Chapter 18
Chapter 18
parveen tai "Haba wasa kike yarinya. Tashi mu shiga Ciki" Sun dade suna hira har akai Sallan la'asar sannan suka shiga kicin dan daura girki. Suna girkin take bah deeza labarin hanata zuwa schl dinda yarima yayi... Dariya kawai deeza tai batace komai bah, har abin yaso bah Parveen haushi. Bayan magrib Yarima ya shigo gidan, Lokacin sun zaune kan dinning suna cin abinci, Jin hayaniya yasa ya qaraso wajan dinning din da sallam, Deeza ce ta amsa tareda gaidashi. Da fara'a ya amsa tareda tambayanta tazo lapia, Ta amsa da lapia lau. Dakinshi ya wuce kai Tsaye. Deeza ta kalleta "Ya dawo baki kai mai abinci bah" Tsaki parveen tai ta cigaba dacin Abincinta "Keh fa matsalata dake knan bae, Bai kamata bah abinda kikeyi. Kada ki biye halinshi ko kin manta maganan da mukai dazu" Mikewa deezan tai ta shiga kicin ta hado abinci a tray ta ajema parveen a gabanta "Pls tashi ki kai mai" Turo baki tayi "Nifa indai abinda ya kawoki knan gwara gobe da sassafe ki kom gida. Nifa da kika gani bana shiga dakinshi, yanzu idan nakaimai saiya raina ni" Kafadanta ta dafa "Bah wani raini bae, Kiyi qoqari ki gyarashi zaki samu lada, ina miki kwadayin ladan da zaki samu nan gaba neh".. Turo baki parveen tai ta mike tareda daukan Trayn har ta doshi dakin deeza tace "Ki Tambayeshi akan maganan zuwa gaida fulanin" Batace komai bah ta qarasa dakin, Bata tsaya knocking ba ta tura qofan ta shiga kai Tsaye. Har ya zame towel dinda ke Jikinshi yana qoqarin sa Kaya ta shigo, Ihu ta Saki Tareda rufe idonta, ta saki trayn ta fita dsauri. Dariya Sosai ta bashi, Kayan Ya qarasa sawa Ya zauna bakin Gadon Yana cigaba da dariya.. Qanqame Deeza tai idonta a rude tana ihu, rufe mata bakin tai Tana jijigata "What?? Menene??" Sakin ta tayi ta ruga daki dagudu. Girgiza kai Kawai tayi ta zauna tacigaba dacin abincinta. Gado parveen ta fada tana maida numfashi, Ganin Surar Yarima tayi cikin idonta. Dasauri ta qara rufe ido tana Turo baki. A Hankali ta furta "Allah ya isa ban yafe bah" Kwanciyanta tayi tana chating har deeza ta shigo. "Wai wane irin abu wannan parveen??" Tashi tayi ta zauna tareda hade rai "Allah ya isa deeza, kin cuceni Wallahi. Gashi kinsa naje..kasa qarasawa tai ta ja tsaki" "Nidai yanzu kin tambayeshi maganan Zuwa gaida Fulanin" "Nifah karki dameni deeza, bazan koma dakin nan bah" cewar Parveen Tsaki deeza taja ta mike "Natafi Kallan Players a bollywood" Wup Parveen ta tashi tana washe baki "dan Allah dagaske??" Batace mata komai bah ta bar dakin, itama binta tayi zuwa Falon. Zama sukai suka soma kallo bah wanda ya qara cewa kowa komai, chan sukaji bude kofar dakinshi, ya fito ya qaraso falon. Parveen ya kalla Fuskan nan a daure "Hu wil clean up dah mess" Tsaki taja ta mike dan tasan zai iya dizgata a gaban deeza. Dakin ta shiga ta soma tattara wajan, tana gamawa ta dawo ta tarar dashi zaune a falon sunata hira da deeza kamar dama sunsan juna. Guntun tsaki taja tana kallan deeza "Ni natafi na kwanta" juyowa tai tana kallanta "Bazaki tsaya ki qarasa kallan bah??" Girgiza kai tayi alamar Aa Harta juya taji muryan Yarima yana cewa "Tashi to kuzo muje ki gaida fulanin sai naraka ki koh" Parveen ta qarasa daki ta zauna bakin gado, deeza ta shigo tana kallanta "Tashi muje pls ya rakamu, kinga ma dare ya soma" Dakyar ta lallaba parveen ta mike tasa hijabi suka fito. A hanya Deeza da Yarima sai hiransu suke parveen ko ta hade rai tana bayansu suna gaba.. Tare suka shiga side din da yarima, deeza da parveen suka zauna kan Carpet tareda gaida Fulani, Parveen ke fadama Fulani wacece Deeza a wajanta. Ta Taresu dakyau sun dade suna yarima ya fito falo ya zauna yana kallan news, Sai wuraren sha daya suka baro Side din, Kamar dazu hiransu sukaitayi suka barta a baya, Haushi abin ya bata sosai. Koda suka qarasa side din ko inda deeza take bata kalla bah ta wuce daki fuuu.. Tho fah kodai Parveen kishi take🤔?? Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤👑 By *Ummy Abduol* Page2⃣5⃣ Koda suka qarasa side din ko inda deeza take bata kalla bah ta wuce daki fuuu.. Ganin ran parveen ya baci yasa tama Yarima sallama ta shigo dakin. Kayan barci tarar parveen nasawa, ta qarasa ta zauna bakin gadon tana kallanta. "Lapia?? Naga ranki ya baci" Aiko kamar jira take tako hayayaqo mata "Ina ruwanki dashi?? Menene hadinki dashi?? Kin wani barni ni kadai kinata wani washemai Baki waike kuna hira" Dariya sosai abin yaba deeza, ta dade tana dariya hakan yasa parveen ta qara quluwa. Saida Ta gama Sannan ta Kalleta "Parveen kishi??, Ana cewa ba'asan yarima anma gashi ana kishinshi" Tsaki parveen taja tana yamutse fuska "Allah ya kiyaye nai kishin yarima. I hate him!" Dan murmushi deeza tai "Umm zakizo kiban labari".. Pillow parveen ta wurga mata "Banasan iskanci deeza, Bakisan yanda na tsani guy din nan baneh" Shawarwari deeza ta dinga bah Parveen Har barci ya daukesu.. Da Safe suna Kicin yarima ya leqo, Murmushi deeza tamai Sannan tace "Morning" Morning shima Yace Yana Kallan Parveen, Fuskanshi bah yabo bah Fallasa Yace "Haba Amarya bah Gaisuwa" Dagowa tai ta kalleshi da mamaki Gira ya daga mata, tai saurin kauda kai tareda hade Rai "Good Morning" Kintashi Lapia??" chewar yarima Batareda ta kalleshi bah tace "Lapia" Deeza ya kalla Yana yar murmushi "Frnd idan kun Gama ki Shirya xan kaiki yawo tunda yau saturday" Murmushi tai tana Kallanshi "Thank you very much Frnd" Baice komai bah Yabar Kicin din. Tsalle Deeza tai Tana cewa "Woaw! Kamar yasan abinda nakeso knan, Allah yarima nada kirki. Kece dai baki gane hakan bah" Dogon tsaki Parveen taja tacigaba da abinda takeyi. Murmushi Deeza tai tareda girgixa kai.. Suna Gamawa Deeza ta shirya Ta Kalli Parveen, pls ki tashi muje. Mugun Kallo ta bita dashi tareda jan tsaki "Bah inda zani, keh dai da kike uwar yawo sai kin dawo" Bah Yanda Deeza bataiba Akan Parveen tabisu taqi, Hakana ta haqura suka Fita itada Yariman. Yawo yakaita Sosai, Sun jaje wurare dayawa, dan Zaman da Yayi da Deeza ya samu Labarin parveen sosai da Halayenta. Basu dawo gidan bah Sai Qarfe tara na dare, kwance suka samu parveen kan 3seater har ta soma barci. Dagudu deexa ta qarasa inda Parveen take tai tsalle ta fada kanta.. Ihu ta saki tareda tureta, Dariya Sosai Abin yaba yarima yabar Wajan zuwa daki yana cigaba da dariya "Yarinya sai Rashin kunya ga shegen Tsoro" Tsarabanta Deeza ta bata, taqi amsa, saida tace mata da kudinta ta siyan mata sannan ta amsa tana dubawa. Abinci ta hada takai mai daki, Wannan karan knocking tai, saida Ya bata izini Sannan ta shiga, Gabanshi ta ajiye Ta juya zata Fita. Muryanshi ta jiyo yana cewa "Were are you going bayan mijinki na buqatarki a kusa dashi" Qarasawa tai Zata bude kofan taji yace "Haba Mallama uwar Malamai, Koh kin manta Malaiku na Tsinewa Macen da ta qauracewa Shinfidar mijinta" Juyowa tai tana Kallanshi gabanta na dukan uku uku "Nibah Malama bace, Har yanzu ni daluba ce. Bana
Table of Contents