Chapter 9
Chapter 9
sai wani farin hayaki yai fitar burgu daga cikin wasikar da ganin haka sai dan aiken daya kawo wasikan ya bace bat, ba afi minti daya ba sai gaba dayan fadan yadauka da dariya bakajin komai sai sautin dariyar sai da akayi dariyar sosai sannan wata kakkausar murya tafara magana "yakai wannan sarki kai sani cewa nine sarki Rava na birnin BULZUM musabbabin isowata wannan birni naka shine na nema wa Dana bishmalu auren zukekiyar yar nan taaka, bijirewa umarnina zai janyo da mugun tashin hankali ga Al'ummanka, don haka ina umartarka da ka gaggawar fitowa da ita don na kaita ga dana" . Hankalin mahaifina ya tashi , ya dugunzuma cikin muryan fada "kai kana ganin wanene kai da har zaka zo har birnina kuma cikin fadata sannan ka dau yata ,toh kai sani cewa mu ga Allah muka dogara, babu abunda ka isa kai mana ," Muryan ya bushee da dariya "dama an sanar dani cewa kana da girman kai, kuma sam ba zakai mani biyayya a bisa kudirina ba, kuma tun fil azal dama ina da muradin na murkushe wannan birni naka da dukkan wasu aljanun da suke ciki Amma bokana ya haneni ga aikata hakan Toh yau kai sani sai Rabin mutanen wannan birni sun ziyarci lahira,ziyarar da baza su taba dawo wa ba" . Kamar daukewan ruwan sama sai muryan ta dauke dif tamkar bata taba wanzuwa ba, Mahaifina yaa koma kan karagarsa ya zauna yai tagumi yana tunani Bayan dakika dari da hamsin sai ga wani badakare ya sukwano a guje akan dokinsa Badakaren bai tsaya a ko'ina ba sai gaban sarki gaba daya jikinsa ya baci da jini, kallo daya zaka mai kasancewa a firgice yake Wani dogari ya daka masa tsawa "kai meyafaru ne muka ganka haka, shin ina sauran abokan aikinka masu tsaron gari" "Wata muguwar masiface ta afku a cikin gari ranka shi dade , rayuka da yawa sun hallaka gidaje da dama sun ruguje, kana nun yara,mata,samari da tsofaffi dukkansu sun rasa rayukansu" Badakaren ya fada ayayin da yake numfarfashi Sarki ya mike tsaye cikin firgita da dimaucewa ya ce "menene ya faru da su" "Muna aikin bada tsaro a cikin babban kasuwa , mutane sai cinikaiya suke , yara,maza,mata,tsofaffi suna ta zirga zirga cikin yanayin nishadi Kwatsam sai mukaji wata kara daga karkashin kasa hakan yasa mutane sukai saurin barin wajen da karar yake fitowa mu kuma muka durfafi wajen cikin shiri, Kasan wajenne ya tsage tamkar an saka wukane aka tsargeta, wani mummunan halitta ne ya fito daga cikin kasan halittan babbane don kuwa tsayinsa yafi na gidajenmu sau goma, halittan yana da kaho guda akan goshinsa sai ido daya rankwalele daya ke gefen hancinsa Hannunsa na rike da wata katuwar Al'amudi wacce inda mutum dari zasu taru baza su iya rabata da kasa ba, Ai nan take sai wannan halitta ya hau ruguza gida jen mu duk abunda ya duka da al'amudin dake hannunsa sai de kaga ya ruguje hakan yasa muka cire tsoro muka far masa muka runga sara da sukan sassan jikinsa, Sam ko yasan munayi, cikin kankanin lokaci ya gama rushe rabin godajen birnin nan sannan ya hau Aljanu , duk aljanin daya taba da Al'amudin hannunsa sai kaga ya zama toka mun tsorata ainun da lamarin wannan halitta, gaba dayan Askar din daka hadani da su sun halaka ni kadai ne kawai na tsira" Askar din ya karasa maganarsa yana aman jini Hankalin mahaifina ya tashi ainun Hakan yasa sukai sauri suka garzaya cikin gari domin ganin barnan da halittan tayi, . Abun da