Chapter 2
Chapter 2
hankali na dinga gogawa, saboda jikina babu ƙarfi sosai, amma duk da haka sai da naji na gaji sai da na ɗan tsaya hutawa, ya yi murmushi ya karɓa ya ƙarasa mini. "Ya sunan ɗaya daga cikin yaran gidanki?" "Mansura ko Muslum." Ya miƙe da hanzari ya ajiye kayan a ƙasa ya leƙa barandar cikin falo, ya kira Mansura, da gudu ta hayo,a inda shi kuma ya dawo ya zauna. Ya umarce ta da ta ɗauko masa mango juice a firji,ta tafi cikin saurinta, shi kuma ya shiga banɗaki da kayan ƙazantar wanke bakina a hannunsa. Ko fitowa bai yi ba, sai ga Aunty ta ce, "Lah! Ina Yarima, bari in gaya masa kin tashi." Sai ga shi ya fito. "Ta tashi?" "Ta ɗan jima, abin da yasa ban ce a taso ki ba,ganin kin samu bacci shi yasa." Ta iso ta zauna gefen gado. "Ya jiki Yasmin?" "Da sauƙi." Nan suka ci gaba da zama ita da Yarima, har sai da ya ga nasha mango juice ɗin nan sannan Aunty ta matsanta masa da ya je ya yi koda wanka ne, da ƙyar ya amince. Bai fi mintuna goma da tafiya ba, sai ga Mama ta iso, cewa take, "Barkanmu, barkanmu Yasmin,tare da Sarki muke yana ƙasa,kin san abun mata, shi ne na hayo in ga yanda ku ke tukunna." Ta juya ta yi baya, sai ga su sun shigo tare da Sarki tun da ya shigo na ga fuskarsa cike da walwala. Sarki ne har gefen gadona,yana ta jinjina abin da ya faru, Mama ta ɗaga bargon da suka lulluɓe ƙafata, suka kalli ƙafar. "She will be alright." Sai ga yarima da saurinsa. Doguwar riga ce a jikinsa har ƙasa ta ƴan Saudiyya, wacce ta sha aiki tun daga samanta har ƙasa da wandonta da hula kalar ruwan madara da takalman ƙafarshi kalar hular. Yana shigowa ya zauna har ƙasa ya gaishe da Sarki, da mahaifiyarsa,yana sunkuyar da kai irin na girmamawa, amma sai na ga Sarki ya ɗan ɗaure fuska,Yarima na ɗagowa, sai na ga ya yi mini ƙyau,wanda ban taɓa gani ba a fuskarshi, na ƙara kallonsa, sai na ga fuskarshi tana ƙara sheƙi. Na juyar da fuskata gefe, saboda tunanin ko shaiɗan ne ya ƙara ƙayata mini fuskarsa. Ranar kam naga jama'a, sai yiwa Yarima barka ake yi, madadin a yi mini. Su Mamee ma da aka zo,ai ta Yarima ake yi bata ni ba,ni kuwa madadin inji yana ba ni haushi kamar baya, sai na ji ina jin daɗi yadda yake nuna ai ya shiga tashin hankali, a inda yake baiwa masu zuwa labarin ƙwanana biyu kenan da suma haka ban farfaɗo ba sai yau. Anan na samu labarin ashe har ƙwanaki na yi a ƙwance,lallai dole bakina ya yi ɗoyi. Ƙwanana huɗu a ƙwancan nan, amma duk wata kulawa da ake nema, tabbas Yarima na ba ni ita, har ma wacce ta fita,a inda tunda ƙwana biyu ya ce Aunty ta tafi gidanta ta ƙwana ta ji da yaranta. Tun ban ɗaukar abin da Yarima ke mini da sunan so, har zuciyata ta amince lallai ya kamu da ciwon sona, ciwon da na lura ya riga ya yi masa katanga a zuciya,ni dai bana cewa ina son Yarima, amma tsanar da nake nuna masa a baya, yanzun bana iya yi masa ita. Da la'asar wacce ta cika ƙwana huɗun sai ga Mama, bayan gaisawarmu ne, na ga sun fita falon sama da yake labulan shara-shara ne tsakanin ƙofata da falon, shi ya bani damar ganin abin da ke faruwa a tsakanin Yarima da Mama. Shi ne na ga ya durƙusa ƙasa yana yi mata magana, amma bana jin maganar, sun ɗan ɗauki mintuna sha biyar