Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

Chapter 23

Kasaita Book Two Complete Hausa Novel 1,218 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

daga zuciyarki, kin canja mini rayuwata gaba ɗaya." Ina jin shi yasa hannu ya janye ɗan dogon gashin da na rufe jikina da shi. Ya sunkuyo ya sumbaci ƙirjina na yi saurin ƙwantawa ƙirjinsa ya tallabe kumatuna. "Yasmin you love me sure?" Na ɗaga kaina alamar eh, ya ɗauke ni cak ni kuwa na koma na ƙwanta a ƙirjinsa ya hau gadon sosai, sannan ya ƙwantar da ni ya janyo filo ya ɗaga ni ya gyara mini ƙwanciyata sosai, ya juya ya janyo bargon da ke maƙale jikin gado ya lulluɓa mini har izuwa ƙirjina,sannan ya sunkuyo ya sumbaci goshina da laɓɓana yasa hannu ya gyara mini gashin da ya sauko mini a saman fuska. Ni kuwa cikin lumsashshen ido nake kallonsa sannan ya ce, "ina zuwa." A cikin raɗa sai na ga ya sauka na buɗe idanuwana sosai na bishi da kallo a take sai na ji na tsorata saboda ganin shi ɗaure da tawul haka ya nuna min ashe Yarima na da tsokar jiki,ganin wasu cinyoyin tsoka a cinyar hannunsa duk sun yi kusurwoyi kamar ta ƴan kokawa (Wrestling). Ga wata tsoka ta ƙwanta a gefunan wuyansa, ban da tsokar da na hango a cinyar ƙafarshi, ya buɗe durowa ina kallonsa sai na ganshi ya juyo yana fesa wani abu a hannunsa, ganin dogon gwangwani ne yasa na gane abun sa ƙamshin ɗaki ne (Room Freshner) duk da ban ga sunansa ba, cikin sakan uku ɗaki ya kaure da ƙamshi mai sanyin gaske, ban da laushin shaƙa da hancina ya yi. Ya ɗauko wata ƴar ƙwalba bayan ya ajiye wancan sai na ga yana ɗan ɗigata yana shafawa a gashin ƙirjinsa,a zuciyata na ce ashe maza ma suna ƴan gyara irin na mata. Ina kallo ya ɗauko turare ya fesawa jikinsa ya mayar da durowa ya rufe, juyowar da zai yi sai na ga idanuwansa sun ƙara fitowa sun yi ja,dama abu (Barakallah), manya da su, sai ya juye mini kamar na ƙwatanta shi da ɗan fim ɗin nan na ƙasar Indiya (Salman Khan), har da faɗin ƙirjin ga tsokar curi-curi a cinyoyin hannunsa. Na ɗan yi saurin kawar da kaina gudun kada ya gane kallonsa nake yi,jin bai hayo gado ba yasa na ƙara waigowa sai na ga ya kunna mana hitar gasa ɗaki (Room heater), sannan ya isa ga makunnin fitila ya kashe ta sai fitila ɗaya ke ci, ta gefen gadonmu, tun da ya hayo gadon ya ƙwanta tare da kashe fitilar gefen gadonmu ban ji ya yi motsi ba, ga shi kusan mintuna ashirin kenan. Zuciyata ba abin da bata saƙa mini ba,na ko lafiya ko kuwa ya yi bacci? Hakan ya sa na juya nima na cigaba da addu'o'in ƙwanciya baccina, na yi ƙwanciyata, jin ya ce, "Alhamdulillah." A bayyane yasa na ce ashe idonsa biyu. Madadin na ji ya yi magana sai kawai na ji ya ɗan cizar mini bayana na ɗan firgita kaɗan saboda a bazatan da cizon ya zo min tare da faɗar. "Kai Yarima!" Kafin in ƙarasa ya kuma cije leɓatun kunnena, daidai wajensa ɗan kunne, kafin na yi magana ya kurɗa ya ciji wuyana, kumatuna, na yi saurin juyowa na fuskance shi, sai kawai na ji ya cije laɓɓana. "Kai...." Yasa tafin hannu ya rufe bakina. "Don't talk." Numfashina na ji ya yi sama wanda ya ɗauki mintuna uku kenan bai dawo mini ba, ba wani abu ya janyo mini haka ba shi ne salon yanda Yarima ke tsotsar ƴan yatsun hannayena. Shin Yarima ne kuwa? Tambayar da zuciyata ta yi mini kenan,a