Chapter 4
Chapter 4
ko?" "Mama,ki taimaka,in Sarki ya haƙura ma zamu Greece Honeymoon da ita." "In tana son ka ko, na san zai sa a tambaye ta,in ta nuna a'a, to kai ka sani." "Mama zan yi ƙoƙarin da Yasmin zata so ni, wallahi na yi miki rantsuwa da Allah." "To na ji kayi ta addu'a ka san halin Sarki, baya tayar da magana in dai har ya furta ta da bakinsa,ka san dai ba sabon abu ba ne ba wannan. Yanzun da ƙafar ƴar mutane ta lalace ya za mu cewa iyayenta?" "Mama shi kenan mu zamu tafi, zan dinga zuwa." Ta yi dariya, "Dama ni ce Yasmin in ce sai Anwar " Ta cigaba da dariya. Suka fito,ni kuwa sai ma na nuna ban san abin da suke yi ba. "Ƴan gidan tun daga nesa na hango su tsaye ana ta murna,kai har da mazajen sashen gidan Yarima, Allah Sarki, Mansura har da kuka,yarinyar nan ta shiga raina nima,ko don yadda take nuna mini ƙauna,wai sai da muka kusan wajen sannan aka ƙara sakin labulan nan baƙi, duk da dama gilashin motar ma baƙi ne, sai dai ka ga mutum amma shi baya ganin ka. Ya juyo sosai ya riƙe hannuna, "A tanadar mini abinci,yau gidanki zan yi hira, saboda in taya ki zama." Na rausayar da idanuwana na yi murmushin da na san gefen kumatuna suna lotsawa. "Ka fi ƙarfina." Ya yi saurin matsowa. "Kada ki ƙara faɗar haka, har kin janyo ma ba zan iya wucewa gidana ba,naki gidan zan sauka." Ka rufa mini asiri." Sai na ga ya yi saurin sakin hannuna ya matsa baya, wacce ta yi daidai da buɗe ƙofar motar da muke ciki. Mun gaisa da jama'a da dama, sannan muka haye sama ɗakina, sai na ji na kasa komai. Wannan yasa na dinga haɗa shi da Allah ya tafi ɗakinsa,an jima da dare ya dawo hirar sannan ya amince. Ƙwana uku yana zuwa taya ni hira, sai sha biyun dare yake tafiya, a ranar na huɗun da goma na dare na ji wayar hannuna ta yi ƙara, na ɗauka a tunanina Aunty ce, sai na ji muryar Yariman da na gaji da jira, na yi ƙwalliyata mai ƙyau, saboda shi amma shiru, wanda na kasa zaune na kasa tsaye saboda rashin zuwansa,ni kuma na kasa zuwa inda yake in dubo ko lafiya. A hankali yake magana cikin muryar da zata iya tayar maka da hankali, idan ka ji ta, saboda tafi yanayi da ta marasa lafiya,a take kuwa na ji hankalina ya tashi. "Yasmin na kasa zuwa wajanki." Cikin yanayin tashin hankali na tambaye shi, "Ba ka da lafiya ne?" "Eh, to ni ya zan ce miki, zaki iya zuwa gare ni yanzu? Yasmin forget the fast please." "Zan yi tunani." "Please Yasmin." "Okey,na ji." Ya kashe wayar, na miƙe tsaye daga zaunawar da na yi a gado, na nufi madubina, na ƙara feshe jikina da turare, na kalli kaina irin kayan da ke jikina, riga da siket ne na Turawa amma buɗaɗɗen siket ne, ga shi da tsayi har zuwa ƙwaurina,bulu ne mai haske (light blue). Sai ruwan ja amma mai haske light pink mai dogon hannuwa ce, amma daga ƙarshen hannun buɗaɗɗu ne, sai buɗaɗɗan wuya, wanda ya nuna sashen bayana a buɗe yake, haka gaban rigar (roundneck) , zagayayyen wuya ne, da wasu zarirrika biyu a gaban rigar waɗanda an yi su don ƙwalliya kawai. Takalmin ƙafata masu ɗan tsini ne,kalar rigar jikina, amma ɗan mayafin da aka sakowa kayan irinsu ɗaya da siket ɗin,bulu mai haske kenan, sai da na feshe gashin kaina da turaran shi, sannan na mayar da