suka gani ya basu tausayi sosai Gidaje sama da Dubu sun rushe, Aljanu sama da dubu sun halaka, sama da dari biyar sun ji munanan Raunuka, kowa sai neman taimako yake Anan take mahaifina ya fashe da kuka ,yana cikin kukan ne akaji wata kakkausar murya ta bushe da dariya sai tai mai isarta sa'annan tai shiru askarawa da yan majalisu sai waige waige suke ko zasu ga ta wajen da muryan ke futa, Muryan ta cigaba da fadin "ayanzu ina amfanin Gardama, Ayanzu ina Amfanin girman kai, da a ce ka yarje da bukatata da duk wannan abu bai faru ba, na rantse da karfin mulkina muddin ka ce baza ka aurawa dana yarka ba, toh nan da shekara mai zuwa sai irin wannan bala'I ta kara samunku, kuma kai sani cewa na gaba ba gidaje da jama'a kadai zai kashe ba 'a'a gaba dayan birnin ne zai Kone ta ta koma Toka, Gargadi na karshe da zan maka, ka daukesa a matsayin Doka ko umarni duk wani Talikin daya sake Kiran HASEENA da sunanta sai de wani ba shiba , da ga yau saide ku runga kiranta da BUDURWAN SIRRI, don kuwa ita ta kasance mai matukar rabo da sa'a da har zata auri dana,na baka nan da shekara daya muddin baka aiko da yarka zuwa marautata ba toh duk abunda ya faru daku, kui kuka da kanku" Muryan na gama fadin hakan sai ta dauke dif tamkar an zabga ruwan sama an dauke . Gaba dayan yan majalisan suka hau mahaifina suka suna cewa akan mace daya jal, an rasa dubban rayuka anyi asaran Arziki mai yawa mai zaisa ba za a bashi ita ba ko dan a kare bala'in da ke tunkararmu, shi de mahaifina shiru yayi yaki tanka masu . Yana dawowa gida ya shige turakarsa babu wanda yasan me yake a cikin turakansa din, Washe gari da sassafe na nufi turakar mahaifina ko kwankwasa kofan ban yi ba nasa kai, Na sameshi a zaune bisa kan sallaya alaman ya iddar da sallah kenan , Koda mahaifina ya ganni sai na ga kwalla suna gangarowa akan kuncinsa nai sauri naje na runugmesa ina mai fashewa da matsanancin kuka , Cikin shishshikan kuka nace "Abba ni na yarda na amince zan auri bishimalu , muddin hakan zai tsaida wannan masifa data ke tunkaromu, nasan cewa in na auri bishmalu Al'umma dayawa zasu tsira da rayukansu, da dukiyoyinsu" "A'a yata kada kiyi saurin yanke hukunci, shi rayuwa da mutuwa dukka Allah ne yake yankesu, ki tashi yanzu kije ki kwanta, ayau dinnan zanyi istahara naga abunda Allah ya zaba mana" Mahaifina ya fada cikin dakewa , Sum sum na tashi na fice daga turakar naje dakina na kwanta ************ Shin kuna biye dani kuwa fans , Alkalamin Shuraih Usman ne inkiya 99% BUDURWAN SIRRI Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 9 . Washe gari da safiya naje na iske mahaifina a turakarsa domin jin abunda ya samu daga istaharan da yayi , Da sallamata na shiga cikin turakar na sameshi a zaune a wajen dana iskeshi jiya, Ya dago kai daga kallon kasa dayakeyi yana mai amsa sallamata, Na samu waje na zauna, Mahaifina yayi gyaran murya sannan ya fara bayani "haseena hakika Allah ba azzalumin bawansa bane, Jiya nayi istahara domin neman zabin Allah akan wannan mugun al'amari dayake tunkaro mu, An nuna mani a mafarkina cewa wani Dan Adam ne kadai zai iya tseratar da mu daga sharrin sarki Rava, dolenmu muje duniyar mutane mu dauko wani yaro wanda bansan sunansa ba, sannan zamu dukufa wajen sana'anta wata makami wacce ba'ataba yin irinta ba a doron kasa, da taimakon wannan makami ne
Table of Contents