Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 20

Chapter 20

Kasaita Book Two Complete Hausa Novel 1,222 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ƙwantalan ƙurji a dukkan jikina ballantana tabo, sannan ko'ina na jikina farinsu ɗaya,in an ɗauke saman tsokar ƙirjina. Na shige ƙwami na zauna dirshen sannan na saki famfunan dukkan biyun ɗaya na zubo da ruwan zafi ɗayan kuwa na sanyi yake ƙwararo min, cikin ɗan gaggawa na gama wankana,gudun kada Yarima ya jira ni da yawa, saboda na san shi mutum ne mai son jam'i. Ina fita sanye da rigar wanka,shi kuma yana sallame sallah. A zuciyata na ce har ya ƙagara. Na ɗauki kayana riga da wando,wandon ruwan baƙi ne rigar kuwa mai dogon hannu ce ruwan madara, sannan rigar ba ta wuce ƙugu ba, na fito na zauna gaban madubi na yi gaggawar shafa ɗan Wetlips kawai nasa a laɓɓana, na taje gashin kaina na ɗaure shi na sakeshi a baya, sai kuwa turaran da na feshe jikina da shi. Alkyabbata na zura domin gabatar da sallah, ina isa wajen da na keɓe mana domin sallah na ga Yarima ya miƙe, sannan ya ce mini "Bismillah." Sai wannan lokacin tunani ya faɗo mini cewa nafila ce Yarima ya yi irin waɗannan halayyar ta son Addininsa yana ba ni mamaki, saboda ban taɓa tunanin yana ma sallah ba, ballantana ya iya riƙe Addininsa da hannu bibbiyu, balle da na je gidan yari na ga irin yanda yake baiwa jama'a wahala, ga mulki har na fitar hankali. Bayan mun gama ne na ji ya ɗaga hannu sama yana jero sunayen Allah gaba ɗayansu daga nan kuwa na ji ya faɗa ga addu'ar Allahumma izzal Islama wal Muslimin har ƙarshenta, sannan ya rufe da wata addu'a wacce tun ina yarinya na ji ana yi mana ita, abin da ya bani mamaki kuma sai na ji ya rufe da ɗayar ma wacce zan ce kowa tun yana yaro ma ya iya ta. _Rabbana atina fidduniya hasanatan wafil alkhirati hasanatan waƙina azaban nari._ _Rabbana latuziƙ ƙulubana ba ada izhadaitana wahablana min ladin ka rahamatan innaka antal wahab._ A take na tuna da malamin islamiyyarmu da yake ce mana ana son duk sallah a dinga karanta ta,falalarta Allah kaɗai ya san yawansa, sai dai yawan yin ta na kawo arziƙi duniya da lahira. Hankalina na ji ya ƙara nutsuwa a kan Yarima,ganinsa yanda yake kula da Addininsa. Muna kammalawa ya miƙe ya gabatar mana da sallar isha'i ni dai gaskiya na ji mamaki matuƙa a kan yanda na ga Yarima na tafiyar da rayuwarsa,in na yi la'akari da yanda yake a baya, mutumin da ko motsi ma baya iya yi sai dai a yi masa. Bayan kammala addu'armu ne na ga ya tashi ya buɗe aƙwatinsa ni kuwa sai bin shi nake da kallon mamaki, wasu kaya na ga ya ɗauko da alama dai na mata ne, ya zauna saman gado sannan na ji ya kira ni na tashi na je inda yake, nima na zauna a gefensa. "Waɗannan kayan nake son ki saka mini su yanzu,zamu fita mu ci abinci a can." Riga ce doguwa har ƙasa take, amma sai ɗan siririn hannunta, sai kuwa ƴar samanta mai dogon hannu har izuwa wuyan hannunta, dole ta sa na tattare su na matse a tsakanin cinyata,gudun kada su ja ƙasa,a cikin banɗaki na isa gaban madubin banɗakin na tare gashin kaina na ɗaure shi da ɗan mayafin da na gani maƙale a jikin kayan, na yi murmushi ganin na yi mugun ƙyau, abin ka ga kalar jinin kare, sai kuwa dogayen hannuwan rigar, amma ragowar jikinsu