Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Budurwar Sirri Book 1 Complete Hausa Novel 1,170 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

jikinsa suna dan kara sakamakon yadda yake tafiyar din . Ya kariso wajen da muke zaune Neman waje yayi ya zauna sannan ya harde kafafuwa irin zaman da yayi sai ya tuna mani da lokacin da nake makarantan Allo, fuska cikin fuska ya dubeni sannan ya takarkare da mahaukacin dariya mai matukar amo, ba shiri na sanya yan yatsuna na toshe kunnuwana sakamakon yadda naji dodon kunena na neman agaji . Sai da yayi dariya mai isarsa sannan ya dubi haseena yace "Budurwan sirri, wai dama wannan dan tsakon ki ka je kika samo, ai nayi mai girma ina laifin ki samo dai dani, " Ya nuna ni da yatsa batare daya kalleni ba sannan yacigab da magana da muryansa mai kama dana jaki "Ina mai tabbatar maki da cewa nine zan aureki ,kuma nine nan zan lashe wannan gasa wacce zamu kara wata mai zuwa ni da wannan dan kwaron " . Duk da cewa ina jin tsoron wannan basamuden aljani wanda bansan sunansa ba , ai koda naji irin kalaman dayake furtawa ga haseena sai na fahimci cewa shine SALMAN, nan take na nemi tsoron dana ke mai na rasa cikin kunan rai na daka masa tsawa "Kai Aljan mutun bisa kanka, girman jiki bashi bane ke nuna cewa mutun yana da karfi, to kayi sani nidin dai daka raina da yardar Allah sai na baka mamaki" ai sai dana gama furta maganar sannan nayi nadamar furtawa Domin kuwa alokacin fuskar aljani salman ta yamutse , yadda kasan an aiko masa da sakon mutuwa, . Badon ina da dauriya ba da babu abunda zai hana ban tsiyayo fitsari ba kasancewar irin kallon danaga yana yimin Cikin kunan zuciya ya daga girjejen hannunsa mai kama da tabarya da nufin ya zabga min mari, rufe idanuwa na nayi don kuwa nasan babu makawa zai aikata, ko kadan banyi kokarin kare kaina ba ta hanyar rufe fuskata don nasan muddin hannunsa ya taba jikina to take zan baje a kasa sumamme ko matacce . Cikin sauri haseena ta daka masa tsawa wanda ya sanya shi tsayawa cak tace "salman izan ba kana son kaaga fushina bane toh ka gaggauta barin wajennan , in kuwa ba haka toh zakayi daana sani wanda ba zai maka Amafani ba, " cike nake da tsoro kamar ace kyat na ruga na dubeshi a yayin da ya dunqule hannunsa ya naushi kasa , a hassale ya tashi sa'annan a dubeni yace "ka shirya nan da wata daya bil'adama maza bisa kanka," yana gama fadin hakan sai naga manyan fuka fukai guda biyu sun fito daga bayansa cikin kankanin lokaci ya tashi sama ya luluka cikin gajimare Na dawo da dubana ga haseena tambayoyi fal bakina . Murmushi tai min wanda shine ya mantar da ni dukkan wannan tambayoyi dana ke shirin jera mata su Tace "nasan ka tsorata da Al'amarin Salman amma karkadamu akwai wanda zan kaika wajensa ya koyar dakai fada da kuma yaki" . "Toh" kawai bakina ya samu fadi a yayin da muka cigaba da hirarmu in ka ganmu sai ka rantse mun yi shekaru da ita, na saki jiki sai zuba zance nake ****** . Washe gari tunda sassafe wayannan yan mata uku suka sake zuwa kirana sai de yau dukkansu sun canja kayan dake jikunsu irin kayan dana sanya jiya shi na sake sakawa duk da ban san wanda yake kawo mani kayan ba hakan bai hanani sakawa ba . Wannan karon ba yalwataccen lambunnan muka nufa ba wani bangare ne daban wanda kallo daya naiwa bangaren nagane cewa mutane ba su cika shiga wajen ba duba