Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

A Wani Masarauta Book 2 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Zuwa Airport. Kyauta Sosai Mai Martaba Yama Parveen har Tana Mamaki Saboda Yawanshi, Sallama Tai Musu Suka Hau Jirgi tana dagama Mai Martaba da Fulani hannu, Suma Hannun Suke daga Mata. Hawayene ya Gangaro mata, Tasa Hannunta na Hagu ta share Ta Shige Cikin Jirgin don inta Tsaya Kallansu Zata iya Fashewa da Kuka... Cikin Awan da bai wuce daya bah suka iso masarautar zaria, Already dogarai tareda bayin umma suna jiransu, Jirginsu na sauka suka Fito tareda shiga motan da aka tanadar musu zuwa gida. Sai Taji dama bata dawoba, ranta bah dadi har suka Qarasa Gda.. Umma Daketa Hidima dan Jiran Yar nata taji Shigowan motoci, Mikewa Tai Dasauri Umma Ta nufi wajan cikeda Farinciki, Kuyanginta neh Suke Take mata baya, Har sun kai Bakin Qofan Fita side din Umma, Sukai Kicibus da Parveen dake Qoqarin Shigowa Side din. Parveenta qarasa dasauri ta rungume umman nata tana dan dariya, Umma Cikeda farinciki Tai mata Sannu Suka qarasa cikin side din. Sun baje Anata Hira, Sunci Sunsha, Parveen ta nunama Umma kyaututukan da Mai Martaba Yamata, Godiya sosai Umma tai Tareda Farinciki... Saida ta huta Sannan Ta nufi Side din Mai Martaba bayan tasa Jakadiya tai mata Iso. Mai Martaba na ganinta ya Mike Cireda Fara'a Tareda bude Hannu, Dasauri ta qarasa ta rungume mahaifinta, Kanta ya shafa Yana mata Sannu da Dawowa. Dan dagowa tai ta Kalleshi "I Missed uh dad" Murmushi Yayi Shima yana Kallanta "I Missed uh My Princess" Dariya tasaki Ta zame jikinta daga nashi ta nemi guri kan Carpet ta zauna Hira suke Sosai Ya Tambayeta Fulani da Mai Martaba, Kyautan da mai Martaba Ya mata Ta fadama Mhaifinta. Yayi Murmushi "Ai sarki Kabeer Akwai Mutumci da datako" Itama murmushin Tai tanata bah shi Labarin Yanda Mai Martaba da Fulani ke Santa, Batabar Side din mai martaba bah saida aka kira Sallan Magriba Sannan.. *Bayan Sati Biyu* An Kammala Ginin Asibitin Yarima Budewa kawai Ya Rage, Sam Ran Yarima Baiso Hakan Bah, Anma bah Yanda zeyi dole Yayima Mahaifinshi biyaiya...Harynzu ya kasa Haqura Akan Abinda parveen Tamai, Dole Yadau Mataki. Dole Ya Rama, Saiya nuna mata Shi yarima fardeen neh kuma ya haifu, Sun Zauna shida Mahdi Abokinshi, Qara nusar Dashi Lalillin Hakan Mahdi Yayi yar Ya Yarda. Sun Yanke Shawaran duk Yanda Za'ayi, Yarima Ya Saki Lallausan Murmushi Sannan ya Kalli Mahdi "Kwanyanka naja Frnd" Shima Mahdin Dariyan yayi... Hadadden Motarda Mai martaba Ya siyan mata Qirar Dodge Ta nufa Dasauri Hannunta rataye da jakan Laptop, Sai Keyn motanta, Motan Ta Shiga Ta Fita Daga Gidan Dasauri. Gudu Take dan Takusa Yin Latti, Ahmadu bello University naga ta nufa dasaurinta, Horn taketa ma Student din Demostration da Sukai Cincirindo a gate sun shiga. Tsaki taja ta Qara danna Horn, Agogon Hannunta ta duba taga 7:56am Gashi 8:00am Takeda Lectures kuma Tasan Lecturan baida mutumci. Dakyar tasamu Ta wuce ta nufi depertment dinsu, Cikin ikon Allah tasamu ta shiga hall din, tana shiga lecturan ya shigo. Saida Tagama Sannan ta fito Tai Kicibus da Aminiyanta... Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page1⃣1⃣ Dedicated dis page to *Maradin Zazzau's Family..Alh Haruna Muh'd Jumare* Allah Yaja kwana Uncle👍🏻 Cikin Ikon Allah tasamu ta shiga Hall din, tana Shiga lecturan ya shigo. Saida Tagama Sannan Ta fito Tai Kicibus da Aminiyarta Hadeeza Yar Maradin Zazzau. Parveen ta Qarasa ta Rungume Deeza, Deeza ta hade rai ta Rungume Hannu "Lallai Parveen Kikai Tafiyanki, Saidai na kira naji kina Gombe" Dan Murmushi Tai Ta Marairaice Fuska "Am Sorry Bae! Wallahi Tafiyan neh Yazo min cikin Gagawa, Sai ana