mayafi na yafa kalar rigar jikina,alkyabbar da na rufa a sama, ita ma pink ce, sai da na kuskura man ƙamshin baki mai ƙamshin (mouth wash,rinse), sannan na rataye wayata mai ruwan alkyabbar a hannuna. Na murɗa ƙofa na shiga,ƙasan ba kowa sai fitilar nan ɗaya da aka saba bari duk dare na Ubangiji, na haye matattakalar bene,domin in isa ɗakinsa. Falon sama na same shi ƙwance cikin kujerar hutawa farar shirt ce da wando a jikinsa, amma ya ɓalle maɓallan gaban rigar, sai farar singilet ce ta rufe fatar naman jikinsa. Wayar hannu ita ce a saman ƙirjinsa, wacce kalar jikinta fari ne daga ƙwancen ya juyo ya kalleni. "Yasmin." Shi kaɗai ya faɗa, amma bai tashi ba, na iso na tsugunna gabansa. "Ba ka da lafiya ne?" Na dafa saman goshinsa, ya lumshe idanuwansa. "A'a." "Yana ga jikinka ya yi laushi?" "Ke ce." "Me ya faru kuma?" "Gobe ne fa Sarki ya yanka mini." Ya yi shiru nima sai na ji gabana ya faɗi. "Na yi waya da Mama yanzun kafin in yi miki, amma ta ce Sarki yana nan a kan abin da ya faɗa." *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 3 "To me ye na damuwa?" "Na san halin Sarki ba tayar da magana." "Shi ne na ce me ye na damuwa? Iyaka ka auro wacce ka ke so,dama ni ma takura ka aka yi ka au...." Ya tashi zaune tamkar tashin wanda ba shi da lafiya. "Me ye abin damuwa Yasmin? Ni ke ce abin damuwata." Na miƙe tsaye na ja baya tare da dafa goshina, na juya kamar zan tafi. "Yasmin,No! No!! No!!! I love you. Na juyo da kaina na gan shi a tsaye yana kallona, na girgiza kaina na juya zan tafi. "Please, Yasmin." Na tsaya cak a lokacin da na ji wani abu yana yi mini yawo a cikin jikina, wanda ba zan iya faɗar yanda yake ba, na mayar da idanuwana na lumshe tare da fitar da numfashi sama-sama,shin me ye wannan? Ban kai ga tunanin amsar ba, na ji an rungume ni ta baya. Ajiyar zuciya uku ce ta fito gaba ɗaya a cikin sakan ɗaya, kafin in yi tunanin ya zan yi in ƙwace jikina daga Yarima, sai na ji ya zame alkyabbar da ke sanye a jikina zuwa bayana, madadin buɗe bakin da na yi inyi magana, sai dai bakin ne ya tsaya a buɗe sakamakon sumbata da ya kai a buɗaɗɗan bayana, wanda riga ba ta ƙarasa rufe shi ba. Madadin inji ya sake ni, sai na ji ya cigaba da sumbatar wuyana zuwa bayana. Me ye wannan ke yi mini yawo a jikina? Lallai ba zan iya gano ko me ye ba,saboda ya fi ƙarfin in iya faɗarsa, jin alkyabbata ta faɗi ƙasa, ita ta dawo da hankalina a jikina, wanda na ji sam ba shi da ƙarfin komai. Ba zan iya wata magana ba, sai dai na yi ɗan ƙoƙarin da bai wuce na mirginawar marar lafiya ba, na zame jikina, ina girgiza kaina, idanuwansa a lumshe suke inda yake saukar da numfashi sama-sama kamar mai asma farkon tashi. Numfashin haɗe yake da faɗar, "No! No!! No!!!" Wacce ba zan iya ƙirga ko nawa ce take fita daga bakinsa ba, wannan ne ya ba ni damar jan jikina in tafi gidana, wanda ko alkyabbar ban tsaya ɗauka ba. Sai da na tsaya jikin ƙarfen matattakalar bene na ɗan huta,don ƙarfi ya samu a jikina, sannan na samu na iya gangarewa ƙasa, har na kai ƙofa na murɗa na juyo muryarshi. "Yasmin." Na waigo na kalleshi tsaye yake a ƙofar benen riƙe da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24