Chapter 9
Chapter 9
nufa dan Fada Mata Qudurinshi, Kishingide ya sameta A Falo tana cin Yayan Itatuwa, Wata Kuyanga Tana Matsa Mata Qafa, Ya Zube Kan 2Seater Yana Kallan Fulanin, Fulani Ta Kalli Kuyangar, Tashi Kije. Ta Amsa Tareda Mikewa Dasauri ta Fita. Kallan dan nata tai "Yadai Lapia??" Yadan Dago "Bakomai Dama Akwai Maganan danakeso nafada miki neh" Ta Mike Ta Zauna Sannan tace "Ina Sauraranka" Dan Murmushi Yayi "Fulani na Dade inasan Parveen Anma narasa Ta Yanda zanyi na Fada miki, Pls ki Fadama mai Martaba Aje a Nema min Aurenta dan Allah" Da Mamaki Fulani keh Kallanshi "Yarima Kasan meh kake fada kuwa??" Kai ya gyada Yana Kallanta "Nasani Fulani, Idan ban Aureta bah..Ya taba Kirjinshi, Zan Shiga Cikin Wani hali pls ki Taimaka min" Kusan d'a da Mahaifi Tausayinshi Taji ya kamata Ta Kalleshi Cikeda Kulawa "Karka Damu Insha Allahu Parveen Matarka Ce, Kuma Nasan Bazata qika bah" Wani Qayataccen Murmushi Ya Saki "Thank Uh Fulani Shiyasa Nake Qara Sanki" Itama Murmushin Tai, Ya mike Yabar Falon Yana dariyar Mugunta... Tho Fah... _Shin Fans kun. Yarda yarima Ya auri Parveen??_ Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page1⃣2⃣ Wani Qayataccen Murmushi ya Saki "Thank uh Fulani Shiyasa Nake Qara Sanki" Itama Murmushin Tai, Ya mike Yabar Falon Yana Dariyar Mugunta... Hidimar Bude Asibiti ne Ya kankama, Gaiyata Sosai Mai martaba Yayi, daga Ciki akwai Gwamnoni, Sarakun, Yan Majilisu, Ya uwa da abokan Arziki, Haka Itama Fulani Tayi Gaiyata Sosai dan a Tayata Murnar Bude Asibitin Dan Nata... Umma nazaune Katin Gaiyata ta Sameta. Dukda Dama sunyi waya da fulani ta fada mata, Katin parveen Musamman Aka Kawo Mata daga Mai Martaba. Lokacinma Tana Schl, sai dt dawo tagani. Dan Tsaki Tai Ahankali Ta aje Katin Umma dake kallanta Sun Sanda Ta Dau katin Tace "Naga Kin Bata Fuska neh, jibi neh dai Kuma Tare zamu Tafi" Tsuke Fuska Tai Tana Kara Kallan Katin "Nifa Umma Inada Lectures Ranan" "Haba Parveen, Dan kinyi missing Lectures na kwana Biyu zuwa uku Shine meh?? Kinga Fah Wannan Gaiyatar daga Sarki Kabeer Take. Shi Yace Abaki, kinga bai kamata ki Watsa mai Qasa a ido bah" Gyada Kai Kawai Tai "Shiknan Allah Ya kaimu" Umma Tace "Ameen" Barin Wajan Tai Tana gungunai, Ita bawai Batasan Zuwa bneh, Kawai Saboda Maqiyinta neh Yasa batasn zuwan, Tsaki Taja Ta qarasa dakinta Tana nazarin Yanda zata Subulbule zuwan. Da Daddare Mai Martaba Yayi Kiranka, Ta Je Side dinshi Ta Gaidashi Tareda Neman Wajan Zama. "Gobe in Allah Ya nufemu da kaiwa zamu Tafi Masarautar Gombe dan Kinsan Akwai Taro na bude Asibitin Yarima Fardeen, Dan Haka Ki Zamana cikin Shiri" Bata Fuska Tai Tadan dago ta Kalli Mahaifin nata "Gobe fah inada Test harda Jibi, nima sai dazu ake Fadamin kuma idan banyi bah Zai Shafi result dina" Shiru Mai Martaba Yayi Nadan Seconds Sannan ya klleta "Shiknan Allah Ya bada Sa'a" Ameen Tace Tana Yar Murmushi Tashi Kije Abinki" Duqawa Tai Kanta Qasa "A Tashi Lapia" Sannan Ta mike Tabar Falon Cikeda Farinciki.. Haka kuwa akai Parveen batabi Su Umma bah, Umma Dai Sam Bata Yarda da test dinda parveen tace Suna dashi bah. Abin bah qaramin daure mata kai Yayi bah, tho mai yasa Parveen batasan Zuwa Gombe?? Da Wannan tunanin Suka Kai Masarautar Gombe. Gidan Cike Yake da Baki Yan nesa, an Karamasu Tareda Basu Masauki, Umma Kam tana Chan Wajan Aminiyarta Fulani. Washe Gari Aka Hau Biki A Chan Haraban Asibitin Mai Suna "Fardeen Specialist Hospital" Taro Yayi Taro, Kowa Daka gani Yana Cikin Farinciki, Bama Kaman Mai Martaba Da Bakinshi Yaqi Rufuwa... Yarima Nachan Zaune Cikin Abokanan Shi Sai Hira