Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

A Wani Masarauta Book 2 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Amsa ciki na rawa suka dauketa suka fita. Kan kujera ya Fada Mamaki fal a ranshi, Lallai dan haqin daka raina shike tsole maka ido. Anma yarinyan nan Ta Cuceshi Wallahi Mikewa Yayi ya nufi side din fulani, Duk yanda yake tunani abin ya wuce haka. Dakyar ya Samu ya lallabata ta Haqura.. Washe Gari dasafe ya shirya Cikin Kaya na Alfarma ya nufi fada, Yayi Sa'a mai Martaba na nan, Ya shiga da Sallama Tareda Duqawa, Mutanen Gurin Ya gaida sannan Ya soma bah Mai Martaba Haquri, Bah Irin Magiyan da Yarima beyi bah anma sarki kememe Yaqi saima Cewa Yayi ya tashi yabashi waje. Jiki Sabule Ya mike Tabar Fadan. Yana Qoqarin Komawa Side dinsh Yayi kicibus da Parveen dake qoqarin Shiga mota, Mummunan Kallo ya bita dashi ta Dan Dara Sannan Ta shiga mota Drivern yabar Gidan a Guje... Bilal dayaga duk abinda ya Faru Ya Karaso inda Yarima ke Tsaye "Wai meye Tsakaninka da Yarinyan nan??, Naga Tana Kallanka tana Dariya" Wani qayatacen Murmushi Yarima Ya Saki Tareda Shafa Suman kamshi "Bah Komai" Cikin Isa Ya fara taku hannunshi daya cikin Aljihunshi Ya Qarasa Side dinshi. Bedroom dinshi ya nufa Ya chanza kayan jikinshi Ya Fito Yana Kallan bilal "Tashi Ka Rakani muje naga wajanda mai Martaba yace Ana Ginawa" Kallan Mamaki Bilal Yamai "Yau kuma??" Bansan iskanci idan Zaka Rakani kazo ka Rakani. Bah musu Ya mike Suka Bar Falon.. Yauma Kamar Rannan, Chan bayan Gidan Mai Martaba Sukaje Shida Parveen, Hira Suke Sosai Cikeda Nishadi. Labararaku kala kala Yake bata Tanata Dariya Harda Kyakyatawa. Mai Martaba najin dadin Zama Tareda Parveen Saboda yarinyace Mai Saurin Shiga Rai, Mai Hankali da natsuwa. Shigowan Yarima Knan daga Yawonshi, Fada Ya nufa koh Allah zaisa Yau Mai martaba ya haqura, Dogaran dake wajan suka sanar dashi yana chan bakin ruwa.. Chan ya nufa wit full confidence, tun daga nes ya hango waja zaune duk daukanshi Fulani ce, Ya qarasa wajan da Sallama, Mai Martaba ya daga kai ya kalleshi, Ganin Parveen a wajan Yasa ya tsuke fuska yaji dama baizo bah, gefen qafan mai martaba ya zauna ya gaidashi, Amsawa yayi a takaice, yarima yadan sunnan dakai Ya fara rokan mai martaba, Parveen koh wayanta ta zaro tahau chatn. Mai martaba rai bace Ya kalleshi "Tashi kabarmin nan" Magiya yahau yi, Dakamai tsawa yayi dole ya mike yabar wajan jiki a sabule Parveen neh ta kalli mai martaba cikeda ladabi "Dan Allah Ranka ya dade kamai Afuwa, Idan Har ya sake sai kadau hukuncin da duk ya dace" Dan Murmushi yayi "Shiknan Parveen" Dogarin dake gefensu mai martaba yasa ya kiramai Yarima wanda har yayi nisa ya kusa barin wajan Chan sai gashi ya dawo ya zauna, Mai martaba Ya kalleshi dakyau da kauda kai "Kaci darajan Parveen ta Roka na yafemaka anma idan bah haka bah, bah Yanda za'ai na sauko yanzu" Godiya yama mai martaban Ya mike Suka hada ido da Parveen, Harara ta sakar mishi Yaja guntun Tsaki mara sauti Yabar Wajan Fuuu.. Side din Fulani ya nufa, Baiko sa amai iso bah ya shiga kai Tsaye, Zaune take kan Darduma tana lazimi, ya Qarasa ciki tareda neman wajan zama. Saida ta Gama Sannan Ta kalleshi "lapia?? Meh kuma kakeso??" Furzar da iska yayi rai bace "Fulani I hate dat girl pls ta koma Garinsu, Banasanta! Banasanta!! I hate her!" Dam! Gaban fulani ya fadi, ta dake Tana kallanshi "Saboda meh??" Wai yanzu fisabilillahi fulani inata Rokan mai martaba akan yamin afuwa anma yaqi, wai saida wannan wawiyar Yarinyan tace Sannan" Dan Murmushi fulani tai tana Kallanshi "Duk Abinda