Chapter 4
Chapter 4
Gaba daya mutanen wannan birni namu sona matukar tsoronshi da shakkar shi, saboda duk birnin nan babu wanda yakai shi jarumta , wannan nema yasa da yawa daga cikin masu neman aurena suka janye sakamakon tsoron salman da sukeyi . a Al'adar wannan kasa tamu itace duk wayanda suka hada neman wani abu tare da wani, ko suke neman mace tare toh akwai wata gasa da zasuyi wanda duk wanda ya cinye wannan gasa toh shine yayi nasarar mallakar wannan abu da suke rigima akai wannan gasa muna kiranshi da GASAR FIDDA GWANI" . Haseena tayi mani murmushi Wanda ke sanyaya min zuciyata, taci gaba "Toh Masoyi kaji tarihin birnin namu mai matukkar Al'ajabi," Wani shauki naji ya dirga min a zuciya sakamakon yadda naji sunan da haseena ta kirani da shi, ta matso kusa dani ta kama hannuna , ai bansan lokacin dana kurma wani dan karamin ihu ba sakamakon wani shocking dana ji ya ziyarci hannuna,murmushi kawai haseena tayi sannan ta dago ni, abun ya bani mamaki domin kuwa yadda ta daga ni sai kace ba katon gardi ta daga, yadda kasan fallen takarda, har naso na tambayeta game da hakan amma sai nayi shiru da bakina, muka fice daga cikin dakin atare . Tafiya muke a jere yayinda hannuna yake cikin nata fuskarta kuwa yana kan fuskana ko gabanta bata kallo sosai, wani zunzurutun wutar kaunarta ne yake ci a zuciyata, Ban yi aune ba sai gani nayi mun iso wani kayataccen fada wanda aka kawata da kayan ado irinsu, zinare,zubarjadi,lu'u lu'u da yakutu domin kuwa daben wajen ma da yakutu akayi shi, Ga bayi da hadimai sai zirga zirga suke tayi amma da zarar sun ganmu sai su russuna su kwashi gaisuwa sa'annan su wuce, Mun danyi tafiya mai dan nisa kafin mu iso bakin wata kofa wacce aka sana'antata da zallar farin zinare sannan akai mata ado da lu'u lu'u sai dai wani abun daya daure mani kai da kofar shine ganin wasu macizai danayi guda biyu nan na de da juna a jikin kofan, . Cikin mamaki naga haseena takai hannu jikin kofan ta kama macizan nan duka ta murde musu kayika, sai gashi kofan ta bude, nan muka shiga ciki har hanzu hannuna na cikin na haseena, dakin da muka shiga ya fi kowanne daki kayatuwa a cikin fadan don ni dai tun da na shigo banga wajen daya kai nan kayatuwa ba, . Sai a sannan na lura da wasu kirda kirdan mutani sanye da kayan karfe, suna rike da makamai a hannunsu, kallo daya nai masu na gane cewa Dakarune masu tsaron gidan, nakai dubana ga gabanmu inda muka dosa toh a nan ne naga tarin mutane suna zaune bisa wani dogon kujera wanda ya kusan kaini tsayi, . Wayannan kujerun suna jere ne, layi biyu kowanne kujera yana fuskantar daya, mutanen sunyi shiga ta alfarma wanda da gani kasan ba kananan mutane bane, mai karatu kar kaji nace mutane ka dauka ko bil'adama ne wayannan mutanen , a'a dukkansu Aljannune amma a siffar mutane suke rayuwa, sai kuma wayansu fuka fukai dake bayansu, . Wani dattijon aljani na gani kyakkyawa da shi, yana sanye da fararen kaya masu daraja, zaune yake akan wata karaga ta sarauta, wacce aka sana'antata da zallar lu'u lu'u aka kuma yi mata ado da takubba na farin yakutu, a gefen karagar sa wayansu sadaukan samudawan aljanu ne su goma cikin shirin kota, fuskarsu a murtuke tamkar wayanda aka aiko ma sakon mutuwa, ko motsi basa yi sai kace Gumaka kwana kallo daya nai ma samudawan aljanun nan na kau da kai don kuwa