Chapter 10
Chapter 10
tie. Qafafuwanshi Cikin Wata Hadadiyar Black cover. Ga Gashin.nan Yasha Gyara Kamar Na india. Kayan sun Matuqar Amsarshi, abinda da Farin Fata, Ni Kaina Ummy Abduol Saida Ya Burgeni. Yana Tafe Dogaranshi na Takemai baya Rike da Breifcase dinshi.da kuma Wata Yar Jaka, Dakin Fulani Ya Shiga Ya gaidata Ta Kalleshi Tana Yar Fara'a "Yau Za'a Fara zuwa asibiti??" Kai Kawai ya Gyada Yana Danna Wayarshi "Tho Allah ya Tsare Ya kiyaye Hanya, A Kula Dan Allah da Haqqin mutane. Sannan Ka Tuna Ran dan Adam Kake Aiki akai Banda Sakaci" Mikewa yayi Yana duba Agogon Hannunshi. "Insha Allah Fulani" Fatan Alheri tamai ya fito Ya nufi side din mai Martaba dan Safiya neh bai Isa ace Yaje Fada lokacin bah Zaune Ya Sameshi Yana Lazumi, Saida Ya Iddar Sannan Ya Amsa Yamai Addua Sosai Tareda fatan Alheri, Ya Fito Ya Shiga Motarda Aka Tanadar Mai Dan Zuwa Aiki, Dogaranshi Suka Shiga Dayan Sai "Fardeen Specialist Hospital" *********** Parveen Na Cigaba da Karatunta Cikin Kwanciyar Hankali da Annasuwa, Koda Su Umma Suka dawo basu Mata Magana Akan Yarima bah, Jira suke Sai Sanda Akazo neman Auren Sannan ta Sani, dukda ita Lokaci Zuwa Lokaci Takan Tuna Yarima Sannan Taji Gabanta Ya Fadi. Addua Take Sosai dan neman Tsari daga Sharrin Yarima. Tana Yawan Fadama Aminiyarta Deeza Halin datake ciki, Kwantar Mata da Hankali koda Yaushe takanyi Tareda Jadada mata Dagewa da Addua... Cikin Satin Nan Yarima Yaba Aikinshi Mahinmanci Sosai, Kuma Yana Matuqar jin Dadin Asibitin, Kasancewarshi Gynecologist (Likitan Mata) hakan Yasa yawan Harka da Mata, Wasu daga Cikin patient Masu zuwa Asibitin Suna Zuwa neh Kawai dan Ganinshi Saboda Yanda Sukejin Labarin Haduwarshi, Hakan Yasa Neman Mata wajan Yarima Ya Qaru "Allah Ya Kyauta"... Ranar Juma'a Da Safe Sarki Kabeer da Tawagarshi Suka nufi Kasar Gombe, Tun a Airport suka Hadu da Tawagar Sarki Khaleed da Sukazo tarbarsu. Suna Sauka Suka Shiga Mota Suka Nufi Gida, Saida Akai Sallan Juma'a Sannan Suka Samu Suka Qebe, Bayan sunci Sunsha, Umma Tazo Ta gaida Mai Martaba sun dan Taba Hira Sannan Tabar Falo, Sarki Kabeer sai Tambayan Parveen Yake, Mai Martaba Yace Tana Makaranta.. An Tsaida Maganan Aure, An Bada Sadaki Naira Dubu Dari. Sannan Ansa Ranar Biki Wata Daya, Sarki Kabeer bai Kwana bah Suka Juya Tareda Tawagarsa Cikeda Farin Ciki, Sun Koma Gida Lapia. Fulani Ta Iske Mai Martaba a Side dinshi, Bayani yamata duk Yanda Akai, Farin ciki Tai Sosai Ta mike Tana Cewa "Yau Yarima Zaisha Albishir" Dan Dariya Mai Martaba Yayi Tadan Rusuna "Ka Huta Lapia" Ta fita daga Dakin Fara'a Kwance Kan Fuskanta... Yarima na dawowa Fulani tasa A mata kiranshi, Ya qaraso Side din yana gungunai. Gefenta yasamu ya Zauna yana Turo baki. Ta kalleshi tana Murnushi "Kasan Dalilin Kiranka??" Kai Ya gyada Alamar Aa Qara Murmushi tai Tana Kallanshi "Mai Martaba Yaje Qasar gombe Yau Akan magananka da Parveen" Gyara Zama Yayi Yace "Tho ya Ake Ciki fulani??" Sumar kanshi ta Shafa "An Gama komai biki nanda Wata Daya" Dariya Ya saki Ya Rungume Fulani "Much Thanks Fulani, Shiyasa Nake Sanki" Ya Mike "Barinje Naima Mai Martaba Godiya" Bai Jira mai Fulani zatace bah Ya fita Yana Fara'a Kamar dagaske.. Parveen Bata dawo gidan bah Sai Yanma, Saida Taci Abinci ta huta Sannan Jakadiya Ta Shigo, Rusunawa tai ta kwashi Gaisuwa Sannan Tace "Ranki Ya dade Mai Martaba Nasan Ganinki" "Tho Tace" Jakadiya tabar dakin Ko Minti daya bata Qaraba Ta mike ta Nufi Side din Mai Martaba da Sallama.. Ya Amsa Ta nemi guri ta zauna.. Shiru ne ya Biyo baya. Chan Ya Dago Ya kalleta Yace "Parveen a Matsayinmu nida Mahaifiyarki, Munada Daman da Zamu zaba Miki Miji wanda mukaga ya Dace da Tsarin Rayuwanki, Mai Hankali mai Tarbiya dan Gidan dattako. Gabanta neh ya fadi ta dake Tana Cigaba da Sauraranshi... Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page1⃣4⃣ Dedicated dis page to *My Facebook Fans* Allah Ya barmu Tare.. "Parveen a Matsayinmu nida Mahaifiyarki, Munada Daman Da zamu Zaba Miki miji Wanda Mukaga Ya Dace da Tsarin Rayuwarki, Mai Hankali da Tarbiya dan Gidan Dattaku. Gabanta neh ya Fadi ta dake Tana Cigaba da Sauraranshi "Dan Haka A Matsayina na Mahaifinki na Zaba Miki Miji wanda Nasan Zakiyi Alfahari dashi ko bayan bah Raina" Kanta na Qasa Batace Komai Bah "Ina Fatan zayi Na'am da Wannan Auren, Anma Inaso ki Fadamin idan da Wanda Kikeso. Duk da Nasan Its Too late Saboda Har an Kawo Sadaki an kuma Sa Rana Nanda Wata Daya" Hawaye ne Ya fara Zarya a fuskanta, Qoqarin boyewa Tai Kar Ya gani.. Dan Murmushi Yayi yana Kallanta. Bakicemin Komai bah Parveen Kanta Na Qasa Muryanta na Rawa Tace "Ranka Ya Dade banida Tacewa. Na Amince, Zabinka shine nawa kuma ina godiya" Murmushi Mai Martaba Yayi "Allah ya Miki Albarka, Tashi kije" Ameen Tace Tareda Mikewa Tabar Falon.. Tana Fitowa Ta Fashe da wani Matsanancin kuka, Ita bah Kukan Auren da Mai Martaba Zeyi mata bneh Aa, kukan Karatunta Take. Haka Ta Qarasa Side din Umma Tana kuka Sosai, Jikinta ta xube Tace "Umma Meh Yasa mai Martaba bazai bari na Qarasa makarantana Bah Sannan Ya Auramin duk wanda nakeso??" Shafa Kanta Umma tai "Kiyi Haquri Parveen, Da nan da Gidan Aurenki duk daya neh. Kamar Yanda za'a kula dake anan Haka a Chan, karki damu kanki kinji??. Maganar Makaranta kuma Za'a miki Transfer Zuwa Chan Garin Sai ki Cigaba da Abinki" Batace Komai bah Ta mike Tana Kuka Sosai Tabar Dakin.. Kwana Tai Kuka, Kota Kan wanda Za'a Aura mata batabi Bah. Washe Gari da Safe Tanada Test Dakyar Ta Tashi ko breakfast batai bah tai Wanka Ta Tafi, Idanunta Luhu luhu. Saida Aka Gama Test din Sannan Suka Hadu da Deexa. Kallanta Tai Da Mamaki "Meya Sameki?? Daga Ganin idanunki kinyi kuka??" Kamar Jira Parveen take Ta Fashe Da Kuka Tana Kallan Deeza. Hannunta Ta Deeza ta kama suka Shiga Motanta, Kuka Parveen Take Sosai Dakyar Deeza Ta lallasheta Ta danyi Shiru "Pls Bae Banasan Ganinki cikin Wannan Halin Fadamin menene?? Ko Yariman neh kuma" Girgiza Kai Parveen tai Hawaye na Cigaba da Zuba "Mai Martaba neh Yakeso Yamin Aure" Dafe Kirji deexa Tai "Aure!? Y??" Girgiza Kai Tai "Nima bansani bah Deeza, Niba Auren da zaimin ke damuna bah, Karatuna. Ke kanki kinsan Yanda Naci buri akan Karatun nan, Inaso na Zama Gynecologist. Inaso na Taimaka ma Yan uwana Mata. Dafata Deeza tai "Wannan Bah Abin damuwa bneh Bae, Ko kina gidanki Zaki Iya Yin Karatunki indai Mijinki zai Yarda" "Ta Yaya Deeza??, Yanda Fa Umma Kemin Bayani Ba Inan Garin Zan Zauna Bah?? Tho ya makomar Karatuna??" Shiru Deeza Tai Tana Nazari "Karki Damu Pls, Allah Yana Tare Dake. Ki Cigaba da Addua Kinji??" Kae kawai Parveen ta Gyada batareda tace komae bah Haka Tai Yinin Ranar Hankalinta ba Akwance Yake bah.. Kwanaki Sun ja, Anata Shirye Shiryen Biki daga Duka bangaren Biyu. Har Yau Parveen batasan Wanda Zata Auraba kuma Bata Tambaya bah. Iyayen neh Kawai ke Shirye Shiryensu, Yarima ko da Parveen bah abinda Suke Shiryawa Bama Kaman Parveen da Tunda Akai mata Maganan Auren Batada Aiki sai kuka Sai tunani, Makarantan ma Ta daina Zuwa, Kullum idan Deeza ta tashi makaranta Sai Tazo ta Lallasheta...
Table of Contents