Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

A Wani Masarauta Book 2 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Juya ya nufi Gidan Amarya... Parveen Taci Kuka Ta Qoshi, Ganin Kukan bazai Pisheta bah Yasa Ta mike Ta Shiga Toilet, Wanka Tai Ta Dauro Alwala ta Gabatar da Sallan Magriba da Isha Sannan Ta Sauya Kayanta Zuwa na Barci Ta Kwanta. Barci ne Yayi Qaura a idonta, Tunani ta Soma Yi Kala kala, Yanzu ya zamansu Zai Kasance Da Yarima?? Tsaki Taja A Fili Tace "Saidai Wallahi Mu Goga, Bazan Zauna Ka Raina min Hankali Bah" Murmushi Tai Ta Gyara Kwanciya A Hankali Barci mai nauyi ya dauketa Cikeda Mafarkai Kala Kala... Koda Yarima Ya Shigo Side din Parveen Ta Dade dayin Barci. Dakuna Yagani Guda Biyu, Shiru Yayi Yana Tunani, Chan Ya bude na Hannun Damanshi Ya Shiga, Hadadden dakine, Wanda Yafi Wanda ya Baro, komai Akwai a Dakin, A Hankali ya Qarasa Ciki, Turarukanshi Da Lotions dinshi Ya hango Kan Mirrow Din Dakin. Riqe Kugu Yayi "So Nan Fulani Tasa a Kawomin Kayana, Umm Not Bad!" Toilet Ya nufa Ya Watsa Ruwa Ya Fito Daure da Towel, Wayanshi Ya dauka Ya Soma neman Wani Layi, Yana Fara Ringing Aka dauka, Banji meh akace achan Bangaren bah. Dan Murmushi Yayi Yace "Am Waiting For You" Sannan Ya Kashe Kiran, Baifi Awa Daya da Wani abu bah Akai Knocking Kofa, Dsauri Yarima Ya mike Ya Fita Ya bude, wata Kyakyawar Yarinya Ce Fara Ta Shigo Ta Rungumeshi Tana Dariya. Shima Dariyan Yayi Tace "Ka Manta Dani Prince, Ai naji kayi Aure" Gefen Fuskanta Ya Shafa Yana Kallan Kwayan idonta "I Dnt Hv time For All dis Conversations, Am in need" Daukanta Yayi Chak Tana Dariya ya Nufi Dakinshi da Ita.. Kiran Sallah neh Ya Tashi Parveen, Addua tai Ta Mike Ta zauna Sannan Ta mike Ta Nufi Toilet, Wanka Tai Ta dauro Alwala Ta Dawo Dakin, Kayan Jikinta ta Sauya Tasa Hijabi Ta Shimfida Sallaya Ta Tada Sallah, Tana Idarwa Tai Adduointa. Shiru Ta zauna Jugum Tana Tunani. Chan Ta Mike Tuna Jiya Deeza Ta bude kit taga Qur'ani, Budewa Tai Ta dauko Qur'anin Ta dawo Kan Sallayan Ta Zauna, Suratul Maryam Ta bude Ta Shiga Karantawa a Hankali Cikin zazzaqan Muryanta, bata Tashi bah Saida Taga Garin yayi Haske a Hankali Tace "Sadaqallahul Azim" Ta Rufe Qur'anin Ta maida Cikin Kit din... Knocking Aka soma Yi a Qofan Falo, Ta Fita Ta Bude, Kuyangi neh dauke da Kulolin abinci kala kala, hanya ta basu suka wuce, kan dinning Suka Aje Sannan Suka Zube dan Kwasan Gaisuwa, amsawa tai suka fita. Shafa Cikinta Tai ta yamutse Fuska, Waige Waige Ta Soma Yi, wani qofa Ta Hango Ta qarasa ta bude a Hankali. Kitchen Ta gani, komai na Buqata Akwai a Ciki, Sosai Kitchen din ya burgeta. Dube dube ta Soma Yi, chan Ta Hango Wani set din plates, kwalin ta bude ta dauko daya ta Wanke, da Dauki chokali Shima Ta Wanke Ta Fito. Tana Zama Kan Dinning din Taji An Bude wani qofa daga Gefenta, Kai Ta daga Cikeda Tsoro... Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page1⃣8⃣ Tana Zama kan Dinning din Taji An Bude Wani qofa Daga Gefenta, Kai Ta Daga Cikeda Tsoro dan A Tunaninta ita kadaice Ta kwana a gidan. Wata Kyakyawar Yarinya ta gani Ta Fito Sanye da Wani Matsatsen Wando da Riga, Kafanta Sanye da Dogon Takalmi, Kan nan Yasha Attachment. Ko inda Parveen Take Bata Kalla Bah Tai Hanyar Kofan Falon, Juyawa Parveen Tai Cikeda Mamaki, daidai Nan Yarima ya fito Sanye da Brown Jallabiya, Bai ko Kalli Parveen Bah Ya Riqema Yarinyan Hannu suka Fita Daga Falon.. Mamaki neh Kwance Kan Fuskan Parveen, Tunani ta Soma, dama Yarima Na