Chapter 16
Chapter 16
jariri, har ya fara goge mini,ganin ina layi yasa na ga ya ɗauke ni cak sai dai na ji ya yi gyaran murya. A take na ga kawai yana tafiya labulan nan na binmu ba mai ganin kowa ba mai ganinmu, shi kuwa ɗan yankin nan ya shinfiɗa shi saman ƙirjina wanda amai ke ta zuba a jikinsa,ni dai dole ta sa na koma saman ƙirjin Yarima na ƙwanta, idanuwana kuwa tuni a lumshe suke. Jin an ajiye ni wani abu mai laushi yasa na buɗe idanuwana,gani na a ɗakina saman lallausar katifar mulkin nan zan ce ko kujera? Wacce ta sha dardumai na alfarma, da rawar jiki na ga ya cire alkyabbar jikinsa da ta sha feshin amai, sannan ya duƙo wajena yana ƙoƙarin cire mini tawa,na ɗaya masa hannu alamar ya tsaya. "Don't touch me." Na faɗa. "Yasmin ki yi haƙuri in taimaka miki." "Bana so,ni ka kira mini Aunty Salwa." Na saka kuka, yayin da na ci gaba da cewa "ka cuceni,ka tona mini asiri,ka yaudare ni, Allah ya saka mini, yanzun kuma gidanmu zan tafi, ba zan ƙara zaman dabbanci ba a gidanka,ƙiri-ƙiri ku mayar da al'ada addini." Yasmin ni kaina ba na so, ya zan yi dama na san sai kin zarge ni." "Zargi ne ma?" Ya zauna jikin gadon zai kama ni. "Kada ka taɓa ni,wa ya sani ko yanzun ma ka fita ka faɗawa jama'a cewa ka rungume ni." "Oh! My Darling....." Dagewa na yi nasa kuka mai ƙarfi, sai na ji ya tashi ina jin takun fitarsa,bai fi minti biyar ba sai na ji an shigo. Aunty Salwa ce ta shigo da saurin ta. "Aunty kin ga Yarima ko, ya cuceni, ya wulaƙanta ni a gaban jama'a." Na ƙara sa da kuka. Ta iso ta zauna kusa da ni tare da dafa kafaɗata. "Haba Yasmin bai dace ba a ce kin zargi mijinki ba a kan abin da ya faru,in har za kiyi la'akari da taron da aka yi a yanzu, wannan zai nuna miki cewa tun kafin a san za'a haifi shi kanshi Sarkin haka akeyi, na fahimci al'ada ce su wacce take muhimmiya a wajensu. Saboda muhimmancinta fa Sarki da kansa yau tun da baƙwai na safe ya je ya gayawa Daddy,kin ga irin murnar da Sarki ke yi kuwa,ni a ɗan tunanina da na yi, wannan shi ne mataki na ƙarshe da za'a gane wa ye Sarki na gaba,in ka dace da mace tagari, to daga lokacin ma za'a iya kiranka Sarki mai jiran gado,in kuwa da sauƙi, to ko mutuwa sarki ya yi an san ɗansa wanda ya cancanci a baiwa sarauta. Ki yi tunani ki gani,ni tunanin abin da za ki yi ƙoƙarin ki hana a nan gaba, shi ne yin taron,ko nunawa jama'a zanin gadon yanzun ki tashi ki canja kayan jikinki, kamata ya yi ma ki ɗan shiga ruwan ɗumi." Aunty ce ta taimaka mini na shirya jikina na ƙara narka wasu kayan, duk da cikin waɗanda Mama ta aiko mini da su ne, shi ma wani irin yadi ne na alfarma mai ruwan jinin kare mai duhuwa (Coffee colour), Ina niyyar in koma in da ake taron, amma ina sai na ji zazzaɓi ya rufe ni. Aunty ta ɗauko magani ta bani na sha, amma duk da haka, sai na ji ƙwanciya kawai nake so. Ƙarfe ɗaya da ƙwata limamin masallacin gidan Yarima ya ƙwallah kiran sallar azahar,jin mata na ta ƴar hayaniya yasa na gane an tashi, amma sai na ƙara yin lamo saboda kunya da ta hanani haɗa ido da kowa, ina jin su Hajiya Kilishi da sauran mutane