gobe Zan Tafi nasani. Buh ai nabaki Haquri" Tabe Baki Deeza tai Tareda Murmusawa "Na Haqurah Anma nima zan Rama" Parveen ta shafa Cikinta Tareda Yatsine Fuska "Muje Musamu Wani abu Yunwa nakeji" Ok muje. Motan Parveen suka Shiga Suka Fita daga cikin Schl din, Wani hadaden Eatry Suka nufa, Abinci mai Raida Lapia Parveen tai musu odering, Sunci Sunsha Deeza ta Kalli Agogon Hannunta "12 Dai Munada Lectures knsani" Itama Agogon Hannunta ta duba, Ai Yanzu 11:31am neh munada Sauran 30mint koh??" Kai Kawa Deeza ta daga Tana daddana Wayanta. Chan ta kalli Parveen "Ahan Bae Wai dan Allah dagaske kike abinda kika Fadamin Rannan??" Parveen ta dago Tana Kallanta "Nameh fah??" Maganarki da Yarima mana Tabe Baki Parveen Tai "Qwarai kuwa" Idonta ya Ciko da Kwalla ta Kalli Deeza "Tunda Nake a Duniyan nan Ba'a Taba Cimin Mutumci irin Ranan Bah, Yanzu dawani ido zan Kalli Mutanen Gombe??" Hawayen dake Maqale a idonta suka Gangaro "I Hate Him Deeza, I Hate Him! Tunda Nake Ban Taba Tsanan wani bah Kamar Yarima. Na Tsaneshi! Na Tsaneshi!!" Kukane Ya Kufce Mata, Deeza ta Dawo Kusada Ita ta zauna tana Lallashinta "Kiyi Haquri Pls, Ai kema kin Guma Masa. Nasan Wannan Abinda kikamai bazai Taba Mantawa dakebah Har Qarshen Rayuwarsa" Dagowa tai Idanunta Chabe Chabe da Hawaye tadan Mata Murmushi "Deeza Mazinaciya fah ya kirani" Ta Qara Rushewa da wani Sabon kukan Haba Bae! Kar wannan Ya daga miki Hankali, Ni Shaida ce akan Halinki. Karki Bari Maganganun Yarima Suyi Tasiri a zuciyarki Pls, Karki Damu Allah zai Saka miki kinji??" Kae Kawai Parveen ta gyada, Dakyar Deeza tasamu ta Lallasheta Sannan suka Bar Wajan Suka Koma Makaranta.. Yanma Lis Parveen ta Dawo Gida, Direct Side din Ummanta ta nufa, Dakinta tq shiga ta fada Jikinta Tana Yar Shagwaba. Umma Ta Kalleta baki Bude "Lallai Parveen sodai kike ki Qarasani ki Huta koh??" Turo Baki Tai Tana gungunai "Kinga Fah Fulani Tana Yarda Nahau Jikinta Har Barci nakeyi" "Iyeh! Tho ai Fulani kikace, Nikam bazan iya bah" Qara Turo baki tai Ta Mike "Ni Natafi tunda Bakyaso ina Hawa Jikinki, Kuma Ana qarayin Hutu zan koma Wajan Fulani nabarki" Bata jira mai Umman Zatace Bah tabar Dakin tana gungunai Murmushi Umman tai "Parveen! Parveen!! Allah ya Shirya" *Masarautar Gombe* Yau Mai martaba bai shiga Fadaba Yana Side dinshi Tareda Manyan baki da sukazo Ganinshi daga Kasa Kasa, Kowanne Yazo neh Dan Tallata hajarshi na Kayan Aiki na Asibiti, Wasu kuwa neman Aiki sukazo, Saida Ya Sallami Kowa Sannan Yasa Amai kiran Yarima. Ba'adau lokcibah sai Gashi, da Sallama ya shigo ya samu guri qasan carpet Ya zauna tareda Gaisuw, mai Martaba ya Amsa Fuska a Sake. Kallan Yariman Yayi "Ina Fata ka gama dukkan Wani Shirye Shiryenka dan sati mai zuwa insha Allah za'a bude Asibitin" Kanshi a duqe ya Girgiza kai "Na Gama ranka ya dade, Allah kuma Ya kaimu" Ameen Inji Mai Martaba Ya Qara kallanshi "Inaso na Hada Qayataccen Biki dan bude Wannan Asibiti, Kana iya Gaiyatan Abokanka na kusa dana qetare Duka dan Zuwa tayaka Murna" Qara dukar dakai Yarima Yayi Yanadan Murmushi "Godiya Nake Ranka ya Dade" Yarima Inaso Kazamo mai Gaskiya da Ruqon Amana Akan Aikinka, kazamo mai Juriya da Tawakalli. Karka zamo Cikin Ma'aikata Masu Wulakanci da Talakawa da Rashin Zuwa duba Marasa lapia dawuri. Dan Allah kai Qoqarin kiyayewa, Sannan Kazamo Maiba Na Qasa dakai Hakinsu daidai Kwargwado banda Cuta da muzgunawa." "Insha Allahu Mai Martaba Bazaka Sameni da Duk Wadannan bah, zanyi qoqarin kiyayewa." Murmushi Mai Martaba yayi "Allah ya maka Albarka" Ameen Ya Amsa Tashi Kaje Ya mike Yamai Sallama Yabar Side Din... Side din Fulani Ya

Table of Contents

Chapters

19 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});