ya faru ai kai Kaja, bakaji masu iya magana nacewa wani lokaci da dan uwa gwara bare bah. Ai duk abinda kagani yanxu kai ka saya da kudinka. Sannan kasha kurumin kah indai Parveen ceh nanda kwana biyu zata bar gidan, Zata Koma garinsu" Mikewa Yayi yace "Dayafi Mata" Barin dakin Yayi yadau waya ya kira Mahdi, Bugu daya ya dauka, Yarima yadanyi jim har saida Yace "Yarima kanajina" "Kazo gida inasan Ganinka Pls" Tho Mahdi Yace tareda kashe wajan. Ba'adau lokaci mai tsawo bah saiga shi. Direct Side din ya nufa, Falon ya shiga ya tarar da Yarima zaune yayi crossing leg sai jijiga nasaman yake. Mahdi ysamu guri ya zauna, Shiru ne ya ratsa Falon, Chan Yarima Ya dago Tana Kallanshi "I Hope kasan Wata yarinya yar Gidan Sarki Khaleed na Kasar Zaria koh" Shiru Mahdi yayi nadan sakanni Sannan Ya dago "Yes! Gimbiya Parveen koh??. Wata Kyakyawa, Kamar Rannan danazo gidan nan naganta. Kai Babyn ta hadu bah karya kaga m.... Saurin Katseshi Yarima yayi da Tsawa. "Shut Up dallah" Labarin Zuwanta yahau bah Mahdi har zuwa sanda Tamai Abin nan Mamaki qarara a fuskan Mahdi.. "Ka Tsaya Kana Kallona kaman tv, Mafita nake nema, jibi zata tafi, Inaso nai mata wani abu wanda harta mutu bazata mantani bah Dan dariya Mahdi yayi yace "Indai wannan neh tazo gidan sauqi" Muje zuwa.. Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page1⃣0⃣ Labarin Zuwanta Yahau bah mahdi har zuwa sanda Tamai Abin nan Mamaki Qarara a Fuskan Mahdi... "Ka Tsaya Kana Kallona Kaman Tv, Mafita nake nema. Jibi zata tafi, Inaso nai mata Wani Abu wanda Harta mutu bazata Mantani bah Dan Dariya Mahdi yayi yace "Indai wannan neh tazo gidan sauqi" Da Mamaki Yarima ya Kalleshi "Kamar Yha Meh kake nufi??" Dan murmusawa Mahdi yayi Sannan Ya kalleshi "Haba Yarima Sai kace baka waye bah??. Har kamar yarinyan nan zataima Wannan Rashin Mutumcin ka Kasa daukan mataki?" Tsaki Yarima Yaja "Kawai ka fadamin meh za'ayi Ynxu" Qara murmushi Yayi "A Nawa tunanin Kawai ka Aureta, Ka Maida Ita Sex Machine dnka Kawai Sannan a Gefe Kaita Gana mata Azaba. Kaga dai bah Halin... Saurin Katseshi Yarima Yayi ta hanyar Dagamai Hannu Kaifa Banza neh Mahdi, Kai Kanka Kasan Banida Ra'ayin Aure Ynzu. Idan ma Inadash bah Wannan Stupid Gurl din bah, Naushin Hannun kujeran dayake kai Yayi "I Hateeee Her Wallahi" Mahdi yadan dara Sannan Yace "A nawa Tunanin Wannan neh kawai mafita, Buh ka tsaya kai tunani Akai. Kaga Idan kai Kama daina Neman Matan nan dakake" Yarima baice komai bah, Yadan Zame daga Zaunen dayake Tareda Lumshe ido Mahdi Ya Mike tareda Farin " Ni Natafi, Inada Uzuri Yanzu" Kai Kawai Yarima Ya gyada mai Ya Fita... Yini Yayi yana Saqawa da kwancewa, Anya Zai iya Auren Parveen?? Lokaci Lokaci Yakanja Tsaki "Ni Ban Shirya Aure bah, Am just 26 fah" Idan kuma Ya tuna da Dalilin auren saiyaji Zuciyarsh Ta aminta da Hakan. Haka Ya Cinye kwanaki Biyun nan Cikin Tunanin Mafita.. Fulani da Mai Martaba Sun Wayi Gari Yau ransu bah Dadi, Kasancewar Parveen zata Koma, Ita Kanta Sai Taji Batasan komawan. Anma bah yanda Zatai saboda Makaranta. Altine che Ta shirya mata Kayanta Tareda Sawa amota, sun Fito don Tafiya, mai Martaba Harda Fulani suka Fito don rakasu, Kallan Fulani tai Wanda duk Ranta bah dadi, Ta juya Ta kalli Mai Martaba, Kawai Saita Fashe da Kuka... Fulani ta Qarasa ta Rungumeta Tana Lallashinta, Magana take Mata a kunni wanda ni kaina bansan meh take ceh mata bah, Saidai naga Ta daina kukan tana dan Murmushi, Fulani ta Share Mata Hawaye Sannan Suka Dunguma

Table of Contents

Chapters

19 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});