Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

Kasaita Book Two Complete Hausa Novel 1,242 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

amma sai na yi tunani sai fa an taimaka mini, da su Mansura su taimaka mini kuwa ai gara jakadiya, tun da ko banza ta haife ni. "Shigo mana, ba na jin daɗi ne." Na laluba makunnin fitila na ajiye kusa da ni, sai da na zauna nasa rigar wankan sannan na kunna, da rawar jikinta ta iso gaban gadona ta zube ƙasa,tana ɗan sussunkuyar da kai, yanda na ga tana yi shi ya sa nake tambayar kaina da cewa ko Yarima ya gaya mata ne? Kamar ta san tambayar da nayi, sai na ji tana wasu ƴan surutai, "Ai dama duk ƴa tagari shi ne ta cika ɗakinta,a yanzu ba ke ba koni na zama abin girmamawa, tunda matar ɗana ta cika ɗakinta,yau kam shagali ya same mu,ai mu yau sai yanda hali ya yi." "Bana son magana ki tashi ki yi aikinki." "To, to ai komai ki ka ce shi za'ayi." Ta miƙe da rawar jiki, sai na ga ta ajiye wasu ƙwalabe, sun kai huɗu ban dai tsaya tambayar ta ba ta shige banɗaki. "Ai ya tara mana ruwan ɗumin,a gaishe da ɗana,ai fa na raine shi tun ranar da aka haife shi,dama ai in ka raini yaro a gidan sarauta, to kai za kayi masa jakadiya a al'adance, saboda kun shaƙu da junanku, yanzu ne dai ake son rai, sai wasu su dinga ɗaukar wata,kin ga ai ta nan za'a iya haɗa kai da ita a cutar da shi, ke kuwa da kika raine shi tamkar ɗa yake a gareki, ba ke ba cutarwa a tsakaninku. Bari dai ki gani in yi sauri, kada a fara taruwa,ai ni murna ce ma ta hana ni yin komai,kin ga yanzun wallahi duk abin da ki ka faɗa ta zauna, komai ki ke so kuwa shi za'ayi miki,ai daga yau kin zama shalelen Sarki. Duk maganganun da take kuwa cikin rawar jikin ɗaukar ƙwalaban da ta ajiye ne, da rawar jiki ta nufi banɗakin. Kafin ta fito na yi ƙoƙari na miƙe, wanda cikin sauri na na mayar da bargo na rufe zanin gadon da na tashi a kai,dama abu ga zanin gado fari ƙal, cikin dabara na dinga jan zanin gadon, amma ya ƙi fita, ina haka sai ga jakadiya ta fito. "Dama na tanadi kayayyakina,ai ina sai kin juya Yarima kamar waina,na dinga gyara ki kenan, yanzun haka waɗannan sai da na je ƙasar Sanigal na siyo su wajen jika ashirin da biyar,dama burina ɗana ya samu mace tagari." Ni kuwa kamar an kulle bakina, ita kaɗai ke surutanta tana rawar jiki, can sai ta lura da ɗan jan zanin gadon da nake yi. "Ina,ai sai wanda ya zaunu gidan sarauta ya san yanda ake shimfiɗa zanin gadon nan ranki ya daɗe." Tun ta ɓangaranta na ga tana ɓalle wasu abubuwa, ɗora su da tayi a gado sai na ga dogayen abu tamkar ƴar fill ɗin ɓalle kaya (fila) ta ɓalle har ta zo inda nake, tana gamawa na janye zanin gadon na ƙudundune shi. "Don Allah jakadiya kada ki bar kowa ya gani,ki ɓoye mini shi, zan tambaye ki anjima,ko da yake ba ni shi nan ma in shiga da shi in wanke." "A'a Gimbiya me ye amfanina." "A'a bai dace ba, ba ni." "To,ai..ai...ai.....dashi ake... ake...imm...im ki dai shiga wankan in ɓoye miki,ai...ai...