Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 1

Chapter 1

Kasaita Book Two Complete Hausa Novel 1,236 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

*ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 1 Hausanovels001.com.ng Ƙwana na yi ina juyi gudun kada ya je ya sanar a gidanmu, saboda na ga alama ba shi da kunyar kai ƙara, tun da ya kai ƙara ta ga Aunty. Ganin an wayi gari lafiya, shi ne na yi wanka na saka kayana doguwar riga ce mai ruɓi biyu, ƴar Saudiyya za mu iya kiranta ko Dubai. Na fito daga gidan ko ɗankwali babu kaina na nufi bakin dutsen da nake hutawa na yi tsaye. Lokacin kuwa ya nuna ƙarfe taƙwas na safe kawai wanda na ce na yafewa su Mansura rakiyata,ko kalaci ban tsaya yi ba. Ina tsaye nan ina ta saƙa abubuwan da na san ba zan samu ba,wato Yarima ya ji haushin maganar jiya ya ce ya sauwaƙe mini inje in auri Anwar, na ɗaga kaina jikin barandar ɗakinsa, sai na hango shi zaune a kujera ya ɗora ƙafafunsa a saman tebir ɗin gabansa. Na juya abina, sai ma na tattaka na haye dutsen, tsayin minti sha biyar na yi sai na ji ina sha'awar shiga ƙoramar nan,ta hanyar tattaka duwatsun da aka jera layi da su, waɗanda suka yi cikin ɗan dajin inda ruwa nan ke nufa,su kuwa duwatsun babu ruwanka da taɓa ruwa idan dai har ka sa ƙafarka a kansu. Nan take na saɓule takalman da ke ƙafata, na sulala cikin ruwan inda na dinga taka duwatsun a hankali, na yi tsaye a wurin ina ta waiwaigawa sai na hango barandar Faysal,ai kuwa juyawar da zan yi ina tsaki, sai na ga wani ƙaton miciji ya nufo inda nake tsaye, ta cikin ruwan nan kanshi a buɗe yana ta huci ban san lokacin da na yi baya da sauri ba ina ƙwalla ihu. Cikin ƙanƙanin lokaci ya tari gabana babu zancan iya motsi a yanda na ga yana hucin. Runtse idanuwana na yi na dinga ƙara,tun ina ƙarar har ya kaini ga kiran Yarima. Saman ƙafata ya kai wa sara, sai dai naji gab,na yi wata irin ƙara, na buɗe idanuwana, sai kuwa na hango Yarima Faysal a guje shi da wasu a bayansa. Sai na dinga cewa, "Maciji! Maciji!! Bai wani tsaya tattaka duwatsun nan ba sai dai kawai na ganshi da gudu a cikin ruwan, wanda ganin da nake masa dishi-dishi ne, daga nan kuwa sai dai na dinga jin maganganun mutane sama-sama, sai kuwa ji na yi ana jijjiga ni da kiran sunana da nake jin ana yi. Ina jin ƙasa na juyawa da ni, sannan ina ji sama-sama Yarima na daka masu tsawa zan iya cewa ɗaukata ya yi cak ya koma gudu, amma daga nan ban ƙara sanin komai ba. A hankali na dinga motsa idanuwana,alamar ina son buɗe su, ina cikin haka na ji Yarima na kiran sunana. "Yasmin! Yasmin!!" Sai na ji yana dafa goshina. "Ta motsa?" Na ji an tambaya. "Eh,tana motsa idanuwanta." Na samu tsayin minti biyar a haka, amma na kasa buɗe idanuwana, amma ina jin abin da ake faɗa. Jin abu mai sanyi a goshina, shi ya ƙara taimaka mini na ji hular idanuwana ta saki daga nauyin da ta yi mini, idanuwana Faysal suka fara gani zaune gefen gado,yana ɗora mini abin nan mai sanyi da nake ji, sai na ga ya yi saurin jefar da shi ya ɗago kaina ya rungume a ƙirjinsa, ya yi wata irin ajiyar zuciya. Sannan na ji ya ce, "Ta tashi." Ya mayar da ni ya ƙara gyara mini ƙwanciya,sannan ya sumbaci goshina, bayan nan kuwa mutane suka dinga leƙowa suna yi mini sannu, idanuwansu kuwa