Chapter 11
Chapter 11
cikin cikakkiyar nutsuwa. A ƙalla ni na san na ɗauki mintuna talatin zuwa talatin da ƴan mintuna ina karantawa, sannan na ɗago kaina na kalli Yarima wanda na ji ya yi shiru,ni a tunanina ya yi bacci, amma sai na ga ya ɓalle maɓallin gaban rigarsa gaba ɗaya. Ni kaina na san Yarima na da gashin da ya ƙwanta a ƙirjinsa, dalilin ganin kuwa,ɗakinsa da na taɓa shiga na same shi yana bacci, amma abin mamaki sai na ga na yau yafi na ranar yawa,baƙi,ƙwantacce tamkar sumar jariri. Na yi saurin mayar da kaina ga littafin da ke hannuna, amma kuma sai na ji na samu kaina da son kallonsa duk bayan ƴan mintuna. Ɗagowar da zan yi in kalleshi sai naga ya ware duk biyun gaba ɗayan rigar jikinsa ta sauka saman gado, cikinsa, cibiyarshi,ƙirjinsa da kafaɗunsa duk a waje suke, take na ji jikina na neman kama rawa,me ye wannan? Ni dai na san har yanzun ba na son Yarima, sai dai na san ina jin kunyarsa. Na mayar da kaina ga karatuna, amma ni kaina sai na ji muryata ta canja,lumfashina kuwa ma nema yake ya tsaya,a zuciyata nake rayawa cewa in ajiye littafin in tafi gidana, madadin in ji ƙwarin gwiwa sai na ji tamkar an sare mini gwaiwoyina,cikin hakan da nake kawai sai na ji Yarima na kiran sunana a hankali. Jin kiran sunana ma sai na ji ya ƙara sani na dake, na dawo dai-dai saboda tunanin ko Yarima ya fahimci na shiga wata matsala da na san ba zan iya faɗarta ba,kiran sunana ya kamata a ce ɗaya ne ko biyu, amma tun da Yarima ya fara shi ban ji ya tsaya ba, tun ina ci gaba da karatun har ya zama ina saukar littafin hannuna a hankali izuwa ƙirjina. Kallona sai ya koma ga yarima da yake kirana, wanda idona ya hango ƙirjinsa na fitar da numfashi da sauri da sauri, wani mashi ne na ji ya dirar mini ta tsakiyar kaina, jikina na ji har ya ɗauki rawa cikin sakan ɗaya, saboda kiran da Yarima yake mini ya fi ƙarfin a tsaya ƙirgawa. Littafin saman ƙirjina wanda hannuwana suka taimaka masa ya zauna a ƙirjin nawa, sai na ji ya faɗo saman cinyata saboda hannuwan nawa sun kasa ɗaukarsa,jiri ne ya ɗauke ni ko kuwa suman sakan biyu na yi? Ni dai ji na nayi na sulale na ƙwanta saman gado sosai a riginginan da nake da ƙyar na ja filo ɗaya ya tallaɓe mini kaina. Amma duk wannan bai hana Yarima kiran sunana ba, idanuwana, kaina,jikina sun yi mini nauyin da ba za su iya motsawa ba, balle har ƙwayar idona ta samu ganin halin da Yarima yake ciki,ko ni kaina,shin me ye wannan? Ni na san ƙwaƙwalwata ta daina aiki balle in tunano amsar abubuwan da suka tarar mini a cikin mintunan da ba su wuce uku ba. Mai nake ji a jikina? Kamar numfashin mutum a hancina, ƙwaƙwalwata na ji na karanto mini Yarima na bin jikina, hannayena da ke ware ya bi da hannayensa a hankali har izuwa tafukan hannayena ya haɗa da nashi ya runtse gam, sumbatar wuyana na ji ya yi, ya dawo hancina,bakina,buɗaɗɗan gaban ƙirjina da riga ba ta ƙarasa rufe shi ba. Ni na san ina ji, amma ba zan iya motsa ɗan yatsana ba, balle har ya kai ni ga iya magana,ko ƙwatar jikina ba, sai dai na san numfashina yana fita sama-sama, ina jin shi kanshi ya ruɗe ya rasa ina zai kai sumbatar nasa,ko ina ya yi ina jin sa yasa haƙoransa ya zuge zib ɗin da ke gaban riga