muddin na cigaba da kallonsu toh zan iya Sumewa wajen wayannan aljanu muka nufa ni da haseena muna zuwa gabansu haseena ta durkusa sannan ta kalleni tai min Alama dana durkusa ba musu nima na durkusa, kawai sai ji nayi haseena tana magana da wani irin yare wanda ni ban taba jin sa ba, bayan ta gama maganar ne wani daga cikin Aljanun nan yace mar habanki dake da wannan bako, yake gimbiya daga nan sai haseena ta mike tsaye ta karasa gaban wannan dattijon mai fararen kaya ta rungumeshi sannan ta tsaya a gefensa, dattijon aljanin ya dubeni har yanzu ina durkushe ban dago ba, . Yafara magana yakai wannan bako kuma masoyi ga yata kai sani cewa muna marhaban da zuwanka, kuma a sannu zamu sanar da kai dalilin daya sa muka kiraka izuwa wannan duniya tamu amma kafin nan yanzu za mu bari ka huta tukunna, aljanin yana zuwa nan a zancensa sai ya dubi wani wani bafaden aljani yace mai zirwanu ka kaishi masaukinsa dun ya huta nasan ya debo gajiya, wanda aka kira da zirwanu ya russuna angama ranka shi dade, ********** Ina zaune a cikin dakin da zirwanu ya kawo ni , nayi tagumi bana tunanin komai sai na gida, Yanzu a wani hali iyayena suke nasan dole su shiga wani irin hali izan har ya kaasance basu ganni ba, . Nan take naji bana marmarin komai sai gida dun kuwa nima ina so na gansu ko hankalina ya kwanta, sai de ba anan gizo ke sakar ba, aduk lokacin dana tuna cewa ina da zukekiyar budurwa kamar haseena sai inji zanma iya yin shekaru hamsin muddin zan zauna da haseena . Tunane tunane kala kala suna ta zuwanma kwakwalwata, ina cikin wannan hali ne sai na fara jin wata zazzakar waka tana tashi daga bayan dakin danake, cikin zumudi na nufi taga na bude don naga wacce keda wannan zazzakar muryar, Wani kayataccen lambu ne yaiwa idanuna maraba acikin wannan lambu kuwa yan mata ne su ashirin, suna rike da kayan kida sai kidi sukeyi, dukkan matan nan kyawawane na gaban kwatance domin kuwa in ka dauke haseena har yau banga macen da ta kaisu kyawu ba, A tsakiyar wayannan yan mata wata mace ce ta lullube kanta da mayafi zazzakar muryarta ne kawai yake tashi, ...... . . Kuyi hakuri da rashin post nawa akan lokaci rashin wadatuwan lokaci shi ya janyo haka , Ni dinne dai Shuraih Usman Inkiya 99% Daga:- www.facebook.com/hausaebooks BUDURWAN SIRRI Marubuci:- Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 5 . A tsakiyar wayannan yan mata wata mace ce ta lullube kanta da mayafi zazzakar muryarta ne kawai yake tashi, Zuciyata ce ke fisgata irin fisgar da ruwan kashe gobara yakeyi yayin fitowa daga cikin bututun ruwan . Ni kaina ban san lokacin dana je na bude kofar dakina ba da nufin nayo waje naga ko wacece wannan mai wakar, har na saka kafa na fita kuma sai nai wani tunani , Ayanda nake jin ana labarta min cewa nan duniyar aljanu ce , na tashi na nufi wajen wayannan kyawawan matan, kila ma aljanu ne ban sani ba, Wannan tunanin dana yi shi yasa na dawo da baya nai kwanciyata cikin dakina, Dakyar na samu nasarar yin bacci sakamakon wannan zazzakar wakar dake tashi daga waje, aduk lokacin dana runtse idanuwana domin nai bacci sai na wannan zazzakar murya ya farkar dani, Har takai da saida na samu wasu yanki na toshe kunnuwana da su sannan na dena jin wannan waka . Washe gari na farka a gajiye na tashi na nufi dan wani kofa dana gani a cikin dakin
Table of Contents