kuwa duk jinin kare ne (Maroon colour). Na fito ina murmushi, sannan na yi saurin sakin rigar sai na ga take ta saman tsakanina da ɗan leɓunta zai kai taku biyu ta cikin ce kawai ke ƙwance a daidai ƙafafuna. Na isa bakin madubi na zauna domin gyara fuskata, na gyare ta da wata irin hodar da take fitowa da ainihin kalar fatar jikinka,jan baki kuwa kalar kayana na saka, jinin kare kenan,dan in ƙarasa zama su turawan har ma gashin ido na saka, gashin ya yi tsaye abin gwanin ban sha'awa. Girata kuwa sai na goga mata ƙarin baƙin jagira, domin ta ƙara fitowa, na ɗauki turare zan fesa, sai na ji ya riƙe hannuna har na ɗan ji tsoro saboda ban ga isowarsa ba, ɗan firgitar tsoron da na yi sai ma naga ta burge shi ya kamo hannuna ya miƙar da ni tsaye sai na ga ya sumbaci goshina, kunya ta sa na sunkuyar da kaina ya tallabo haɓata da hannunsa ɗaya. "Your beauty make you to be the Prince's wife. Yasmin ya za'ayi in samu kamar ki in yi sakaci in rabu da ke,ai ya zama dole in ajiye mulkina in zama bawa a gare ki, saboda in samu in mallake ki da zuciyarki su zamo sun gauraya da jinina." Idona a nashi amma sai na ji kamar idanunsa sun fi ƙarfin nawa, saboda wasu kunamun haske da suka fito daga cikinsa suka shiga nawa idon, wannan yasa na yi fari da idanuwana tare da lumshe su, wanda ɗan guntun murmushin da na yi, ya nutsar da gefunan kumatuna, abin da na san yana ƙara fito mini da ƙyauna a fili. *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 12 "Sorry,ina baki kunya ko? Tashi na daina." Ya kamo ni na miƙe tsaye, sannan ya fesa mini turaren da ke hannunsa. "Komai ya yi sai dai abu ɗaya da ki ka manta." Na ɗan yi ƴan dube-dubena, na ga jikina ba abin da ya rasa, na tambaye shi amma irin tambayar nan ta ido. Ya warware ɗan mayafin da na ɗaure gashin kaina ya lulluɓa mini shi irin lulluɓin nan na ƴan gayun boko shi ne a nannaɗe kai kawai a saki leɓe ɗaya a baya, ɗaya kuwa gaba, wanda ya bazashi ya rufe ƙirjina da shi, sannan ya zagaya ya fito da gashina ya ƙwanta baya, ya zagayo. "Tsaya ina zuwa." Har da ɗan gudun saurinsa ya isa ga aƙwati ya buɗa sai ga ɗan aƙwati ya fito da shi ya iso ya ɗora saman madubi, sannan ya buɗe sai ga sarƙa da ƴan kunne da zobe da agogo, duk shi ya saka mini su,ni kuwa ina tsaye ina kallon ikon Allah. "Kin san dalilin gyara miki mayafi?" Na girgiza kaina. "Saboda You are full house wife." Na yi murmushi. "To an gama, sai in ce miki yau zan miki wani abin mamaki, amma sai mun sauka ƙasa, sannan zan ɗaure miki idanuwanki da wannan ɗan hankicin sai mun isa." "Gaya min tun a nan." "No,sai kin gani da idonki." Riƙe yake da hannuna muna tafiya har sai da muka iso ƙafar bene,sannan ya rungume ni jikinsa wai kada in faɗi,balle wani irin takalmi mai tsini ya saka ni sawa,ni dai na san mun daɗe muna sauka ƙafar benen,don na ji ya ce in tsaya ya dawo. Na yi tsaye tare da riƙe katakon da ke kare mai tafiya. Ɗan tsayin mintuna biyu sai ga shi ya dawo, ya kama ni ina ji muka ci gaba da tafiya,ƙafata ta gane an zo irin ɗan filin nan na tsakanin wani hawa da wani sai na ji ya tsayar da ni ya zagayo ta bayana sai na ji ya ce. "Zan ƙwance miki, amma kada ki buɗe ido sai na ce ki buɗe." Sai da

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});