Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

A Wani Masarauta Book 2 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

na Safe, Ta mikr dasauri Tace "Umma Ina Zuwa" Umma ta gyada kai. Kitchen ta nufa inda Ma'aikata ke girki, Altine tasamu a Wajan Ta kirata Suka Qebe, Altine Tace "Ranki ya Dade komai yatafi Yanda Akeso, Wacchan ta nuna Wata baiwa Tace "Itace komai na Dangane da Girkin Yarima Yake Hannunta" Parveen ta tabe Baki Tace "Tho Yanzu ya Ake Ciki??" altine Ta Sadda kai Tace "Ranki ya Dade komai yatafi Yanda Akeso" dan Murmushi Parveen tai Tace "I hope komai Yatafi yanda akeso" Altine tai Murmushi Tace kwarai Kuwa Ranki Ya dade" kyada Kai Parveen tai Tana Murmushin Mugunta. _shin Fans meh Parveen ke qoqarin yi??_ Miqewa yayi zaune Tareda miqa, Yarinyan dake kusa dashi Ya Kalla tareda murmushi, Yau bah ta rannan bace, daga Gani bama musulma bace. Ya shiga Tashinta A hankali yace "wake up!" ta mike Tana Yamutse Fuska, Yadan Hade Rai Yace "You have to lyv now" ta marairaice Fuska tace "why pls, Am Stl sleepy n tired" tsawa ya daka mata ta mike dasauri ko wanka batai bah tasa kayanta, Bandir din Yan Dubu ya wurga mata Ta fita Tana Gungunnai, Tana Bude Qofan Falon Tai Kicibus da Bilal, Matsawa yayi dasauri Yabata wuri ta Wuce. Binta yayi da kallo tareda Girgiza Kai Sannan Ya shiga Falon, Kan kujera ya zauna ya kunna kallo, Saida Yarima Yayi wanka Sannan ya fito falon, Bilal yabishi da Kallo ya girgiza kai, yarima Ya dake Yace "meye kake wani kallona kana girgiza kai" Bilal Yace "Yarima Ina jiyema Ranan da Mai Martaba zai San kana kawo mata Gidan nan" tsuke Fuska Yayi yace "Tho idan ma yagane ai inace bah damuwanka bneh" Bilal Ya girgiza kai Yace "Kai Bakasan Abokin Barawo akance Barawo baneh" bata Fuska Yayi yace Kai Kajiyo... Cikinshi ya shafa yace "Am Hungry wai Har Yanzu Banzayan nan basu kawomin break bah" koh kallanshi bilak beyi bah yacigaba da kallanshi, Fridge ya bude Yaga bah komai, yaja tsaki Ya mike yadawo Falon. Sha daya Dai dai Ma'aikaciyarshi Ta Shigo dasallama ciqe da tray dauke da nauikan Abinci kala kala, Wata ma Ta shiga da Wasu, Saida Suka Kwashi gaisuwa koh kallansu beyi bah Sannan Suka Aje a dinning, Altine Ta Shigo da Sallama Dauke da Tray da Ruwa akai da chi- exotic akai, Sam Bai lura da ita bah har suka aje suka Fita... Bilal neh ya mike Yayi Serving dinsh ya koma ya zauna ya cigaba da kallanshi, Abincin Yaci sosai saboda Yunwan dayake ji, Sannan Yasha Exotic dinda Aka zubamai a cup, kurba daya yayi ya Aje Saboda Ji dayayi ya chanza Taste, Harya Mike Ya Qara daukan Cup din Ya kwankwade Saboda bai Sama Cin Abinci baisha bah, Ga mamakina Qara Zubawa Yayi ya shanye ya Aje cup din. Niko ummy Abduol nace Kodai Saboda Hadimar Parveen ce ta kawo??? Altine na fita ta nufi side din Parveen tana murmushi, Parveen cikeda zumudi Tace "Ya akai Altine" Altine Tace "An gama Ranki ya dade" Tsalle Parveen tai tace "Yauwa Haka nakeso" Sai kuma mu jira cika aiki kawai, Itama Altine Murnushin Tai... Tho Fah Fans meh Parveen ke qoqarin yi??? Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page7⃣ Tsalle Parveen tai Tace "Yauwa haka nakeso" Sai kuma mu jira Cika Aiki kawai, Itama Altine Murmushin tai, Parveen tace "Muje Wajan Umma" tana tafe Altine na take mata baya, Lokaci lokaci takan saki Murmushi har suka qarasa Side din, Sun baje Umma nata bata labarin yanda Tai kewanta Sanda Bata nan, Parveen koh saima Umma dariya take, lokaci lokaci Takan duba Agogo. Har Umma takaiga cewa "wai Parveen wannan duba Agogon Fah??" tai Murnushi Tace "Bkmai".. Bilal idonshi nakan kallan dayake Coz ana Favorite hindi film dinshi "Mujshe dosti karoge", Yarima koh tunda ya zauna yake jinshi wani iri ya mike yana dan tangaji Yace "Bilal idan kagama ka tasheni, Zamu fita da mai martaba anjima Around 12, am Slipy" kai kawai Bilal yadaga batareda Ya Kalleshi bah, Daki ya Shga dakyar Ya fada kan Gado, Barci neh mai nauyi ya daukeshi, Sam Bilal ya manta Yana Gama Kallanshi Yabar Side din. Shiru shiru Mai Martaba Baiga Yarima bah dan Haka Yasa amai kiran Jakadiya, Ta karasa Fadan dasauri, Umartanta yayi ta kiramai Yarima, Amsawa tai ta nufi side din Yarima, Kai Tsaye Ta shiga Side din, Bah kowa a falon don Haka Tai knocking a kofar bedroom din, Nanma Shiru, Rakai Minti goma Tana Knocking jin shirun yayi yawa Yasa Ta murda ta shiga da Sallama.. Kwance ta Sameshi shame shame kamar Matacce Yanata Barci, Mamakine Qarara a fuskan Jakadiya, Ta shiga Tashinshi a Hankali tana Kiran sunanshi Yarima! Yarima!! Shiru, Dakyar tasamu ya Bude ido dakyar, Tace "Mai Martaba Nasan Ganinka ranka Ya dade" cikin Muryan Maye Yace "dallah Mallama Getout, Kije Kice Baza'azo bah" da Mamaki Jakadiya Ta Kalleshi Tace "Ranka Ya Dade Lapia?? Ban saba ganinka Cikin Wannan Halin bah" Mikewa Yayi Zaune yana wani lullumshe ido Yace "I Said get out!" alajabi ya hana jakadiya koh motsi. Tunda Take Bata Taba ganin Yarima cikin maye bah Sai Yau, Mikewa Yayi yana tangani Yace "keh wacce irin Tabbace, Fitar min daga Daaaki dallah. Kinbi kin ishhheni da Warrri" ta fita Dasauri ta Nufi fada harda dan gudunta... Tsugunawa Tai Ta gaida mai Martaba Sannan Tace "Ranka Ya dade bansan Yanda Zaka dau Maganan nan bah Anma...waziri Yayi saurin Katseta da Cewa "Meya faru Jakadiya??" kuka ta Fashe dashi Tace "Yarima Ya jefa kanshi cikin hali irin na Yaran Zamani, Naje dubashi naganshi Cikin Maye yanata Sambatu" Mai martaba Yace "Jakadiya Kin Tabbatar da Abinda kike fada" ta Share kwallan idonta tace "kwarai Ranka Ya dade" Dogarawan Dake Wajan Mai Martaba Ya Kalla Yace "Kuje ku tahomin da Yarima" suka Amsa suka fita dasauri. Sunsha wuya kamin su daukoshi sai sambatu yake, Parveen ta Fito zata Shiga Garden taga an daukoshi Sai Sambatu da Buge buge Yake kamar Mahaukaci, Tai Murmushi Kawai suka hada ido da Altine. Garden din suka shiga Saida Tasamu wuri ta xauna sannan Ta fashe da dariya Harda Kwanciya, Saida Tai Mai Isarta sannan tajawo Wayanta ta Shiga Instagram Tanata Liking post din wayanda Take following cikeda nishadi... Jakadiya dasauri ta qarasa Sashen Fulani tasanar da ita abinda ke faruwa. Hankali Tashe Itada Umma Sukai Fada, Zaune suka Samu Yarima Sai Sambatu Yake, Takaici Ya hana mai Martaba magana, Fulani ta qarasa kusada Yarima ta tsugunna kusadashi tana Girgiza Shi Tace "Yarima meyasa zakai haka, meh Yasa ka jefa kanka cikin wannan Halin??" kuka take sosai dakyar Umma Tajata Suka bar Wajan... Mai Martaba Ranshi a bace Yacema dogarawa "ku kaishi ku dauremin shi" waziri yace "Ranka ya dade Aimai afuwa, Muna roqamai Sassauci" baice komai bah suka bar wajan riqe da Yarima, Parveen na xaune akazo aka wuce dashi, Dariya tasaki tareda yin kwafa... Yarima baisan inda Kanshi Yake bah Sai washe Gari dasafe, Bude ido Yayi ahankali, Ganin Dakin duhu Yasa ya daga kai dakyar, haske ya hango ta Window, Dasauri ya tashi zaune tareda bin dakin da kallo. Mamakine Qarara a fuskarshi, Mai Yakeyi anan dakin?? Kamarshi yarima Fardeen dan Sarki kabeer ya kwana a Magarqama, Dasauri ya miqe ya fara Ihun kiran bayin dake gadin wajan,

Table of Contents

Chapters

19 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});