Suke, Wanda Yawanci Wayanda Sukai Karatu neh Tare, Anan Yake Fada Musu Ya kusa Aure. Niko Nace "Wah Yce Ya Bashi?? Yaushe Akai Maganan Balle" Yawancinsu Mamaki Suke Saboda Sunsan Yarima Baisan Kalmar Aure, Sanin halinshi Yasa kowa Yaja bakinshi Yayi Shiru, Saidai Fatan Alheri dasuka mai... Anci ansha, Sannan Aka Bude Asibiti, Mutane Suka Shishiga Aka Zagaya Ko Ina Na cikin Asibitin, Niko Ummy Abduol Sakin Baki nai Ina Kallan Asibitin, Kayan Aikin ban Taba Ganin Irinsu anan nigeria bah. Mutanen dake Wajan Sai Santin Asibitin suke Saboda Tsaruwanshi da kuma Kayan Aikin dake ciki. Addua Sosai Akai Sannan Kowa Ya Watse Cikeda Nishadi bayan An Raba Kyaututuka Kala kala. Su Mai martaba Gda Suka koma, Haka su Fulani da Ummah. Saida Aka Natsa Da Daddare Lokacin Duk baki Sun koma, Fulani da Umma Sai Sarki Kabeer da Sarki Khaleed Zaune a Side din Mai Martaba Sunata Hira, Kayan Itatuwane a Gabansu, Da Abinci kala kala. Fulani ce Ta Kallesu Tace "Damako Akwai Wani Abu danakesan Fadama Mai Martaba, Anma Tunda Ga sarki Khaleed Saina Fada Duka" Sarki Kabeer Ya Kalleta "Maganan Meh Fah?" Fulani Ta gyara Zama "Last Week ina Zaune Yarima Yazo ya Sameni akan Maganan Parveen, Yace Gaskiya Yana santa kuma Aurenta Yakeson Yi" Murmushi Sarki Khaleed Yayi Yace "Indai Wannan neh Bah Matsala ni nabashi" Itama Umma Murmushin Tai "Wannan Ai bah Abin Damuwa baneh. Allah Ya shige Mana Gaba Ya Sanya Alheri" Sarki Kabeer koh Tsuke Fuska Yayi "Niko Sam Ban Amince bah" Dukkansu Suka Juyo Suka Kalleshi da Mamaki Ya Gyada Kai Sannan Yace "Yarinya Mai Hankali kamar Parveen za'a dauka aba Fardeen??, Aa Bazai Yuwu bah. Salan Yaje Yayita Cutanta" Dan Murmushi Sarki Khaleed Yayi "Na Yarda da Tarbiyan Yarima, Nasan Bazaiyi Abinda Kake tunani bah" Girgiza Kai Kawai Sarki kabeer Yayi yana Murmushin Qarfin hali Umma Tace "Bah Damuwa Ranka Ya dade, Yarima Mutum neh Na Qwarai bashida Matsala" Shidai sarki Kabeer bai Qara cewa komai bah Akan magana, Haka suka Cigaba da Hiransu... _Shin Fans Kodai Sarki Kabeer naciki neh??_ Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page1⃣3⃣ Shidai Sarki Kabeer bai Qara cewa Komai bah Akan Maganan, haka suka Cigaba da hirarsu..Kwanansu uku Suka Koma, Ranan da Suka koma fulani ta iske Mai Martaba a side dinshi, Newspapern dake Hannunshi Ya Aje Yana Kallanta, Ta zauna Kan kujera tana Kallanshi, Dogaran dake gefenshi Yama nuni Suka Bar Falon Dasauri... Ya Kalleta Cikeda Tsokana "Uwargida Sarautar Mata, Yana Ganki neh Yau wani iri??" Fuskanta bah Fara'a Ta kalleshi "Ranka Ya Dade bai Kamata Kai Irin Furucin nan Akan danka bah" Ya Dago "Kamar Yha??" "Muna Magana Akan Yarima da Parveen kuma naji ka Sako wani Maganan" Murmusawa Yayi yana Kallanta "Rabiatu knan! Keh Kanki kinsan Hali irin na Yarima. Bah saina Fada Miki bah, Tho Fisabilillahi Jibi abinda Yayi Rannan Har Saida Ya Kwana Magarqama" Saurin Katseshi tai da Cewa "Wannan Ya wuce, Rayuwar dana nake Tunani, Yace bazai iya Rayuwa bah parveen bah. Ni kuma banason rasa shi" Dariya Mai Martaba Yayi qasa, Qasa yana Kallanta "Maida Wuqar Uwargida, Na gama Shirya Komai. Sati mai kamawa Insha Allahu za'aje nema mai Aurenta" Murmushi Fulani tai ta Harareshi da Sigar Wasa "Mai Makon ka fadamin tunda na Shigo ka barni inata Asarar kalamaina" Dariya Sosai Mai Martaba Yayi Suka Cigaba da Hirarshu Cikin Nishadi... Yau Monday Tushan Aiki, Tunda Asubah da Yarima Yayi Sallah bai Koma bah, abubuwan da Duk yake Buqata Yasa dogaranshi Suka Hada Mai a Wata Yar Jaka, Wanka Yayi Ya Shirya Cikin Yellow Suit da Black Shirt, Sai black
Table of Contents