aka shiga ana yi wa Aunty ya mai jiki. Yanda na ji Aunty nata hira da mutane yasa na gane lallai da ƴan'uwanmu suke hira,shin wa ya gaya musu? Haushi da takaici suka ƙara dirar mini a zuciyata. Yanda na ji ana yi masa sannu da zuwa da tambayarsa ya mai jiki shi ya tabbatar mini da Yarima ne ya shigo, ƙara lamo na yi tamkar ma yanzun na fara barcin, ina jin shi yana tambayar na yi sallah? Aka bashi amsa a'a, sai na ji ya ce lallai a tashe ni inyi sallah. Bayan sallar isha'i ne ya shigo ɗakina ni kuwa a wannan lokacin na samu sauƙi sosai kamar ma ban yi wani zazzaɓi ba, asali ma ina zaune a kan abin sallah ta da alƙur'ani mai tsarki a hannuna ina karantawa, ba don komai ba saboda godiya ga Allah da ya taimakeni na riƙe mutuncina, sannan na yi godiya ta musamman ga iyayena da suka yi mini tarbiyya tagari. Maimakon ya yi mini magana sai na ga ya zauna gefen gadona, ina jin gani ya yi ba ni da niyyar dainawa, saboda ya yi kusan mintuna ashirin da biyu, amma sai in buɗe wani fejin in cigaba, ganin haka na san yasa shi ya taso ya zo ya zauna bayana, madadin inji ya yi magana sai na ji ya ɗaga hijabin da ke jikina ya shiga ciki, daga nan kuwa sai dai na ji ya sa hannayensa ya rungume ni ta bayana, kenan hannayensa suna saman ruwan cikina, sai a lokacin na ji ya yi magana. "Ya isa haka nan Yasayyada, ya kamata a zo a kula da baƙo ko shima ya zo ya yi wa matarsa sannu. Madadin in tashi ko in mayar masa sai dai na ajiye Alƙur'anin na mayar da kaina na matse a tsakanin gwaiwoyina saboda dalilin abu biyu. Na farko na san ni ba zan iya haɗa ido da shi ba, saboda kunya. Na biyu kuma saboda ɗan haushinsa da yake a zuciyata. Ganin ya samu sama da mintuna sha biyar yana fama da ni in ma yi masa magana na ƙiya, ya sa naga ya sake ni ya miƙe tsaye,dama tuni ya cire hijabin jikina ya mayar da ni ya ƙwantar a cinyarsa,yana ta ɗan kokawar cire tafukan hannayena waɗanda ke rufe da fuskata, wanda ko ya cire zan runtse idanuwana da ƙarfi. Sai dai na ji yana cewa, "Mama ta ƙi yi mini magana, Mama ki zo,wai haushina take ji,ni ma na gaya mata ba laifina ba ne ba,kona ba ta ba zata karɓa ba." "Kai! Ni na ce." Na faɗa cikin sauri. Ya juyo muka haɗa ido na harare shi. "Dama na ce miki cewa ta yi ni ɗin me." Na taso zan karɓi wayar ya juya na bi shi ya juya na riƙe hannunsa,wai ni in karɓe wayar, amma saboda ƙarfi irin na namiji ya riƙe hannun gam. "Mama ban yi mata ƙarya ba, cewa ta yi ban isa in sa ta karɓa ba." Na yi tsalle na fige wayar. "Mama wallahi ba da gaske ba ne ba sai na kashe wayar nasa kuka. Bacin ka gama wulaƙanta ni a gaban jama'a yanzun kuma so ka ke mahaifayarka ta tsane Ni?" Na tafi na faɗa gado. Kusan mintuna arba'in kenan da zuwan Mama,ni kuwa tsugunne a falo jikina ya sha naɗi da hijabi, hankalina ya nutsu da abin da Mama ke faɗi, kamar yanda ta fara da farko. "Ba wata kalmar da zan yi amfani da ita inyi miki godiya, sai dai inyi amfani da ƙarfina in yi miki addu'ar Allah ya saka miki da ƴaƴa nagari, kamar yanda iyayenki suka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24