daidai lokacin da numfashina ya dawo dai-dai kunya ta kama ni da na ji ya amsa mini da "Yasmin ni ne." A nan take na tabbatar wa kaina maganar da ke cikin zuciyata ce ta fito fili. Idanuwana kuwa na ƙara runtsewa,runtsewar da ta kai ni har wayewar gari ban ƙara buɗa su ba. Ji na cikin ruwan ɗumi yasa na san mafarki nake,a cikin mafarkin na dinga cewa, "Yarima mafarki nake na shiga ruwa." A kunnena na ji ya ce "Buɗe idanuwanki ba mafarki ba ne ba." Na firgita sai na ji ni rungume a ƙirjin Yariman a cikin ruwa, na waiga na kalle shi ƙwance cikin ruwan kumfa sai ƙamshi kawai ke tashi, na juyo na kalli kaina nima cikin ruwan kumfa. Na sa hannu na dinga laluba jikina, na ji zargin da nake ya tabbata na rashin kayan jikina, na juyo na ƙara kallonsa sosai sai na ga ya lumshe mini ido na juya a sanyaye na ƙwantar da kaina jikin gefen bahon wankan, sai na ji hawaye, saboda tunanin gane ni ba kaya. "Why! Why!! Why!!! Yarima? Me yasa ba ka tashe ni ba? Me yasa ka kalle mini jiki?" Ya ƙwanta bayana, "Yasmin,don kina matata kin manta mun amince da junanmu." Ya sumbaci bayan wuyana, "kada ki yi da na sani ko ki ji haushin abin da na yi,me yasa ba ki da yarda Yasmin? Nifa na amince da ke ce matata, ke me yasa ki ke kokwanto ne har yanzu?" Ya yi saurin dawowa gabana jin ina fitar da ƴar jaririyar kukan ƙissa, wanda Aunty ta ce mini ana yi, ya dago kumatuna ya tallabe da hannuwansa masu kumfa. "Ba ki son abin da na yi miki? Na ɗaga kaina. "To shi kenan ki yi haƙuri tsaya na baki haƙuri sosai." Sai na ga ya ɗebo kumfa yasa a saman kansa ya ɗiga a goshi, hanci a kunnuwa, sannan ya riƙe kunnuwa ya gwale idanuwa,dama abu (Tubarakallah) inji Malam bahaushe. Sannan ya ce, "Sorry." Dole ne ma na yi dariya, na yi murmushi kuwa sai ya yi saurin rungume ni. Ya ɗago kaina ya goge hawayen fuskata. "Kin yi haƙuri?" Na ɗaga kaina. "Ban yarda ba, sai kin ce eheee." Yanda ya tale baki ya ce eh, dole ta sa ka dariya, na sa dariya na daki ƙirjinsa da dukkan hannayena, ya girgiza kansa alamar jin daɗi sai ya rungume ni tare da faɗar "I love You too." Nima na amsa masa da "I love You too much." Amma a zuciyata,na koma na ƙara lafewa a ƙirjinsa. **** **** **** Satinmu huɗu a Greece,amma wurare ɗai-ɗai ne ban sani ba, balle ma da muka shirya sosai da shi. Ƙasar London,Rum(Italy) da kuma Turkey,duk su ma satinmu bibbiyu, wanda idan na haɗa su waje ɗaya mun ƙwashe watanmu biyu da sati biyu. Yau kuwa ranar Asabar ce, wacce ta yi daidai da ita ce ranar da muka iso Nijeriya, sai da ma Yarima ya tashe ni daga bacci ya sanar da ni an zo Nijeriya, wanda tun da muka shiga jirgi ya janyo ni ya ƙwantar a ƙirjinsa, ɗan wasannin shafa mini baya ya kama yi, wannan ne ma yasa har bacci ya ɗauke ni ba tare da na sani ba. Maƙale nake a kafaɗar Yarima har muka iso bakin ƙofar fitowa daga jirgi cikin ɗan ƙaramin lokaci na yi saurin janye jikina daga gare shi, saboda hango mutanenmu da na yi sun zo taryarmu. Dogarawa kenan. Ya janyo ni jikinsa. "Me ye haka,mun iso Nijeriya za ki fara gasa ni, wallahi sai mu koma." "Kalli gabanka." Na faɗa a lokacin da muke sauka matattakalar benen jirgin. Waziri ne da sauran manyan fada a tsaye suna jiran saukowarmu, ban da

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});