Chapter 2
Chapter 2
Martaba. Suna Cikin Hiran Bayan Rabo Yarima Fardeen Yayi Sallama Ya Shigo tareda Rakiyan Abokinshi Adnan da fadawanshi, Zama Sukai Kan Carpet din Falon Sannan Suka Soma Gaida Sarki, Sarki Khaleed Ya kalli Yarima Cikeda Kulawa Yace "Yarima an Girma Ya Karatu??? Ka Kammala neh?" kai Ya gyada Sannan Yace "Angama Ranka ya Dade", Sarki Khaleed Yashafa Kanshi Yace "Allah yamaka Albarka" Yarima Ya amsa da Ameen Sannan Suka Mike Suka Bar Falon... Side din Yarima Suka nufa shida Abokinshi, har sunkai Bakin Kofan Ya Daga Hannu Batare daya Juyoba Fadawan dake Take musu baya suka Bar wajan Dasauri, Adnan Ya bude kofan Suka Shiga. Kan Three seater Ya Fada Tareda Sakin Wani dogon Tsaki, Adnan Yakalleshi Cikeda Mamaki Yace "Deen Yadai Whts Wrong?" tsakin Yakuma Ja Sannan Yace "Wallahi Mai Martaba neh Waishi dole sai nayi aiki a Nigeria nikuma Sam Banasan Zaman Kasan nan" adnan Yadan nisa Sannan Yace "Buh Yarima Yan Kasan nan nabuqatanka matuqa, Suna neman kwararun Likitoci Kamarka, Shiyasa Zakaga Mutane na fita Qasashen Qetare Ganin likita. Kuma Bawai dan Fararen sun Fimu baneh Aa! Zakaga Yawanci mah Baqaqen Fatan neh Anan tho.... Saurin Katseshi yayi ta hanyar dagamai Hannu, Dasauri Yayi Shiru, ya Mike Sannan Yace "pls katashi kaban waje I need privacy" Mikewa Adnan Yayi dasauri dan Yasan Halin Abokin nashi Yamai Sallama Ya bar Side din... A Dakin Fulani Suka Yada Zango itada Yar nata, Hadimai Sai Hidima suke da Parveen kamar zasu hadiyeta, Hira Suke Sosai Cikeda Farinciki, Sunci sunsha Sannan Jakadiya ta nunama Parveen Dakinta Sannan ta Nunama Altine Nata dakin..Kwanan Sarki Khaleed biyu Ya Koma.. *Bayan Kwana Biyu* Cikin Sauri Yarima Yafito fadawanshi na takemai baya, hannunshi Riqe da Agogo yana qoqarin Daurawa, Daidai Nan Parveen Tafito daga dakinta Cikeda Farinciki Tana Waya da Ummanta, Hankalinta Sam baikai kanshibah, Shima haka. Jitai Tayi karo da mutum Ta dago Zara xaran idanunta dasauri suka hada ido, Hade Rai Tai, Hadiye Yawu tai dakyar Da Qarfin hali Tace "Haba Mallan baka Gani neh" da Mamaki Yarima Ya Kalleta Yace.... Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 A WANI MASARAUTA 🏤🏤🏤 👑 By Ummy Abduol Page3⃣ Jitai Tayi karo da mutun Ta dago Zara Zaran idanunta dasauri suka hada ido, Hade Rai Tai tah hadiye yawu dakyar. Da Qarfin Hali Tace "Haba Mallan baka gani neh??" da Mamaki Yarima ya Kalleta Yace "Keh Har kin Isah ki Hanani Yin Abinda nagadama a masarautar Ubana" Cikeda Tsoro Tace "Gani nai kana abu irin na Jahilai dabasuje Islamiya bah" Zaro ido Yayi karo na Farko A Rayuwanshi Ya daga Hannu Cikeda Fushi Zai saiga Fulani, dasauri Yabar wajan Yana Huci, fulani Ta qaraso inda Parveen ke Tsaye Tace "Lapia meh ya Faru?" dan Murmushi Tai Sannan Tace "Bkmai dama Tunda nazo bamu hadu baneh Sai Yanzu" Kallanta Fulani tai na Alamar Rashin Yarda Tace "Shknan kije ki Shirya nasa Sarkin mota yakaiki Yawo" Tsalle Tai Tareda Rungume Fulani tace "Shiyasa nake Qara sanki fulani" Dakinta tai dagudu tabar fulani nan Tsaye Tana Dan Murmushi... Dakatar da Bayinshi Yayi dae dae kofar Fadan ya shiga da sallama, Mutanen Yan fada dake Zazzaune suka amsa mai Ya nemi guri ya zauna cikeda ladabi Sannan Ya soma kwasan Gaisuwa. Dogarin Dake gefen Sarki Yace "An Gaisheka Yarima! Sarki ya amsa" Waziri dake Chan gefe Ya kalli Mai martaba Yace "Allah ya Taimakeka Yarima Ya iso" Mai Martaba Yamai nuni dan Haka Ya Cigaba da cewa "Dama Maqasudin Kiranka Fada Shine, Sarki Yace a Qara jadadama ba Komawa Qasar Farin fata dan Cigaba da Aiki, Yanzu haka Ya bada kwangilan Gina maka Asibiti naka