Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Kasaita Book Two Complete Hausa Novel 1,222 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kenan. Bai fi mintuna biyar ba da shigowar mu ɗakin ba wata ƴar ƙararrawa ta kaɗa cikin sauri na ga Yarima ya fita falon da muka baro,mu kuwa muna ɗaki Yarima na ɗan shirya mana kayanmu. Jin an ɗauki ƴan mintuna yasa na fito falon da ɗan saurina, fararan mutane ne biyu Turawa, sanye da farar rigar shirt da bulu ɗin wando, sai baƙaƙen takalma a ƙafarsu, wannan ne ya nuna mini alamun su ne ma'aikatan hotel ɗin da muka sauka. Baki ɗayan hankalinsu ya dawo gare ni,ni kaina sai na ji kunya ta kama ni kallon da na ga suna yi mini, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci Yarima ya nufo inda nake. "Shiga ciki." Ya faɗa a daidai lokacin da ya iso gareni. Na shiga ciki ina ɗan murmushina na mamakin yanda Yarima ya nuna kishinsa a fili. Wajen yammarsu, wacce a tamu yamman za mu iya kiranta ƙarfe biyar da wasu mintuna na yamma. A lokacin ne muka gama komai muna zaune a falonmu mu dai ga mu nan, ba ka cewa ƙiyayya ba kuma za ka kira mu masoya ba, tunda kowa a kujerarsa yake a zaune,ni zan iya cewa kishingiɗe nake a tawa kujerar duk maganar da ya yi idan ta amsa ce in bashi amsarta,in naji zan iya. Ana cikin haka hankalina ya kai ga talabijin ɗin da ke ta aiki ita kaɗai, na yi saurin tashi zaune har da ɗan salatina. "Me ye?" Ya tambaye ni. Har sai na ji na ɗan ji kunya, "Wa ye wannan? Ɗan uwanku ne?" "A'a. Ya naga kina ta murnar ganinsa?" "Ɗan wasa ne na finafinan Indiya." Ya gyara zama sosai. "Ya sunansa?" Na ce, "Sharukhan." "Haka nan ki ke son ganinsa?" "Ina bala'in son shi ne, ya iya acting." "Me kika ce?" "Cewa na yi ina son shi." Ya yi murmushi mai fitar da sauti. "Ko wajensa za ki koma?" Nan take na juyo na kalli fuskarshi,ko kallona ma bai yi ba, balle ya bani wata amsa, na miƙe na nufi cikin ɗakina na ƙwanta,bai fi mintuna sha biyar ba sai gashi ya shigo, ya iso ya zauna gefena. "Ban fahimci abin da ki ke nufi da tasowa ki ƙwanta ba, daga na yi miki maganar mutumin da ba muharramin ki ba?" Ya juyo sosai ya sumbaci kumatuna. "Ki yi haƙuri in kin ji ba daɗi." Na ɗan yi murmushi. "Ban ji komai ba, na dai zo na ƙwanta ne kawai." "To taso mu sauka ƙasa ki ga mutane kafin gobe in kai ki wurare da dama waɗanda na sani." Na yi murmushi na tashi zaune, da niyyar in tashi mu tafi, ya riƙe hannuna. "Kisa doguwar suit ɗinki,saboda jama'a." Yau ƙwananmu huɗu a ƙasar Greece,a ƙwanakin ukun da muka fara fita ba inda Yarima bai kai ni ba, wuraren wasansu na yara, amma su manya ma na zuwa,a nan ma ya ga na fara sakin jiki da shi, balle da aka ɗora ni wata mota mai sa jiri ina saukowa na kasa tafiya, sai dai Yarima ne ya ƙwantar da ni saman kafaɗarsa muka samu wajen zama yana yi mini dariya. Wani abin burgewa irin na ƙasar Turawa, shi ne ba wanda ya damu da abin da ka ke ciki, balle a tsaya kallonka, shi kansa Yarima sai yanzun na ƙara gane cewa dogarawan da ke bin shi a baya suke ƙara masa girman kai, amma yanzun ba ki gane shi ko ɗan waye. A ƙwanakin nan huɗu kuwa ba wata alama da Yarima ya nuna mini sai ma ɗan tilasta ni in yawaita shiga