyar saura? Ko dai suna da wani abu ne na sarauta wanda suke yi daidai wannan lokacin? Ni kaɗai ke tunanina, da agogo a hannuna, na ɗan ɓata raina, na girgiza kaina, shi kenan rayuwata ta ƙare, sai da na amince da Yarima, sannan wani sabon halinsa ya bayyana. Cikin sanyin jiki da cikowar hawaye a idanuwana na mayar da agogon na ajiye saman durowar,farar takarda mai rubutun baƙin biro mai ruwan (ink pen) idona ya gani a gefen durowar, na yi ɗan saurin miƙa hannuna na ɗauka, cikin ɗan rawar jiki na kai idanuwana a jikinta. _Barka da Asuba_ _Mace tagari,macen da kowanne namiji na duniya yake son ya mallaki irin ta,kin zama abin alfahari a gare ni._ Na gode. _Na je masallaci, amma komai zai biyo baya, ina neman afuwarki, saboda ni kaina bana son al'adar nan da zata biyo baya yanzun ba da daɗewa ba, ba wai naƙi tsayawa in taimaka miki ba, na kasa tsayawa ne saboda abubuwa guda uku,kunyarki,girmanki, wanda ba za su bar ni haɗa ido da ke ba,sai kuwa masallaci saboda ba a tayar da sallah sai na isa._ _Rashin ganina a masallaci zai iya haifar da ɗan ƙaramin tashin hankali, saboda za su yi zaton ko banida lafiya ne, godiyata ba zata iya samun ki ta baki ba, saboda ban san wane bakin ne ya cancanci ya yi miki godiya ba,ni dai na yanke hukuncin yi miki addu'a da Allah yasaka miki da aljanna firdausi mani'imciya._ _Husband._ Na jefar da takardar na sa tafukan hannayena na rufe fuskata, saboda kunyar da na ji,a hakan ma sai na ga kamar yana tsaye yana kallona, wannan yasa na yi sauri na lalubo makashin fitila na kashe,bargo na ja na rufe har kaina, ba wani tunani da ya faɗo mini sai na ya zanyi in haɗa ido da iyayena da shi kansa Yarima? Tunani ya faɗo mini,na inyi sauri in shirya in ɓuya kafin Yarima ya dawo, amma kuma abu ɗaya yana neman gagara ta, shi ne tashi tsaye, amma duk da haka na samu na yi ƙarfin hali na tashi zaune, na yi shiru ina sauraran ko zan ji motsin Yarima,wai ni gudun kada in tashi ban sani ba ko yana laɓe yana kallona. Tsayin minti biyu na ɗauka sannan na ɗan janyo jikina na kunna fitilar gefen gadona, haske ya gauraye ɗakin nawa,a nan ne na hango rigar wankan da Yarima ya ɗora a saman gefen gadona, na ja jikina zuwa inda take, nasa hannu kenan na ɗauka sai na ji motsin murɗa ƙofa, na yi sauri na janyo rigar na dawo na kashe fitila na koma na ƙwanta. Muryar da na ji tana kirana, "Gimbiya, Allah ya taimaki Gimbiya." Da naji na gane ta mace ce, a cikin rufar da nake na ce, "Wace ce?" "Allah ya taimaki Gimbiya uwar kowa, jakadiya ce, mai girma Yarima ya ce in zo kina kirana,wai zan taimaka miki da wasu ayyukan." Nan take na ji hankalina ya tashi, me Yarima yake nufi? Zuwa ya yi ya gaya mata abin da ya faru da ni? Nan take haushi ya kama ni, da nayi tunanin korar ta

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});