ɗana ya kamata dai ya wanke ke dai shiga Gimbiya." Ban dai fahimci abin da take nufi ba, haka nan dai na shige banɗakin na ƙyale ta a tsaye tana ƴan soshe-soshe, ina shiga na ji wani irin mugun ƙamshi, wanda dole idan ya shiga hancin mutum sai ya lumshe idanuwa, daga nan ma zai iya tafiya mafarkin tsaye. Na buɗe idanuwana, na ce lallai jakadiya tana son Yarima zan ce,ko kuwa ni take so? Har na ɗaga ƙafa zan shiga cikin ruwan da ke cike da bahon wankan wanda kalarshi ta koma ja-ja ja-ja, sai na tuno cikin surutan jakadiya na ji tana cewa lallai sai an fara yin wankan sabulu sai ayi wanka, kuma na tsarkake jiki, daga baya sai a shiga ruwan bahon, ana ɗaukar minti talatin har fi a ciki, saboda komai na sinadarin ƙamshin ya ratsa jiki. Na girgiza kaina,lallai harka da irin su jakadiya akwai ilimantarwa, zan kuwa ja ta a jikina ta dinga koya mini sirrikan zama da miji da jama'a,lallai sarauta sai ɗanta,sai kuwa wanda ya gaje ta, wannan turare kullum kana wanka da shi,ai sai ka hana mijinka fita ƙofar gida. Bayan kamar mintuna hamsin da uku na fito daga banɗaki, wani al'ajabi ya dirar mini a take, tawul ɗin da ke hannuna ina tsane kaina na saki ƙasa,shin me ye haka kuma? Ɗakina na ga ya canja gaba ɗaya, wajen zaman gadon da zanin gadon sababbin wasu zagayayyun filalluka sun kai goma sha biyu aka zuba a saman gadon, kowanne an yi masa mazauninsa, shi kansa labulan gadon ya koma kalar zannuwan gadon, haka labulayen da ke zagaye a ɗakin nawa, na ƙara zagayawa sai na ga wata irin lafiyayyiyar kujera zan ce ko gado ƙarama daga gefe, ta sha dardumai, daidai da kafet ɗin gaban gadon an canja mini shi, da komai ruwan fari ne a ɗakin, yanzu kuwa ruwan bulu ne mai haske, ma'ana tamkar fararan kayan da suka sha bula. Mata ne su uku zaune a ƙasa, ban da jakadiya ta huɗu, wani ƙamshi ɗakin ke yi wanda kuma ya sha bambam da na banɗakin da ya ruɗani, saboda mamaki har ma na kasa tunawa da komai,maganar da suka ɗauki yi gaba ɗayansu ita ta dawo mini da hankalina a jikina. Irin kirarin nan da ake wa ƴaƴan sarauta shi na ji suna yi mini,wanda ba zan iya riƙe komai daga cikin abinda suke faɗa ba, na isa wajen abin sallata tare da saka rigar sallata, na sa hijabin sallah, waɗanda na tarar duk an canja mini su, hatta da mazauninsu ma sai da aka canja. Sai a lokacin na ɗago kai na kalli jakadiya cikin ɗan jan kai irin na masu mulki na yi masu magana. Jakadiya ku ɗan bani waje in shirya ko?" "Ki dai kimtsa Gimbiya, amma ai masu shirya ki sun iso suna ƙasa." Wannan maganar ta jakadiya tana yi tana tafiya, wacce a lokacin da ta kai ƙofa ta gama yin ta, wannan ne ni kuma bai bani damar mayar mata da amsa ba,ko kuwa in ce tambayarta ba, da cewa su wa zasu shirya ni, wanda ya wuce ni kaina?. Kafin in gama sallah da lazimin da na kan taɓa bayan kowacce sallar farillah tawa, jakadiya ta leƙo ya kai sau taƙwas a inda daga ƙarshe ta ga na kammala na miƙe tsaye ina ninke hijabin sallah ta. Wannan kuwa ya yi daidai da shidda da ƙwata na safiyar asabar. Ko mai ban ƙarasa shafawa ba na ga jakadiya ta shigo tana cewa, "Ku shigo ku shigo mana." "Me zasu yi miki in sun shigo?" "Dama masu shirin ne." "Shirin me?" "Jikinki,daga gidan Mai Martaba aka turo su." "Ba na so kina jina,ku fita." "Allah ya huce ran Gimbiya ai.." Wayar da ke kan ƴar durowar gefen gadona ta ɗauki ƙara. Cikin gaggawa jakadiya ta isa ta yi saurin ɗauka ta kanga a kunnanta,ganin cikin saurin da bai wuce na sakan ba ta durƙusa

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});