sannan ya shigo. "Yasmin can gida zan tafi da ke domin yi miki magani sosai,kin ga can an fi samun magani,a yanzun haka ma Sarki ya tura a ɗauko wani mai magani a ƙauyen Bukuru." Na washe baki alamar na ji daɗin maganar da ta faɗa, amma sai na ji jikina kamar bai amince ba, sai dai kuma ba zancen gardama a tsakaninmu,ɗaga kaina da nayi na hango Yarima jingine a jikin bangon shigowa ɗakina, shi yasa na ji tausayinsa ya kama ni. Ya iso wajen Mama jiki a sanyaye, ya durƙusa ƙasa ya kama hannuwanta. "Mama, wallahi ina kulawa da ita,ki tambaye ta ki ji, Yasmin ba ina kulawa da ke ba? Mama a nan fa nake ƙwana a wajenta, Mama ki bar ta wallahi zan kula da ita sosai, zan fi dama." "Wai kai meye na damun kanka ne a kanta, kai ka ce mini baka son...." "Mama kada ki faɗa, wannan a da ne,shin ba cewa na yi ƙwata-ƙwata ba." "Ka ga an gama magana, sai dai ka yi haƙuri." Ta juya ta kalleni. "Zan tafi da ke yanzun,su wa za'a kira su shirya miki kayanki?" "Mansura." Na bata amsa. Ta kalleshi, "Kirawo Mansura a falo babba." Ya ce to, ya miƙe ya tafi. Saman kujera doguwa yake zaune a babban falo, ya ƙwanta jikinta sosai, da gani ka san cikin damuwa yake, ya ɗago ya kalleni a daidai lokacin da ake saukowa da ni sai na ga ya yi murmushi. "Ina nan zuwa anjima." Haka kawai ya faɗa,mu kuwa muka wuce. **** **** ***" Lallai kam na ga gata, na tabbatar da cewa iyayen mijina na ƙaunar ɗan su, shi yasa ƙaunar ta shafe ni,a nan na ƙara yarda da cewa sarauta abin ƙauna ce, ga wanda bai shige ta ba ne yake ganin tamkar aikin bauta ake a cikinta. Yanzun kam ni da kaina zuciyata da sauran jikina suna ƙaunar sarauta, saboda ganin yanda take tafiya cikin tsari da nunawa jama'a ƙauna ta gaske. A wannan zaman ne ma na san wa ye Yarima da iyayensa. **** **** **** Yarima fari ne,ƙyakƙyawan gaske wanda dirin jikinsa na cikakken namijin da ya amsa sunansa, wanda gashin bakin fuskarsa ya ƙara ƙawata fuskar tasa, amma shi farin shi ja ne, tamkar na Turawa, idanuwansa kuwa sun ɗan yi girma kaɗan, tamkar na Salman Khan ɗan ƙasar Indiya. Sai dai shi zamu iya kiran ƙirar jikinsa irin ta Turawa, da ganinsa dai ka ga (Handsome). Tabbas ya cancanci sunansa, wato FAYSAL. Su biyar ne kaɗai ƴaƴan Sarki. Yarima shi ne babba, sai ƙannansa huɗu, amma mace ke bi masa Salimat, ita ce matar ɗan Sarkin Wasai, wato ƙaramar hukuma ce a Jos,sunan mai bi mata Idris,saurayi ne yana karatu a London, sai Sauda wacce take aure a Mina,sai autansu Ahmad. Yarima za a iya kiransa ɗan shekara talatin da biyar, ya yi karatunsa ne a Greece tun yana ɗan Sakandire aka kai shi ya karanci hulɗa da jama'a Public Relations. Ba wai domin ya yi aiki ba, a'a don dai ya iya zama da jama'a da riƙe gari, idan ya zamana ya hau mulki. Matan Sarki biyu ne, amma mahaifiyarsu Yarima Hajiya Mariya, ita ta haifesu su uku, shi da ƙannansa, da Idris da Salimat, amma Sauda ƴar ɗakin Hajiya Khilishi ce ita da Ahmad wanda yanzu yake makarantar gaba da Primary. *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 2 Ko a ido ka ga yanda ake wa Yarima,ka san ana ji da shi, sannan kuma sam ba ka gane cewa ba ɗakinsu ɗaya da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24