ruwan ɗumi cikin hikima irin tasa. Tabbas Yarima na sona,ni kaina na amince da hakan,ni kuwa zuciyata har yanzun tana baƙunta da shi, shi ne ta kasa tsayawa ta saki jikinta da shi, har ta gano irin son da take yi masa. Yanda nake ƙwance a gadon da ke bakin ramin wanka,in ka hango ni ba ni da maraba da Turawa, saboda kayan jikina,siket ne baƙi da farar riga a jikina, wanda gilashi ne manne a idanuwana, irin ɗaurin ɗanƙwalin Turawa nima shi na yi, shi ne ka ɗaure gefe-gefe amma tsakiya a baje saman baya. Kaina ƙwance yake gefe, ina kallon cikin ramin wankan,babu inda idanuwana suke sai kan Yarima da ke ta wasan wanka a cikin ruwan, duk da duk ɗan lokaci ya zo bakin ruwan ya ɗan watso mini shi kaɗan,in ɗan yi ƴar ƙarar ƙissa, shi kuwa ya yi ƴar dariya ya ƙara komawa sosai cikin ruwan. Ganin inda ya nutsa kansa ya tsaya cak ruwan baya motsi irin ana wanka da shi, shi yasa na ɗan ɗaga kaina sosai ko zan ƙara hango shi, amma ba na ganin sa ko kaɗan, cikin sakan ɗaya sai na ji kamar kaina ya sara, irin na tashin hankalin nan, ban san lokacin da na miƙe tsaye ba, isowa na yi bakin ruwan na tsugunna duk gwiwa biyu ina jira,in ga ɗagowar Yarima. Tun ina ganin kamar wasa, har na ga ya ƙwashe mintuna,nan take na ji kamar kaina ya fara juyawa, na waiga ban hango wani wanda ya yi kama da ɗan Afrika ba, ballantana in kirawo shi, abin ka ga ƙasar Turawa, kowa da tashi hidimar ba ma wanda hankalinsa yake a kaina. Juyowar da zan yi sai na hango Yarima ƙwance saman ruwa, amma ta bayansa kenan kanshi da cikinsa duk a ruwan suke, na miƙe tsaye na yi kamar in yi ihu, to wa zan yi wa,ni kuwa dalilina na ƙara ruɗewa a irin ƴan fina-finan da nake kallo na san in an ga mutum a saman ruwa to ya mutu kenan. Ganin ba zan iya zuwa cikin hotel ɗin ba in kira ma'aikatan yasa na ji wani ƙarfi ya zo mini ban san lokacin da na shiga cikin ruwan nan ba sai dai gani na nayi ina kokawa da gangar jikin Yarima,manufata in juyo fuskarshi ta kalleni ta hakan zan gane ko yana da rai. Duk cikin mintin da bai wuce ɗaya ba na yi haka,babu wani alamar rai a jikin Yarima a lokacin da na juyo shi nan take na ji zazzafan gumi na tsiyayo mini ta saman gashina, ban da mugayen hawayen da ke shatata ba tare da an rera masu waƙar kuka ba. Ƙarfi na ji ya ƙara zo mini cikin rawar jiki na ji na janyo shi zuwa bakin ruwan, sannan na yi ta maza na ɗora shi saman gefen ruwan, da rawar jikina na zagaya na fita daga ruwan. Sannan na janyo shi. *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 11 Amma ina namiji ba mace ba sai ma ya ƙara komawa cikin ruwan nan, take na sa ƙara mai tsanani, na ruga a guje ina cewa a taimaka mini da harshen Turanci, ma'ana. "Please help me! Help me!!” Nan da nan aka zagaye shi ni kuwa gani nake duk ba su isa ba, tunda ba ma'aikatan hotel ɗin, da gudu na isa falon da ake fara karɓar baƙi (Reception) da harshen Turanci na yi masu bayani, kafin minti biyu har sun riga ni isa inda yake, ina isa na cakume shi, cewa nake, "Yarima ka tashi! Tashi!!...” har sai da suka ɗan riƙe ni, sannan aka danna ƙirjinsa da cikinsa sai ruwa ya ɗan fito ta bakinsa. Na fizge

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});