na kanka a nan cikin Gari" shiru Fadan Yayi Alamar ana Jira Aji Mai Yarima Zaice, Murya chan Qasa Yace "Duk Yanda kace Haka za'ayi Mai Martaba Godiya nake" Dogarin Dake gefen Sarki Yace "Yarima ya gode" Waziri yace "Zaka iya tafiya". Mikewa Yayi jiki a Sabule Ya Fice daga Fadan, Bayinshi dake Waje suna jiranshi suka take mai baya har side dinshi, Daidai bakin kofa ya musu alama dasu tafi, cikin Rawar jiki suka bar Wajen Ya shige Falonshi... Maganar Parveen ke Yawomai cikin Qwaqwalwarshi, Kai Kawo Yasoma Yi Cikin Katafaren Falonshi lokaci lokaci Yakan furzar da iska Tareda naushin Tafin Hannunshi na hagu, A hankali Ya Furta "Harni Kamarni Yarinyan nan zata kira jahili?? Lallai batasan Yarima fardeen bah" Yana cikin Safa da marwanshi Abokinshi kuma Dan uwanshi Bilal (Yaran waziri) ya Shigo da sallama ya zube kan kujeran tareda Fadin Wash! Koh Kallo bai Ishi Yarima bah, Ganin safa da marwan da yake Yasa yace "Wai Yaneh Yarima meke Faruwa??" Tsaki Yarima yaja Baice Komai bah, Bilal Ya kyalkyale da Dariya Yace "Koh duk akan Maganan Rashin Komawa Egypt neh??, Mallan Kasha Zamanka A nigeria" Ya Qara Fashewa da Dariya Yace "nasan Matsalarka bah komawa balle a cigaba da Duniyancin da Aka Saba" Dariya ya cigaba dayi harda riqe Ciki. Yarima ya Kalleshi Cikeda Quluwa Yace "Bansan iskanci Bilal, Danma fah kaine da Yanzu Nasa an zanemin kai" Tsagaitawa da Dariyan Yayi Yace "Nayi shiru dan nasan Bah mutunci ka cikaba yanzu kasa a suburbudenin Anma a Waje dan A Cikin gidan nan kasan ban Tabuwa, Yanzu Dai Fadamin meke Faruwa??" Batareda Ya Kalleshi bah Yace "Bah Matsalarka bace" Bedroom ya shige Bilal ya kwanta kan 3seater Ya Soma barci... Yinin Ranan Yarima Bah abinda Yakeyi Sai Saqawa da kwancewa, lokaci zuwa lokaci yakan Maimaita Kalmar "Jahili" Sam Yama Manta da Maganan da Aka fadamai a fada akan qin amincewa daya koma Kasar Waje. Yanzu mah haka Yakai kusan Awa biyu a Zaune Yana neman Mafita, Chan Ya saki wani Lalausar Murmushi wanda ya Qarawa Fuskarshi Kyau Yace "hakan mah Za'ayi" Ya mike dsauri Ya Shiga Toilet dan Watsa Ruwa... Wuraren Qarfe Takwas na dare Parveen zaune itada Fulani Suna Hira, Hadimai Nata Hidima dasu Bangaren Kayan Marmari abinci kala kala, dadai Sauransu, Fulani Tana Kishingide Ana Tausa mata Qafa, Ta Kalli Parveen dake Tauna Apple a hankali tana latsa wayanta Tace "Parveen wai yaushe zamuzo musha biki?? Dan Murmushi Tai Tareda sunkuyar dakai. Fulani ta murmusa Tace "Allah ya kaimu lokacin, Dai Dai nan Yarima Ya shigo Tareda Sallama, a Tare suka amsa, ya zauna kusada qafan Fulani Yace "Yanzu Fulani Abinda akamin Ydace knan??, A hanani komawa. Nidai Gaskiya inaso na koma" qurrri Tamai Tana Kallanshi Harya gama ta hade rai Tace "Tashi Kaban guri" Da mamaki ya kalleta Yace "Haba Fulani keda nazo na fadamiki damuwata ko naji sanyi" kofa ta nunamai sannan Tace "Idan bazaka fita bah ni zan bar maka dakin" Mikewa Yayi Sah sah Yabar dakin, Duk abinda Yake Faruwa Parveen na Zaune tai Kamar batajishi bah tanata latsa wayanta har ya fita... Yau Parveen Ta tashi dasan zuwa yawo, dan haka tana wanka ta shirya cikin atamfa ja mai Ratsin baki, Dinkin Riga da Skirt kayan sun amsheta Sosai, Dakin Fulani ta nufa Altine na biye da ita riqe da Wayoyinta da Jaka, Da Sallama ta Shiga ta rusunna ta gaidata Sannan ta fada mata, Fatan Alheri Fulani tai mata Suka Fito, Drivern dazai Kaiso Ya qaraso Dae dae qofan dazasu fito Yayi Parking, Duk abinda akeyi Yarima Nachan cikin Runfar Shaqatawa Yana Kallansu, Cikin isah Parveen Ta fito Altine Tai saurin Bude mata qofan Ta shiga, Sannan
Table of Contents