da yadda naga wajen yayi kura, kuma yanan gizo gizo duk ya gauraye rufin wajen, . Muka iso bakin wata kofa mai kauri wacce aka sana'antata da zallan bakin karfe daya daga cikin matannan ce ta ciro wata tsohuwar kubba daga jikinta ta zura a cikin dan siririn ramin dake jikin kofan sannan ta murda Dan karamin dakine mai dauke da kayan tarkace iri iri , a karshen bangon dakin muka hango ta naayi mamaki kwarai da ganinta anan . Na kariso ni kadai a yayin da yan mata ukunnan suka tsaya a bakin kofan dakin rufe kofar dakin sukai Na budi baki zanyi magana haseena ta dora yatsanta a kan lebbana alamar nayi shiru ta nufi wani kusurwan dakin daban wata tsohuwar tayan keken doki naga ta daga, ta kama wani katako ta murda shi . Nan take jiri ya fara dibana sakamakon yadda naga dakin yana juyawa da sauri haseena ta ruko hannuna sannan itama ta rike wani karfe , kafin kace kwabo sai dakin ya runga juyawa dukkan tarkacen nan suka fara tashi sama suna haduwa da junansu, baki kawai na saki ina kallon ikon rabbi, sai da gaba dayan tarkacennan suka gama hadewa waje guda suka dunkule kaman dunkulin magi . Sai da suka gama dulkulewa tukunna sai kuma dunkulin ya fara fitarda yar karamar kofa, kan kace kwabo har wannan dunkulin ya canja siffa izuwa na Kofa, Babu abunda zai baka mamaki ma kaman yadda kofan ta kasance sai haske take tana daukan idanu . Adai dai lokacinne dakin ya daina juyawa komai ya tsaya cak sai a sannan haseena ta ce "wannan shine babul hajir, ta cikin wannan kofa zaka iya tafiya ko ina a doron kasa, tun daga kan duniyarku har zuwa wasu duniyoyinma," . Shiru kawai nayi na saki baki ina kallonta ni yanzu ma har na saba da abubuwan mamakinsu koda na gani ma banayin mamaki sosai kamar yadda nake a baya . Ta ja hannuna wanda hakan yasa nima nabi bayanta bakin kofan muka zo muka tsaya ta sanya lallausan hannunta ta bude kofan sai a sannan dukkan wani mamakina ya karu domin kuwa babu komai a gaban kofan banda hazo daya ke gittawa lokaci lokaci, banga alaman wani abun ba . Haseena ta jani muka shiga cikin kofan ai sai dukkanmu muka ji kamar mun fado daga saman wani katon tsauni ne, saboda tsaban firgici kulle idanuwana nayi yayin da muke fadawa kasa iska sai gittani yake ta ko ina hakan yasa na saki wata kara . Kamar daukewan wutan nepa sai mukaji mun fado a cikin wani rami, abun da ya kara dauremin kai shine da kafafuwanmu muka fado kuma ko dan zogi banji kafata tayi min ba . Haseena tai murmushi "tace haka ka iya ihu dama ban sani ba, ai kuwa sai ka tanadi wani ihun da yafi wanda kayi a baya, domin kuwa yanzu ne za'afara ainahin tafiya" cikin sigar zolaya ta fada Na sosa keyana "ai ni kaina ban san lokacin da na saki ihun b....." Wani kara ne ya katse mani maganata karan kuma daga kasan inda muke yake fitowa sai a sannan na daga kaina na kalli sama Gani nai tamkar mun fada cikin rijiya gaba dubu ne Ban gama wannan tunanin ba kasan wajen ya wawake take muka fada ciki amma wannan karon a tsaye muka fada kuma ahankali muke sauka kasa, Cikin wani daji mai yawan guntayen bishiyu muka sauka , sosai yanayin dajin ya burgeni dukkan wasu ganye na dajin jane maimakon kore mun danyi gajeriyar tafiya da kafafunmu sannan muka riski wani Bukka irin na mutanen da shi kansa bukkan da jajayen

Table of Contents

Chapters

15 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});