jajir kamar suna ciwon idon Afolo. Da ɗaiɗaya duk na fara gane fuskokinsu, amma matan,mazan ban san kowa ba,gwara ma ƴan na kusa da shi da ba su fi Biyar ba, ƴaƴan ɗakina kuwa har wannan lokacin kuka sukeyi. Bayan kamar minti sha biyar duk suka fita,a inda Yarima ya miƙe shi ma ya ɗauki wayar hannu, ya fara daddannawa. "Barka da yamma,eh, yanzun za ta yi minti ashirin, Eh, tana gane mutane, a'a ban duba ba, to yanzun zan duba. To sai kun zo,Mama da wuri don Allah yanzun ko, to zataji." Ya juyo ya yi mini murmushi. Sannan na ga ya cigaba, "Barka da yamma, eh, Yarima ne. Eh,Mamee, yanzu ta yi minti ashirin da ɗaya,a cewa Daddy ya zo yanzun ta gan shi. To Mamee ai kamawa ta yi,to, to zataji, to sai kun iso, to a huta lafiya, eh tana ƙasa, eh, na san yanzun zata hayo,kin san ƙwana biyu bacci ina jin bacci ne ya ɗauke ta,a ɗakin ƙasa, to za'a taso ta, mungode." Ya dawo ya zauna gefena ya matso kusa da ni sosai, sannan yasa hannunsa ya shafa gashin kaina, ya ƙara gyara mini gashina zuwa gefe, "Sannu." Ya ga dai ban amsa ba, sai na ga ya juyo sosai. "Yasmin,kina jina? Yasmin?" Sai na ɗaga masa kai, sai na ga ya ɗan mayar da numfashi tare da lumshe idanuwa, ya yi saurin kai min sumbata a kumatuna. Ya tashi a hankali sai na ga ya buɗe bargon da yake lulluɓe da ƙafa ta, sai a lokacin na tuna da cewa fa Maciji ya sare ni, nayi ƙoƙarin motsa ƙafar, na ji ta kamar dutse, ina kallo ya ɗaga ƙafar tawa a hankali, yasa hannu ya ɗan shafe ta. "Ƙafar ta mutu ko Yarima?" Na faɗa da muryata irin ta marasa lafiya. Ya rufe ya zagayo ya kama hannuna tare da zaunawa a gefena, wanda ƙafarshi ɗaya ya ɗago ta duka ya lanƙwashe ta har sai da gwiwarsa ma ta ɗan hau saman cikina. "Bata mutu ba,za ki warke sosai ma." Ya sumbaci hannun nawa,a take sai na ji tausayinsa ya kama ni. "A kawo miki abinci za ki iya ci?" Na girgiza kai. "A'a,zaki ɗan ci ko yaya ne,ko abu mai ruwa ne." Ya miƙe. "Bari inyi miki burush(Brush)." Da saurinsa ya fito daga banɗaki da burushi na a hannunsa wanda saman shi ke cike da makilin, da ruwa a ƙaton kofi da wata silba a hannunsa, ya ajiye su gefen gado, sannan ya hayo gadon gaba ɗayansa, ya ɗaga ni ya jera filallika guda uku a bayana, na ɗago sosai, ya janye bargon jikina ya mayar da shi iya ƙuguna, ya gyara shi sosai, sannan ya sauka ya ɗauko kayan ya ɗora silbar a cinyata. Ya kanga mini kofin a bakina, "Kuskure bakin tukunna." Na kurɓa, ya yi saurin ajiye ruwan a durowar gefen gadon, sannan ya ɗago silbar. "Zuba a nan." Na zuba sai na ga jajawur yawun bakina, ga ɗoyi yana yi, kunya ta kamani, amma na ga shi bai nuna alamar ƙyanƙyamina ba, ya ƙara bani ruwan na kurɓa, na ƙara kuskurewa ya ɗago na juye. Ya ɗauko burushin na ɗago hannuna na riƙe, "Zan iya." "A'a, kada ki wahala fa." Bazan wahala ba." Ya ƙura mini idanuwa,sai ya lumshe su tare da yin murmushinsa, ya buɗe idanuwan tare da girgiza kai. "No Yasmin, jikinki ba ƙarfi, ki yi haƙuri in kula da ke har ki warke,kina ga ya dace in bar yaran can su dinga kula da ke, alhalin ƙasa suke da ni, amma su ga wani ɓangare na sirrin matata? No,no,is not possible." "Wallahi zan iya." Ya miƙo mini burushin. "Na amince da ke." A

Table of Contents

Chapters

24 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});