Chapter 6
Chapter 6
ina son Yarima Faysal ne?" Anwar shi ne mutumin da ya fara saka ni hanyar soyayya, mutumin da ya shayar da ni ɗanɗanonta. Anwar Mutum ne wanda ya rigaya ya karanci halayyata, har ta zamo ba ta ɓata masa rai. Anwar ba wai ƙyakkyawa ba ne, sai dai sam ba ya layin munana,kalar fatar jikinsa kuwa mai ɗan duhu ce, amma da ganinsa ka san yana cikin hutu. Anwar babban ma'aikaci ne shi, wanda har ya kai matsayin babba a ofishin da yake (Cooporate Affairs Commission). Mahaifinshi ya tsufa, mahaifiyarshi ce mai ɗan jini a jika, wanda gidansu su huɗu ne kacal,yayyansa biyu, mace da namiji, sai kuwa ƙaninsa namiji ɗaya. Ni kaina na san ina son Anwar, Mutumin da muka shekara uku da shi muna (Friending), amma rashin auranmu da shi tun a baya, na san laifina ne, tare da ƙaddarar auran Yarima Faysal. Iyayensa ƴan asalin Kano ne, aiki ya kawo mahaifinsa na Likitan dabbobi, suna da arziƙinsu daidai gwargwado, ga shi mutum ne mai tausayin gaske ni kaina na san Anwar na matuƙar ƙaunata. **** **** **** Wazirin Sarki,Galadima,Tafida, Talba da Durɓi,su ne a tebirin shawarar Sarki, wanda Sarki Jafar Sada ya tarasu ne a kan hukuncin da ya yanke a raba auran Yarima Faysal da Gimbiya Yasmin,saboda su ne mutanen da suka fi kowa kasanci da shi fiye da kowa. An ɗauki ɗan tsayin lokacin da za'a iya ba shi sa'a ɗaya (awa ɗaya), ana mahawara a kan maganar, wanda a ƙarshe magana ta koma ta basuyi na'am da hukuncin da Sarki ya yanke ba, saboda dalilai da suka kawo irin nasu na manya, kamar dalilin waziri. Ya Kawo dalilinsa ne a kan nan gaba idan suka nemi aure za'a iya hana su, saboda za'a ga ba sa riƙe aure da daraja, dalilinsa na biyu kuwa shi ne,a bar yaran da kansu su zo su ce basa son junansu,in sun zo da zancen haka, ina ga in an raba su ba za'ayi laifi ba wajen kowa. Galadima kuwa cewa ya yi a kan samu haka a tsakanin ma'auratan da aka haɗa aure, ma'ana waɗanda ba su suka zaɓi junansu ba. Shi kuwa Tafida cewa ya yi abin kunya ne a garesu a ce sun yi wa ɗansu aure wanda suka tara jama'a ba iyaka daga garuruwa, jahohi, ƙasashe, amma a ce ƙwanakin da ba su wuce arba'in ba aure ya rabu, alhalin muna taƙama da cewa shi ne magajin Sarkinmu a nan gaba. Shi kuwa Durɓi cewa ya yi anyi daidai da aka ja masu kunne aka tsorata su, amma maganar rabuwa ma bata taso ba,a kira su dai a ƙara ba su lokaci, idan har ba su sasanta kansu ba, to sai a haɗu da iyayen yarinya a ƙara tattaunawa, daga nan sai a nemi shawarar da ta fi cancanta, sannan yana mai baiwa Sarki shawarar ya je ya samu iyalinsa ya lalubi wani abu daga gare su na game da yaran, saboda su mata ne za su fi mu samun labarinsu. *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 4 A nan dai suka tashi saboda ganin juma'a ce za'a fita Masallaci da wuri. Sarki ya shiga ya kira iyalansa,Mama Mariya ita ce mahaifiyar Yarima, sai kuwa Hajiya Kilishi wacce take mahaifiyarsu Ahmad ga ta amarya. Ya gaya masu shawarar da ya yanke a kansu Yarima, amma yana mai tambayarsu shawarar ya suka gani. Hajiya Kilishi ita ta fara magana,haba Shugaba ya za'a yi a ji irin wannan maganar daga bakinka, alhalin ku ne manyan da ku ke yankewa ƙanana hukunci,haba mai girma,ai ka san