neman mata meh?? Wata zuciyar Tace "Ina Ruwanki da neman Matanshi" Tsaki Taja Ta Soma Zuba abincinta, saida Taci Ta qoshi Sannan Tadauke Plate din Takai Kicin Ta koma Daki. Wanka Ta sake Ta Shirya Cikin Pink and Purple Atamfa, Simple Make up tayi tasa Mayafi Pink, Tadau Flat Shoe Shima Pink Tasa. Wayanta ta Dauka Ta Fito Falo, Tana Qofarin Bude qofan Falon Aka Bude. Yarima Neh, Yana Ganinta Ya Hade rai, Itama hade Ran Tai TaKauda kai, ta gefenta Yabi Ya Wuce ya Shige Dakinsa. Tsaki tai Ta Fita Ta nufi Side din Fulani.. Fulani na Ganinta ta Tareta da Murna, Har Kasa Ta Tsugunna Ta Gaida Fulani, Ta Amsa Fuska A Sake Tana Fara'a. Parveen Tsintan Kanta Tai da Jin Kunyan Fulani, Lura da Hakan Yasa Fulani Tace "Amarya kinsha Kanshi" Sadda kai Parveen tai tana dan Dariya "Bai Kamata Ki Fara Fita Tun Yanzu bah, ki Bari idan kikai Sati daya Saiki Fita. Sannan Maganan Makaranta Mun Gama Magana Da Mai Martaba nan da Sati Biyu saiki Fara" Dagowa Parveen Tai Fara'a Kwance Akan Fuskanta "Nagode Allah Ya Qara Girma" Fulani ta Amsa da Ameen Mikewa Parveen tai tace "Na Barki Lapia" Fulani Cikeda Sigan Wasa tace "A Gaidamin da Ango" Murmushi Parveen Tai Tabar Dakin.. Koda Ta koma Yanda Tabar Abincin Haka Tadawo tasameshi, Tsaki Tai ta Kwashe Kwanukan Takai Kicin. Daki ta Koma Tai Kwanciyarta Tareda Jawo Wayanta, Numbern Umma Ta kira, Yana Fara Ringing ta dauka. Ajiyan Zuciya Parveen Tai Sannan Tace "Barka da Safiya Umma" Umma Cikeda Murna Tace "Parveen kin Tashi Lapia? Ya Kwanan Ango?" Jim Parveen Tai Sannan Tace "Yana Lapia lau" Tho Madallah "Umma Ya Mai Martaba??" "Yana Lapia Lau, Dazu koh muka Gama Maganan ki" Murmushi Tai "Ina Gaidashi" Insha Allahu Zaiji..Kashe Wayan Umma Tai, Parveeb Tabi wayan da Kallo. Tayi Missing din Ummanta, Nan da Nan Hawaye Suka Fara zuba A Idonta... Kwanciya Tai Ta Lumshe Idonta, A Haka Barci Ya dauketa Cikeda Kewan Gida.. Haka Suka dau Tsawan Sati, Kullum Sai yarima Ya kawo Yanmatan shi. Sam Parveen Hakan Bai Damunta, Tunda Tazo gidan Magana bai Taba Hadasu dashi bah. Ita Hakan mah Yafi mata.. Ranar da Takai Sati Daya Fulani ta Umarceta data Fara Girki..Da Yanma Ta Daura Tuwon Shinkafa Miyan Ugu, Kasancewar Komai Na Dangane da Kayan Miya Akwai a Cikin Kicin din.. Nan da Nan gidan ya Gauraye da Kamshi, Saida Ta Gama Komai Ta zuba a flask Ta Kawo Dinning, Mai Martaba ta Zubamawa a Wasu Hadaddun Kuloli. Baiwar dake Taimaka Mata da Goge Goge Taba Takai Ita kuma Ta Koma Dakinta dan Watsa Ruwa... Watsa Ruwa Tai Ta Fito Daure da Towel a Kirjinta, Sai Qarami datake Tsane Ruwan Kanta, zama Tai kan Stool din Mirrow Tana Cigaba da tsane Kan nata. Saida Ta Gama ta dago ta Kalli kanta a Mirrown, Ganin Mutum kawai tai Kan gado Yana Kallanta, Dasauri ta mike Tareda Kwalla ihu. Saura Kadan Towel dinda ke Kirjinta ya Fadi, Sam batama Lura da Waye bah Tabar dakin a Guje. Baiwarta Atika Taci Karo da Ita, atika ta Kalleta Hankali Tashe "Lapia Ranki Ya dade Maiya Faru??" Dakinta Ta Fara nunama Atika a Rude Har atika ta Nufi dakin Taga Yarima Ya Fito Hannunshi daya Cikin Aljihunshi, Fuskan nan Daure Tamau. Barin wajan Atika tai Kanta a Qasa Kamar munafuka... Sai a Sannan Parveen Tasan Yarima Neh, Dogon Tsaki Taja Tareda Kauda kai Gefe. Dariya yarima Yaso yi anma Ya Dake, Shima Tsakin Yayi yabar Falon Zuwa Dakinshi "Anma Allah ya Isa, Mutum Yayita Abu kamar bah musulmi bah" Dakinta ta koma Ta Shirya

Table of Contents

Chapters

19 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});