ta, wai nan na yi ƙarfin hali zan yi magana, amma madadin bakin da na samu da ƙyar na buɗe in yi magana sai gani na tsaya da wani irin numfashin da ya kasa wucewa cikina, ya tsaya mini cak a maƙoshina,saboda jin harshen Yarima na lasar fatar cikina, sai a lokacin na ji kamar na tunano ban sa shimi ba,rigar mama ce kawai na saka da zan taho. Jin ya nutsa hannayensa a gashin kaina yasa na samu da ƙyar lumfashina ya isa cikin cikina tare da faɗar "Hasbunallahu wani'imal wakil" sai na ji kamar ɗan jinin jikina ya dawo, na samu na yi ɗan ƙoƙarin miƙewa zaune, amma ina sam na kasa, saboda Yarima da ya samu ƙaramin taɓin hankali a jikina. Da ƙyar na buɗe idanuwana sannan na ɗaga kan Yarima na tallabo kumatunsa na girgiza kaina, wanda fuskata ke fitar da hawaye da ban fahimci ta ina suke fitowa ba, yasa hannuwansa duk biyun ya ɗago kaina ya girgiza kanshi shi ma, sai a nan na lura da hawayen da suka wanke fuskarshi shi ma, da ƙyar na ji ya ce, "Yasmin!" Yana mayar da numfashi ɗaya bayan ɗaya. Na girgiza kaina da ƙarfi, sannan na samu na miƙe na zauna, ya koma gefe ya ƙwanta rigingine yana wani irin numfashi. Na miƙe tsaye, tafiya na fara nayi luuu zan faɗi, na yi saurin zaunawa, na nutsa hannuwana a gashin kaina, jin ya rarrafo ya zo ya rungume ni yasa na ɗan samu ƙarfin cire hannuwansa daga jikina na miƙe. *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 7 Na mayar da zib ɗin rigata na zuge, na samu na ja mayafina da ke saman gado ba zancen tsayawa yafawa, sai da na je ƙofa, sannan na tsugunna na ɗauki takalmana a lokacin idanuwana suka sauya kallo izuwa saman gadon da Yarima ke durƙushe yana kallona ya ware hannayensa yana ɗan girgiza kansa kada in tafi. Ganin ina kallon shi yasa na ji yana kiran, "Please Yasmin come to me." Wannan ma yasa na juya na tafi, sai kuwa da na je ƙofar fita, sannan na samu na yafa mayafina, amma takalma sai da na je ƙofar gida, sannan na iya sa su, ina buɗe ƙofa kuwa taku uku na yi na tuɓe su na riƙe a hannuna ina isa ɗakina na wurgar da su. Fitilu kawai na kashe na faɗa saman gadona ban tsaya neman wata rigar bacci ba,fulalluka na haɗa na rungume a ƙirjina,ni kaina ban san me zan tunano ba saboda ƙwaƙwalwata ma ta daina aiki, sai dai numfashina kam ya dawo, amma da ɗan sauri nake fitar da shi tamkar na yi gudu na gaji. Ban fi mintuna biyar ba na ji an murɗa ƙofata an shigo, da ƙyar na samu na lalubo wayar makunnan fitilar ɗakina ina kunnawa sai na ga Yarima a tsaye, yanda rigarsa take haka take ma yanzu, na lumshe idanuwana na mayar da kaina na ƙwantar alamar mamaki,jin an mayar da ƙofa an rufe yasa na ɗaga na kalleshi, ban yi wani ƙoƙarin tashi ba. Ganin ya nufo gadona yasa na fara tunanin me zan yi yanzu ban tunano komai ba na ji ƙarar faɗuwa, kallon da zan yi sai na ga yarima a ƙasa na yi wata doguwar wuntsulawar da ban san ma ina da ƙarfin yin ta ba,ni dai gani na nayi kawai a gabansa na ɗago shi na girgiza shi, cikin wani yanayin muryar tashin hankali na kira sunansa. Cikin sakan uku na ga ya buɗe idanuwansa yana murmushi,ni kuwa har na fara fita daga hayyacina a cikin ƴan sakannin nan, sai na ji
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24