auran haɗi dama ya gaji haka kafin ma'auratan su saba. Ka tuna kanka mana,watana nawa a gidan nan ban saba ba, yanzu fa ka ga a sai mutuwa kawai ta rage mini a cikin gidanka. Ni a shawarata mai girma a sa masu ido, tun da an ɗan tsorata su, balle ma yanda naga shi Yarima na yawan zuwa gidan nan,a lokacin da aka dawo da Yasmin nan gidan,kai a taƙaice sai na kore shi gida yake tafiya in dare ya yi. In kuwa suka shige ƙuryar Mama sai su ƙwashi awanni, sallah kawai ke fito da shi,don ma yarinyar na da kunya,waya kuwa in dai har ba ya cikin gidan nan har gajiya muke yi da ɗauka, sai na cewa yarinyar ta taimaka ta ɗauka, sannan zai bar mana kunnuwa su huta. A fahimtata dai Yarima ya sauko, ita ce dai ke da saura, kuma ka san dan tana mace, akwai kunya irin ta mata,ko Mama kin yi shiru?" "Me zan ce ai kin gama faɗa, ƴaƴanki ne fa, shawarata ɗaya in har da ragowar zamansu tare,to ki kira ɗanki ki ja masa kunne, saboda laifin na wajensa,ai ya ba ni labarin duk abin da ya haɗa su tun farko." "Allah ya huci zuciyar Sarki,a ƙara dai duba wannan magana." Inji Hajiya Kilishi. Ya miƙe, "Zan je in huta kafin tafiya masallaci, zan duba maganar insha Allahu." "Godiya muke,a huta lafiya, sai ka fito." Inji su gaba ɗaya. **** **** **** Sarki Jafar Sada ne zaune a doguwar kujerar mulkinsa, amma ta fadar cikin gida, kenan ɗakin shaƙatawar da yake ganawa da iyalinsa. Ni da Yarima kuma muna zaune a tsakiyar fadar,kowannan mu kanshi a sunkuye a ƙasa,ko ban faɗa ba kuwa na san daga ni har Yarima gabanmu faɗuwa yake yi, saboda na kalle shi ta wutsiyar ido ko motsi ma baya iya yi, saboda sanyi da jikinsa ya yi. Cikin ɗan satar kallo ta wutsiyar ido na kallo fuskar Sarki, gumi ne ya fara tsiyayo mini a fuskata,tun kafin in dawo da kallon gabana, saboda ganin fuskarsa da na yi ba wani annuri cikinta, ballantana alamar wasa. Na ƙara mayar da satar wutsiyar idon nawa ga yarima, na gan shi yana mayar da ajiyar zuciya, duk bayan sakan biyu, ban da gumin da na hango yana yi wa kansa magangara a jikinsa. Take kawai sai na ji tamkar in sa haɓar mayafina in dinga goge masa, wannan ne ma yasa na ji kamar zuciyata na ɗan kiɗan da ba sauti, balle ta samu ƴan rawa, hakan kuwa shi ya tunano mini daran jiya yanda muka ƙwana. A daran jiya ni na yi imanin babu wanda ya samu runtsawa ni da Yarima, dalilin da yasa na gane hakan kuwa shi ne,ganin saman ɗakinsa da fitila duk da ba mai haske ba ce ba,a tunanina ta gefen gado ce ma ya bari a kunne. Na gane hakan ne a sakamakon leƙen da na kusan ƙwana ina yi ta labulayen taga ta,wai ko na ga Yarima a ƴar barandarsa, yanda ya saba. Amma har na gaji na haye gadona ban ga ko da ƙyallin kayansa ba, wannan ya ba ni tabbacin bai samu yin bacci ba,ƙila gara ma ni tunda na samu na shiga bargona na yi lamo. Inji Malam bahaushe ya ce, "wacce ta fi barci daɗi." To ni dai jiya, wacce ta fi barci ciwo na yi. Saboda har yatsun hannuna sai da suka yi mini ciwo, saboda jan carbi,wai ko ya suɓuce daga hannuna in samu bacci ya ɗan ɗauke ni, amma sai dai na gaji na ajiye na cigaba da lazimin cikin zuciya, sai dai wani abin al'ajabi zan ce ko abin haushi? Wai har
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24